Waiwaye: Rasuwar Muhammadu Buhari da ficewar Atiku daga PDP

Buhari

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin shekarar 2025 ce tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rasu yana da shekara 82 da haihuwa.

Mamacin ya rasu ne da misalin ƙarfe 4:30 "bayan fama da jinya".

Buhari ya rasu ne kimamin mako ɗaya bayan an samu rahotanin an kwantar da a wani asibiti a London domin duba lafiyarsa, wanda aka ce asali ya je domin ganin likita kamar yadda ya saba, amma daga baya sai ya kamu da rashin lafiya.

Tuni aka binne marigayin a gidansa da ke Daura a jihar Katsina, lamarin da ya ɗauki hankalin ƴan Najeriya da ma ƙasashen waje.

APC ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Legas

Masu zaɓe sama da miliyan bakwai ne suka kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙananan hukumomi 20 da ƙananan yankunan mulki 37, haɗi da kansuloli a faɗin jihar Lagos, wanda aka yi a ranar Asabar ɗin makon jiya.

An kaɗa ƙuri'a a cibiyoyin zaɓe 13,325 a mazaɓu 376 a jihar da ke zaman babbar cibiyar kasuwancin Najeriya.

Tun da farko, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (Lasiec), ta bayar da tabbacin cewa ta yi shirin da duk ya kamata domin zaɓen, kuma ta ce an inganta hanyoyin zuwa cibiyoyin zaɓen.

Kamar yadda aka gudanar da zaɓukan da aka yi na jihar da kuma na tarayya na bayan-bayan nan za a yi amfani da na'urar tantance mai kaɗa ƙuri'a ta hanyar tantance zanen yatsu ko kuma fuska, tare kuma da aikawa da sakamakon zaɓen kai tsaye daga cibiyoyin zaɓen.

Jam'iyyar APC mai mulki a ƙasar da ma jihar ne ta lashe dukkan ƙananan hukumomi da kansiloli.

Abin da ya sa na fice daga PDP - Atiku

Atiku

Asalin hoton, Atiku team

Haka kuma a makon ne tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.

A wata sanarwa da ya fitar mai kwanan watan ranar 14 ga watan Yulin 2025, Atiku Abubakar ya ce "ina sanar da jama'a ficewata daga jam'iyyar PDP ba tare da ɓata lokaci ba."

"Ina son yin amfani da wannan damar na bayyana godiyata ga jam'iyyar ta PDP bisa irin damarmakin da ta ba ni: Na yi mataimakin shugaban ƙasa karo biyu a jam'iyyar sannan na yi takarar shugaban ƙsa karo biyu a PDP. A matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar ta PDP, saboda haka akwai sosa rai ƙwarai dangane da ɗaukar wannan hukunci." In ji Atiku.

Dangane kuma da dalilin da ya sa tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya bar jam'iyyar a wannan lokaci sanarwar ta ce:

'An kashe aƙalla mutum 27 a Filato'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rahotanni sun ce aƙalla mutum 27 ne ake zargin ƴanbindiga sun kashe a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya.

An kuma jikkata wasu da dama.

Wannan hari na zuwa ne kimamin wata ɗaya da kai wani hari da ya hallaka kusan mutum 200 a wani ɓangare na jihar.

Mazauna jihar sun bayyana kaɗuwa da harin, wanda suka ce ƴanbindigar da suka kai shi sun je ne ɗauke da manyan bindigogi a safiyar Talata.

Maharan sun bi gida zuwa gida, inda suka yi ta hallaka mutane da kuma cinna wa gidajensu wuta.

Wani jami'i a jihar ya shaida wa BBC cewa an ƙona wata jaririya mai kimamin wata uku tare da iyayenta.

Shi ma wani shugaban matasa ya bayyana cewa yawanci waɗanda lamarin ya rutsa da su, sun ƙone har ta kai ba a iya gane su.

Sun yi zargin cewa sojoji da ke kusa da wajen da aka kai harin sun ƙasa kai musu ɗauki yayin harin.

Ana sa ran gwamnan jihar ta Filato zai kai ziyara zuwa waɗannan al'ummomi da harin ya shafa - mai nisan kilomita 50 da Jos, babban birnin jihar.

An samu sauƙin hauhawan farashi a Najeriya -NBS

Kayan miya

Hukumar kididdiga ta ƙasa, NBS ta ce an samu raguwar hauhawan farashi da maki 22.22 cikin 100 idan aka kwatanta da maki 22.97 cikin 100 a watan Mayun 2025.

Rahoton da ta fitar ya ce idan aka haɗe alkaluman bana sun yi ƙasa da maki 11.97 cikin 100 idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a shekara ta 2024.

Hukumar ta ce ana iya ganin tasirin hakan a ɓangaren abinci da sauran kayan masarufi.

Tun bayan cire tallafin man fetur aka shiga cikin matsi na rayuwa da hauhawan farashin wanda ya je 'yan ƙasar cikin tasku.

Sai dai da wannan alkaluma idan aka cigaba da tafiya a haka babu mamaki nan gaba a samu sauki, in ji masana.

Yadda Lakurawa suka kashe yansanda uku a Kebbi

Lakurawa

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Asabar ce rundunar ƴansandan Najeriya ta ce ta tsaurara matakan tsaro a garin Zogirma na yankin ƙaramar hukumar Bunza ta jihar Kebbi, bayan wani hari da wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar Lakurawa ne suka kaddamar, inda suka kashe jami'an ƴansanda uku.

Rundunar ta ce bayan ƴansanda uku da aka kashe a yayin harin, akwai kuma wasu fararen hula biyu da suka samu rauni.

Kakakin rundunar ƴansandan jihar Kebbi, CSP Nafi'u Abubakar ya ce ''Jami'an mu da aka girke a Zogirma zuwa Tilli sun samu hari daga wasu da ake zargin ƴan ta'addan Lakurawa ne, inda suka yi musayar wuta kuma sanadiyyar haka su jami'an mu uku sun rasa rayukan su.''

CSP Nafi'u Abubakar ya ce itama rundunar ƴansandan ta yi wa maharan mummunar illar a lokacin arangamar.