Ko yin Azumi na taimakawa wajen rage ƙiba?

    • Marubuci, Philippa Roxby
  • Lokacin karatu: Minti 2

Zabar wasu ranaku da niyyar yin azumi domin rage kiba ba mafita ba ce.

Masu bincike sun ce yin azumi a wasu ranaku da wasu mutane ke yi ko kuma kin cin wasu abubuwa da suka saba ci a baya don su rage kiba ba ya taimakawa wajen rage kiba.

Amma duk da haka sun ce yin azumin a wasu ranakun yana taimakawa lafiyar dan'adam.

Masu binciken sun yi bincike a kan wasu mutane dubu biyu domin gano ko yin azumi a wasu ranaku na taimakawa wajen rage kiba musamman idan aka kwashi kamar watanni 12 ana yi.

Masu binciken sun ce yin hakan kan taimakawa masu kiba idan har za su kwashe tsawon wannan lokaci suna azumin, don ya fi su sauya yanayin cin abinci ko kuma daina cin wasu abubuwa da nufin rage kibar.

A shekarun baya-bayan nan mutane musamman masu kiba kan yi azumin a wasu ranaku domin su rage kiba.

Wasu kuma kan zabi wasu lokuta da suke cin abinci da kuma lokutan da ba sa ci kamar misali da daddare a ci a kwanta duk su kan kaucewa irin hakan duk don dai su rage kiba.

Kuma idan mutane suka dauki irin wannan matsaya akan da ce amma ba lallai ba saboda ya danganta da irin abincin kuma da mutum ke ci.

Luis Garegnani, shi ne jagoran mutanen da suka yi bincike daga Italiya, ya ce ya damu da irin shawarwarin da ake bayar wa a intanet a kan yadda mutum zai rage kiba musamman idan aka ce mutum ya yi azumi.

Ya ce," Yin azumi a wasu ranaku zai iya zama silar rage kiba ga wasu mutane, to amma bincike ya nuna ba lallai hakan ta kasance ba kamar yadda ake gani a kafafan sada zumunta."

Amma duk da haka masu binciken sun amince cewa kowanne dan'adam da yanayin nasa jikin, don haka wasu za su iya amfana da wannan dabara. A don haka yana da kyau likitoci sun rinka duba yanayin mutum kafin a ba shi shawarar abin da zai yi idan yana son rage kiba.

Masu binciken sun ce akwai bukatar a kara zurfafa bincike domin gano fa'idar yin azumi a wasu ranaku da kuma batun lafiyar dan'adam musamman idan aka yi la'akari da masu lalurar ciwon suga da kuma wasu cutukan masu hadari.

Sannan kuma sun ce shi kansa azumin ya rabu gida-gida, don haka yana da kyau a gano ta yadda zai yi amfani ga mata da maza da ma yanayin mutane.

Dr Baptiste Leurent, na wata jami'ar kiwon lafiya da ke London, ya ce idan aka yi nazari akan yadda yanayin jikin kowanne dan'adam ya ke to za a gane cewa yin azumin a wasu ranakun zai iya yi wa aiki wasu kuma ba lallai suga amfaninsa ba.

Farfesa Keith Frayn, na jami'ar Oxford da ke London, ya ce ana yawan cewa mutane su yi azumi don su rage kiba to hakan ma yana da tasa illar.

A kusan ko'ina a duniya an yarda cewa yin azumi a wasu ranaku hanya ce ta rage kiba, to amma duk da haka yana da tasa illar, amma duk da haka ya kan taimaka wajen rage yawan maiko a jikin dan'adam da sikari da dai sauransu.

Kusan mutane miliyan 1 da dubu 600 a Birtaniya na amfani da da allura don su rage kiba.

Kuma bincike ya gano cewa idan har masu amfani da irin wannan allura ta rage kiba suka daina to kibar za ta dawo har ma ta rubanta ta baya.