Ƙasashe shida da ake samun ƙaruwar masu kamuwa da HIV a duniya

    • Marubuci, Swaminathan Natarajan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 3

Duk da samun raguwar kamuwa da cutar HIV, mai karya garkuwar jiki da mace-macen da ake samu sakamakon cutar, hukumar yaƙi da cutar HIV/AIDS ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa duniya ba ta shirya kawar da barazanar cutar ba.

Hukumar UNAIDS ta ce a yanzu haka akwai mutum miliyan 39.9 da ke rayuwa da cutar a faɗin duniya, kuma kusan rabin wannan adadi na yankin kudanci da gabashin Afirka.

Adadin mutane da ke kamuwa da cutar mai karya garkuwar jiki ya ragu ka kashi 39 cikin 100 tun shekarar 2010, kuma mace-macen da ake samu sakamakon cutar ya ragu da rabi.

To sai dai ƙasashen Afghanistan da Masar da Fiji da Philippines da Papua New Guinea da Saudiyya sun bayar da rahoton samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar da fiye da kashi 100 tsakanin 2010 zuwa 2023.

Kenya da Malawi da kuma Zimbabwe tare da Nepal sun samu nasarar rage yawan masu kamuwa da cutar da kashi 75 cikin 100 tun 2010.

A yanzu nahiyar Afirka na kan gaba wajen yaƙi da cutar AIDS.

Wasu ƙasashen 18 sun rage adadin sabbin kamuwa da cutar a shekara-shekara da fiye da kashi 60 cikin 100 tun 2010.

Mafi yawancin na yankin Afirka na Kudu da Hamadar sahara, da suka haɗa da Lesotho da Eswatini da Benin da Ethiopia da Rwanda da Botswana da Eritrea da Liberia da Burkina Faso da Togo da Zambia da Burundi da Guinea-Bissau da kuma Uganda, sannan sai Tajikistan da Portugal da Belarus da kuma Italiya.

Daga cikin masu ɗauke da cutar, kashi 77 cikin 100 na karɓar maganin rage kaifin cutar. A ƙasashen Afirka na yankin Kudu da Hamadar Sahara kashi 82 na masu ɗauke da cutar ne ke karɓar irin wannan maganin.

Haka kuma tsawon rayuwar masu ɗauke da cutar ya ƙaru da shekara biyar, daga 56 a 2010 zuwa 61 a 2023, saboda ci gaban da aka samu wajen yaƙi da cutar.

UNAIDS ta ce girman yaƙi da cutar a ƙasashen Afirka ta bai wa masu ɗauke da cutar HIV damar rage hatsarin yaɗa cutar.

Dokokin da suka haramta auren jinsi da amfani da muggan ƙwayoyi - waɗanda suka zama ruwan dare a wasu ƙasashe - na kare mutane masu rauni daga kamuwa da cutar.

Ci gaba a ƙasashen Afirka na yankin Kudu da hamadar Sahara

"Ci gaban da aka samu wajen yaƙi da cutar, musamman a yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka, ya nuna irin tasirin da haɗi kan da jagoranci da yunƙurin ƙasa da ƙasa za su yi wajen yaki da cutar,'' in ji Christine Stegling, mataimakiyar Babban Darakta na UNAIDS.

Cikin wani saƙon martani da ta aike wa BBC, ta ce akwai buƙatar shugabanni su mayar da hankali wajen bunƙasa hanyoyin samun kariya daga cutar, sannan su kawar da matsalolin da ke hana mutane zuwa cibiyoyin lafiya.

“Duniya na kan hanyar kawar da cutar AIDS a matsayin barazanar lafiya, saboda babbar matsalar ita ce rashin samun damar zuwa cibiyoyin lafiya, musamman al'umomin da aka ware. Kariya daga cutar HIV na ci gaba da zama matsala''.

To sai dai yaƙi da cutar a wasu ƙasashen na tafiyar hawainiya.

Ƙasashen Papua New Guinea da Afghanistan da Fiji da Philippines da Masar da kuma Saudiyya na bayar da rahoton samun ƙaruwar fiye da kashi 100 na masu kamuwa da cutar AIDs tsakanin shekara 2010 zuwa 2023.

Idan aka kwatantan da yawan mutanen ƙasashen, Masu ɗauke da cutar HIV ba su da yawa a ƙasashen Afghanistan da Masar da kuma Saudiyya.

To sai dai akwai kyakkyawan fata. Hasashen UNAIDS ya nuna, idan aka ci gaba da ɗaukar matakan bayar da tallafi da kuɗaɗe, za a iya kawo ƙarshen barazanar cutar HIV a faɗin duniya nan da shekara shida.