Ƙauyen da al’ummarsa ke cikin barazanar ƙarewa saboda ƙarancin haihuwa

- Marubuci, Sarah Rainsford
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Southern and Eastern Europe correspondent
- Aiko rahoto daga, Veneto region, Italy
- Lokacin karatu: Minti 7
Yayin da ya kusa kure karshen babban hanyar da ta ratsa cikin garinsu da ke arewacin Italiya, dan asalin garin mai suna Giacomo de Luca na kallon shagunan da ke rufe; manyan kantuna biyu da shagon aski da wurin cin abinci - duk an rufe su. Sai kawai rubutun da ke saman kofofinsu wanda ya dusashe har ma yake kokarin bacewa.
Kayataccen garin Fregona da ke a wuri mai yawan tsaunuka yana kara zama kufai kamar sauran garuruwa da dama, kasancewar Italiyawan yankin sun kasance suna da karancin haihuwa sannan suna yawan yin kaura zuwa manyan birane ko ma tafiya kasashen waje.
A yanzu ita ma makarantar firamare da ke garin tana fuskantar barazana kuma lamarin ya jefa magajin garin cikin damuwa.
"Ba za a ci gaba da zangon karatu na ajin farko ba saboda yara hudu ne kawai a aji. Suna son su rufe," In ji De Luca. Adadin dalibai a aji mafi karanci da za su samu tallafi shi ne yara 10.
"Haihuwa da yawan al'umma na raguwa sosai."
Magajin garin ya kiyasta yawan al'ummar Fregona, mai nisan sa'a daya daga arewacin Venice, ya yi kasa da kusan kashi daya bisa biyar cikin shekaru 10 da suka gabata.
Daga Janairu zuwa watan Yunin bana jarirai hudu kawai aka haifa kuma galibin mazauna yankin da suka rage su 2,700 tsofaffi ne, daga maza masu shan giyar prosecco zuwa matan da ke cika jakunkunansu da ganyen chicory da tumatur a kasuwar da ke ci kowane mako.

Ga De Luca, rufe karbar dalibai a makarantar shi ne mataki mafi dacewa: idan yara suka bar Fregona don karatu, yana fargabar ba za su sake komawa ba.
A don haka yake rangadi a yankin, har ma ya ziyarci wata masana'antar yin gurasar pizza yana kokarin shawo kan iyaye da su tura yaransu zuwa garinsa don su taimaka wajen kasancewar makarantar ta ci gaba da aiki.
"Ina tayin zuwa daukansu a yar karamar bas, mun yi tayi ga yara su zauna a makaranta har sai shida na yamma, duka hukumar gudanarwar yankin ce za ta dauki nauyin biya," kamar yadda magajin garin ya shaida wa BBC.
"Ina cikin damuwa. Da kadan da kadan, idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka, kauyen nan zai zama kufai."
Matsala ta gama-gari
Matsalar karancin al'umma da Italiya ke fama da ita ta zarce Fregona kadai, tana kara tabarbarewa.
Cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan mutanen kasar ya ragu da kusan miliyan 1.9 kuma haihuwa ta ragu tsawon shekaru 16 a jere.
A matsakaicin mataki, matan Italiya na haihuwar jarirai 1.18, mataki mafi kankanta da aka taba gani a tarihi. Mataki ne da bai kai matakin haihuwa na 1.38 da Tarayyar Turai ta gindaya ba kuma ya yi kasa sosai da matakin 2.1 da ake bukata domin ci gaban al'umma.
Duk da kokarin bai wa iyaye kwarin gwiwar su haihu, da kuma yawan magana kan siyasa da ta yi daidai da tsarin iyali, gwamnatin Giorgia Meloni mai sassaucin ra'ayi ba ta iya kawo sauyi dangane da haka ba.
"Dole ka yi tunani sosai kafin ka haihu" in ji Valentina Dottor da muka hadu a babban dandalin Fregona, yarta yar wata 10 Diletta tana wasa a kujerar jarirai.

