Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea da Man Utd na hamayya kan Yildiz, Everton na zawarcin Phillips
Manchester United na shirin gabatar da tayin fam miliyan 78 kan ɗan wasan Juventus da Turkiyya Kenan Yildiz, mai shekara 20, yayin da ita ma Chelsea ke zawarcin ɗan wasan.(Caught Offside)
Everton na nazarin yiwuwar ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Manchester City Kalvin Phillips, mai shekara 29 a watan Janairu. (Football Insider)
Liverpool na cikin jerin ƙungiyoyin Ingila da ke zawarcin ɗan wasan Crystal Palace da Ingila Adam Wharton mai shekara 21. (Mail)
Ba a sa ran Brentford za ta bai wa ɗan wasan Jamaica Michail Antonio, mai shekara 35 kwantiragi, duk da cewa tsohon ɗan wasan na West Ham na atisaye tare da ƙungiyar. (Mail)
Manchester United ta ci gaba da tattaunawa da Harry Maguire, mai shekara 32, kan sabuwar yarjejeniya kuma tuni aka yi wata ganawa tsakanin ƙungiyar da wakilan ɗan wasan bayan Ingilan, wanda kwantiraginsa zai ƙare a bazara mai zuwa. (Fabrizio Romano)
Yayin da ta ke harin sayen sabon ɗan wasan tsakiya a bazara mai zuwa, Manchester United na nazari kan ɗan wasan Brighton da Kamaru Carlos Baleba, mai shekara 21, da ɗan wasan Ingila da Nottingham Forest Elliot Anderson, mai shekara 22 (Sky Sports)
Crystal Palace na shirin tafiyar Marc Guehi, ko dai a lokacin kasuwar musayar ƴan wasa ta Janairu ko kuma bazara mai zuwa, inda Liverpool da Barcelona da Real Madrid ke cikin ƙungiyoyin da ke ci gaba da zawarcin ɗan wasan bayan Ingilan mai shekara 25. (Express)
Napoli na son ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Manchester United Kobbie Mainoo a matsayin aro a watan Janairu duk da cewa ta yanke shawarar ƙin neman ɗan wasan na Ingila mai shekara 20 a bazarar da ta gabata. (La Gazzetta dello Sport)
Ɗan wasan bayan Nottingham Forest da Brazil Murillo, mai shekara 23, na ɗaya daga cikin sunayen da ke kan gaba a jerin waɗanda Chelsea ke zawarci yayin da ta ke ƙoƙarin ƙarfafa masu tsaron bayanta. (Football Insider)
Ɗan wasan Chelsea da Sifaniya Marc Guiu yana sa ran komawa Sunderland a kasuwar musayar ƴan wasa ta watan Janairu duk da cewa ɗan wasan mai shekara 19 ya dawo daga zaman aro daga ƙungiyar a watan Agusta. (GiveMeSport)