Cutukan da suka kamata a yi kaffa-kaffa da su lokacin watan azumi

Lokacin karatu: Minti 4

A kowacce shekara miliyoyin Musulmai suna azumi tun daga fitowar rana har faɗuwarta, na tsawon kwanaki 29 ko 30 a cikin watan Ramadan.

Azumi yanayi ne da kan samar da daidaito da zaburar da jiki ga ayyuka da na'uin niƙa abinci, ko kuma atisaye na jikin ɗan'adam.

Sai dai, wasu mutanen da suka tsinci kansu cikin wani yanayi na rashin lafiya ko zama ba cin abinci yana zama matsala, inda ake ba su shawarar dakatar da yin azumi.

Mun tuntuɓi masana harkar kiwon lafiya domin jin irin cutukan da masu su za su yi taka tsantsan.

Gyambon ciki

Dakta Tasiu Ibrahim malami a sangayar koyar da aikin likita a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya ce ɗaya daga cikin cutukan da masu su za su yi kaffa-kaffa su ne gyambon ciki.

Ya ce waɗannan su kan tsinci kansu cikin yanayin rashin cin abinci zai zama matsala a gare su.

"Domin cikinsu na fitar da sinadarin acid da ke ƙona gyambon ciki matukar ba abinci suka ci ba. Suna irin mutane da ake son su yi taka tsantsan. Ana so ma su haƙura idan cutar ta yi tsanani," in ji Dakta Tasiu.

Ciwon suga

Likitan ya ce ana son masu ciwon suga su riƙa cin abinci kaɗan-kaɗan a lokuta makusanta.

Ya ce cin abinci da yawa yana janyo matsala ga masu ciwon suga har ta kai sai sun je wurin likita.

Masu cutuka da ke kan magani

Dakta Tasiu Ibrahim ya ce akwai waɗanda ke da wani yanayi na rashin lafiya da ya shafi ciwon daji ko sanakara su ma ya kamata su riƙa kula.

"Akwai waɗanda suna yanayin na rashin lafiya da ake ɗorawa kan magani ko cin abinci. Misali idan akwai waɗanda likita ya ce dole ne su sha magani sau biyu ko uku a rana to dle su yi duba kan rashin lafiyarsu," in ji shi.

Nau'in mata masu juna biyu da masu shayarwa

Likitan ya ce akwai nau'in mata masu juna da masu shayarwa da su ma ya kamata su kula.

Ya ce watakila akwai mai karamin ciki wadda take iya samun yin azumi duka da kuma wadda cikin ya girma ba ta iya zama da yunwa sai ta ci abinci - duka waɗannan ya kamata su yi kaffa.

"Sai kuma mace mai shayawar ko da ta gama biki ya kamata ta kula. Tana buƙatar abinci ita ma kafin shayar da yaro don haka za ta yi duba da kuma neman fatawar yadda za ta yi," in ji dakta Tasiu.

Masu lalurar makoko

Wane nau'in cutar da ya kamata masu ita su kula ita ce lalurar makoko, in ji likitan.

Ya ce lalurar na janyo kumburi a wuya da kuma zazzagowar idanu.

"Irinsu suna fama da ƙarfin ƙonar abinci saboda sinadarin da suke samarwa ya sa tsarin jikinsu na aiki cikin sauri inda duk abin da aka ci cikin sauri yake narƙewa. Irin waɗannan mutane su ma ba za su iya azumi ba saboda yanayin da suka samu kansu a ciki," in ji dakta Tasiu Ibahim.

Ya ce duka masu irin waɗannan cutuka akwai buƙatar su nemi shawarar likitoci na yanda za su kula da kansu.

Wane nau'in abinci ya kamata su ci?

Dakta Tasiu Ibrahim ya ce akwai irin nau'in abincin da kowace lalura ke buƙata.

Ga waɗanda ma za su iyaazumi su je asibiti don ba su shawara kan irin abincin da ya kamata su ci.

"Akwai abincin da ke riƙe jiki da wanda ba ya narƙewa cikin sauri, irinsu ne za su iya riƙe jiki zuwa na dogon lokaci ta yanda ba za su saka mai azumi ko lalura ya jiga ta ba.

"Amma kowanne abinci ya ta'allaka da na'uin lalurar da ake so a kula da ita. Asibiti ko likita su ne za su iya bayar da shawara ga mara lafiya kan abin da ya kamata ya ci ko ya kiyaye," in ji likitan.

Me za su yi don kula da kansu lokacin azumi?

Babban abin da za su kula da shi, shi ne ɗaukar hanyar da ta dace kada su takurawa kansu na lallai sai sun yi azumi, in ji dakta Tasiu.

"In kuma za su iya azumi su je asibiti a ba su shawarwari. Akwai waɗanda za su iya azumi amma sai su shagwaɓe ko shantaƙewa su ki jin tsoron Allah musamman wasu matasa. Ba su ne za su yanke wa kansu hukunci ba sai dai likita," in ji likitan.

Ya ce likitan ko da ba Musulmi bane matuƙar ya san aikinshi zai iya ba da shawara.