Darussa huɗu da aka koya daga korona shekaru biyar bayan annobar

Gwaji

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Isabel Caro
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 6

Shekaru biyar ke nan tun bayan da hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana cutar korona a matsayin annoba a ranar 11 ga Maris ɗn 2020.

Gwamnatoci sun ɗauki matakan da ba a yi zato ba da suka jefa mutum biliyan 2.6 cikin yanayi na kulle na tsawon watanni.

Mutum sama da miliyan 777 ne suka kamu da cutar sannan ta janyo mace-macen fiye da mutum miliyan bakwai, a cewar alƙaluman WHO. Hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta cewa mace-macen da korona ta haddasa a yanzu sun kai mutum miliyan 15.

Har yanzu ana ganin tasirin annobar korona a faɗin duniya sai dai wasu masu nazari sun ce akwai darussa da aka koya daga wannan lokaci.

Elke Van Hoof, wata ƙwararriya kan yaye damuwa da firgici, kuma tsohuwar farfesa a ɓangaren tunanin ɗan'adam a jami'ar Vrije da ke Brussels a Belgium, ta bayyana cewa lokacin kulle shi ne gwajin tunanin ɗan'adam mafi girma a tarihi."

Ga abubuwan koyi:

Margaret Keenan ce mutum ta farko a yammacin duniya da ta karɓi allurar rigakafin korona a Birtaniya a Disamban 2020 zaune kan kujera launin shuɗi tare da wata malamar jinya sanye da kayan ariya daga cutar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata dattijuwa a Birtaniya ce mutum ta farko a duniya da aka fara yi wa allurar korona ta kamfanin Pfizer a Disamban 2020 a wani ɓangare na shirin yi wa mutane rigakafin cutar.

Nasarori kan samar da allurar rigakafi

Masana kimiyya sun ɗauki tsawon watanni tara ne kawai kafin su samar da rigakafi don yaƙar nau'in ƙwayar cutar mai suna Sars-Cov-2. Sannan sun samar da rigakafin ta hanyar amfani da fasaha da a yanzu ta sauya ci gaban allurorin rigakafi a duniya.

Duniya ta yi koƙarin yin bincike kan hanyar haɗa rigakafi ta hanyar amfani da fasahar RNA amma hakan ba ta tabbata ba har sai lokacin korona.

An yi amfani da fasahar RNA a binciken da kamfanin Pfizer na Amurka ya yi haɗin gwiwa da BioNtech na Jamus da kuma Moderna na Amurka, suka yi wajen samar da rigakafin, abin da ya bai wa miliyoyin mutane damar karɓar allurar da za ta kare su daga munanan tasirin ƙwayar cutar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Margaret Keenan, wata dattijuwa mai shekara 90 a duniya daga Birtaniya, ta zama mutum na farko a yammacin duniya da ta karɓi allurar ranar 8 ga Disamban 2020. Masana kimiyyar da suka ƙirƙiri rigakafin, Katalin Kariko da Drew Weissman, sun karɓi lambar yabo ta Nobel a 2023.

Dakta Margaret Harris, wata ƙwararriya kan lafiyar al'umma a WHO ta bayyana tseren gano rigakafin a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan koyi daga korona. "Mun ga ci gaba a ɓangaren fasaha cikin ƙanƙanin lokaci," in ji Dakta Harris.

"Dama an san Fasahar RNA amma yanzu ana ganin yadda ake amfani da ita wajen bunƙasa sauran allurori, har da rigakafin cutar daji," in ji ta.

Farfesa a Jami'ar Edinburgh, Devi Sridhar kuma marubuciyar littafin yadda annoba ta sauya duniya da yadda za a kare ɓullar ta gaba, ta ce darussan da aka koya daga korona sun ƙara inaganta hanyoyin bincike da gano ɓullar sabbin ƙwayoyin cuta.

"Ƙarfin kimiyyarmu ya inganta, ana samun ci gaba sosai," in ji ta. "Idan da tambayar da muka fara samu a farkon annobar ita ce ko za a samu rigakafi, tambayar a yanzu ita ce, 'ta yaya za mu samar da ita cikin sauri?".

Akwai kuma darussa a yadda za a shirya tunkarar annoba ta gaba, in ji ta. Misali, ƙasashen da alamu suka nuna sun yi abin da ya dace, su ne masu lafiyayyar al'umma kafin zuwan annobar."

Ɗaliban makarantun firamare a Jamus sanye da takunkumi suna hawa sama.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda aka gaggauta rufe makarantu lokacin annobar ya taimaka wajen sanya ilimi a sahun gaba cikin jadawalin abubuwan da ƙasashe suka tattauna

Sabon babi ga ilimi

Rufe makarantu ya yi wa yara illa a faɗin duniya. Samun ƙaruwar masu barin makaranta da kuma jinkirin koyarwa a matakin firamare da sakandare har yanzu shi ne ɗaya daga cikin tabon da har yanzu korona ta bari, a cewar Mercedes Mateo, shugaban sashen ilimi na Bankin IDB.