Valentina na samun albashin kusan fam 175 duk wata tsawon shekara daya na diyarta sai dai ta yi rashin sabon tagomashin gwamnati da take bai wa jariran da aka haifa 1,000 ga yaran da aka haifa a 2025.
Akwai sassaucin biyan haraji da kuma samun hutun raino mai tsawo.
Sai dai Valentina a yanzu tana bukatar ta koma aiki inda ta ce samun wurin raino mai saukin kudi, abu ne mai wuyar gaske.
"Babu jarirai da yawa amma babu isassun wuraren rainon yara, a cewarta. "Na yi sa'a kakata tana kula min da yata. Idan ba haka ba, ban san inda zan rika kai ta ba."
Shi ya sa kawayenta suke dari-darin haihuwa.
"Akwai wahala - saboda aiki, makaranta da kudi," in ji Valentimna. "Akwai taimako amma bai isa ba da har mutum zai yi ta haihuwa.
"Ba zai warware matsalar ba."
Tsare-tsaren taimakon kai da kai
Wasu kamfanoni a yankin Veneto sun dauki ragamar halin da ake ciki.
Yanki ne da ba shi da nisa daga Fregona kuma ya kasance wuri na masana'antu, da iyalai da dama ke tafiyarwa.
Irinox mai kera na'urar sanyaya abinci, ya gano matsalar da iyaye ke fuskanta da dadewa kuma ya yanke shawarar daukan mataki a maimakon rasa ma'aikata.
Kamfanin ya hada karfi da karfe da wasu kamfanoni bakwai domin gina makarantar reno da ba ta da nisa daga masana'antar - ba kyauta ba ce amma ba ta da tsada kuma ta kawo wa iyaye kwanciyar hankali. Ita ce makaranta irin ta ta farko a Italiya.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Sanin cewa ina da damar sa dana a makarantar da ba ta da nisa daga nan, yana da muhimmanci saboda zan iya zuwa inda yake kowane lokaci nake so, cikin sauri," in ji daya daga cikin masu kula da bangaren kudi na kamfanin Melania Sandrin.
Da babu makarantar renon, za ta fuskani kalubale a komawarta wajen aiki: ba ta son ta dogara a kan iyayenta kuma makarantun kula da yara na gwamnati ba za su kula da yaro tsawon yini ba.
"Akwai muhimman bukatu... kuma akwai wurare kalilan," in ji Melania.
Kamar Valentina, ita da kawayenta sun ba da lokaci kafin su haihu yayin da suke da shekaru 30, sun zaku su gina makomarsu a fannin aikin da suke, Melania ba ta da tabbas ko za ta haifi yaro na biyu, ko a yanzu ma "ba abu ne mai sauki ba," in ji ta.
Haihuwa daga baya, da ke neman zama ruwan dare a nan, wani dalili ne na raguwar haihuwa da ake gani.
Duka wadannan ne ya sa shugabar kamfanin Irinox Katia da Ros take tunanin Italiya na bukatar yin sauye-sauye muhimmai domin magance matsalar raguwar al'umma.
"Ba batun euro 1,000 da ake biya ba ne zai kawo sauyi, sai dai samar da makarantun renon yara kyauta. Idan muna son mu gyara lamarin dole mu dauki mataki kwakkwara," in ji ta.

Daya maslahar ita ce yawan yin kaura, wadda ta fi kawo wa gwamnatin Meloni cece-kuce.
Fiye da kashi 40 cikin 100 na ma'aikata a kamfanin Irinox sun fito ne daga wasu kasashen.
Wata taswira da aka manna a bango ta nuna cewa ma'aikatan sun fito daga Mongolia zuwa Burkina Faso. Katia da Ros na ganin Italiya - kamar Veneto - za ta bukaci karin ma'aikata baki domin tafiyar da tattalin arzikinta.
"Makomar za ta kasance haka."
Karshen zamanin makarantu
Batun kaura ma bai iya taimakon wata makaranmta da ke Treviso mai makwabtaka ba.
A watan da ya gabata, makarantar Pascoli ta rufe kofofinta har sai baba ta gani saboda rashin wadatar dalibai da za su sa makarantar ta ci gaba da aiki.

Yara 27 ne suka taru kan matattakalar makarantar domin bikin karshe na rufe ta yayin da aka yi kasa-kasa da tutar Itakiya.
"Rana ce ta bakin ciki," in ji Eleanora Franceschi, da ta zo daukan yarta mai shekara 8 karo na karshe. Daga Satumba, dole ta yi tafiya mai nisa zuwa wata makarantar.
Eleanora ba ta yadda cewa raguwar haihuwa ce kadai ta janyo rufe makarantar ba: ta ce makarantar Pascoli ba ta koyarwa da rana, lamarin da ke bai wa iyaye masu zuwa aiki ciwon kai wadanda daga bisani suka sauyawa yaransu makaranta.
Shugabar malamai ta yi wani bayani na daban.
"Wannan yankin ya sauya saboda mutane da yawa daga kasashen waje suna zuwa nan," kamar yadda Luana Scarfi ta fada wa BBC, tana nuni da shekaru 20 na kaura zuwa yankin Veneto da ke da masana'antu masu yawan gaske da kuma damarmaki na ayyukan yi.

Wasu [iyalai] sun yanke shawarar zuwa wasu makarantu inda yawan baki ba shi da yawa."
"Cikin shekaru da suka gabata, muna samun raguwar mutanen da suke zuwa wannan makaranta," in ji shugabar malaman.
Wani hasashe na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa yawan al'ummar Italiya zai ragu da kusan miliyan biyar cikin shekaru 25 masu zuwa, daga miliyan 59. Yawan dattawa na karuwa, lamarin da ke kara wa tattalin arzikin kasar nauyi.
Matakan gwamnati na magance matsakar zuwa yanzu ba su yi wani tasiri ba.
Sai dai Eleanora na ganin iyaye kamar ta na bukatar karin taimako ba wai kawai kudi ba.

"Muna samun chekin kudi a kowane wata amma muna bukatar tallafi a aikace kamar sansanin kula da yara a lokacin bazara," in ji ta, tana nuni da hutun wata uku da yara ke yi daga Yuni wanda ke zama tashin hankali ga iyayen da suke zuwa aiki.
"Gwamnati na son karuwar al'umma amma a lokaci guda kuma, ba ta taimakawa," in ji Eleanora.
"Ta yaya za mu yi ta haihuwa a irin wannan yanayin?"
Wanda ya shirya: David Ghiglione.