Amma duk da koma-bayan, Mateo na ganin an samu kyakkyawan sauyi a yadda ake kallon harkar ilimi. "An samu kyakkyawan sauyi wajen shigar da muhawara kan ilimi zuwa ƙarni na 21, [...] domin sake tunani kan tsarin ilimi," kamar yadda ta shaida wa BBC.

"A lokacin annobar, ta bayyana ƙarara cewa ɓangaren ilimi ɗaya ne daga cikin ɓangarorin da ba a zamanantar ba," a bayanin Mateo. Sai dai korona ta tilasta samar da wata hanya wajen samar da tsarin karatu daga gida, in ji ta.

Kazalika a wurin Mateo, annobar ta buɗe kafofin wayar da kai game da rawar da makarantu ke takawa a zamanin yanzu.

Hoton wata malama da aka ɗauka daga sama a gida tana koyar da ɗalibai ta hanyar bidiyo.

Asalin hoton, Getty Images

Gagarumin sauyi a wurin aiki

Rasa ayyukan yi da talaucin da aka gani na daga cikin manyan illolin cutar korona. Annobar ta kuma sa tsirarun matasa da mata fafutukar neman aiki, wanda har yanzu ke zama ƙalubale mafi girma na annobar.

Ɗaya daga cikin abubuwan da aka koya daga lokacin korona shi ne tsare-tsaren ayyuka da kare kuɗaɗen shiga - kamar rage ma'aikata - ya taimaka wajen magance illar koma-bayan, in ji Gerson Martinex, wani ƙwararre kan ririta ayyukan yi da ke ƙungiyar ƙwadago ta duniya, ILO. Ba shi da shakku cewa waɗannan hanyoyin sun haifar da farfaɗowar tattalin arziki cikin hanzari.

Sauyin da aka gani shi ne yadda aka koma aiki daga gida. Duk da a yanzu kamfanoni da dama na neman komawa tsarin yin aiki daga ofis, shaidun alfanun yin aiki daga gida ya rabu gida biyu.

Elke Van Hoof, wata ƙwararriya kan yaye damuwa da firgici, kuma tsohuwar farfesa a ɓangaren tunanin ɗan'adam a jami'ar Vrije da ke Brussels a Belgium, ta bayyana cewa lokacin kulle shi ne gwajin tunanin ɗan'adam mafi girma a tarihi."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Elke Van Hoof, wata ƙwararriya kan yaye damuwa da firgici, ta bayyana cewa lokacin kulle shi ne gwajin tunanin ɗan'adam mafi girma a tarihi."

Fifita lafiyar ƙwaƙwalwa

Zaman kulle da rashin tabbas da kaɗaici da fargabar da aka gani a duniya sun sa rayuwa a lokacin korona kasancewa ta firgici.

Hukumomi kamar WHO da PAHO sun gudanar da zuzzurfan nazari kan ƙaruwar damuwa da kuma raya kashe kai sakamakon annobar.

Sai dai wata ƙwararriya kan tunanin ɗan'adam Laura Rojas-Marcos ta ce korona ta yi tasiri sosai kan tunaninmu da mu'amalarmu [...] Ya kasance lokaci na koyo ba wai kawai na shan wuya ba.

Ta ce a yanzu mun fi sanin muhimmancin yadda za mu kula da lafiyar ƙwaƙwalwarmu, "ba wai a matsayin wani sashe na daban a jikinmu ba.

"Mutane, sun yi amfani da damar wajen sake yin nazari kan rayuwarsu tare da koyon kula da lafiyar ƙwaƙwalwar mutane," in ji ta.

Wani bincike da aka yi a 2022 wanda BBC ya ƙaddamar daga kamfanin GlobeScan, ya gano cewa kashi ɗaya bisa uku na mutanen da aka yi binciken a kansu da ke ƙasashe 30 sun ce sun fi jin daɗin jikinsu a kan gabanin zuwan korona. Galibinsu sun ba da rahoton cewa sun fi kasancewa tare da iyalinsu; sun ƙara samun kyakkyawar dangantaka da mutane da kuma yanayi da kuma samun kyakkyawar fahimta kan abubuwan da suka fi fifitawa. Waɗannan sauye-sauye sun yi kyakkyawan tasiri, a cewar ƙididdigar.

Annobar ta kuma samar da wani sauyi mai ɗorewa na yadda masu ilimin tunanin ɗan'adam ke bayar da kulawa ta hanyar bidiyo. Wannan sauyin ya bai wa masu wannan ilimin damar misali, bai wa sojojin Ukraine kulawa ana tsaka da yaƙi ko sauran masu buƙatar kulawa da ke zaune a yankuna masu nisa.

Annobar ta sa mutane daina tunani game da jajircewa da tausayawa, abubuwa biyu da a cewar Rojas-Marco, sune kan gaba a tsarin rayuwar bil'adama.