Yadda masu zanga-zanga suka kawo ƙarshen mulkin shugabar Bangladesh na shekara 15

Asalin hoton, Getty Images
Firaiministan Bangaladesh, Sheikh Hasina ta ajiye muƙaminta tare da ficewa daga ƙasar.
Rahotonni sun ce Hasina mai shekara 76, wadda ta mulki ƙasar tun daga shekara ta 2009, ta isa Indiya domin neman mafaka.
Mutane sun fantsama kan tituna cikin murna a ranar Litinin, inda wasu suka kutsa fadar firaministar tare da wawashe kayayyaki a tsohon gidanta da ke Dhaka babban birnin ƙasar.
Shugaban rundunar sojin ƙasar, Waker-Uz-Zaman, ya ce za su fara tattaunawa kan yadda za a kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya.
'Yan awanni bayan saukarta daga mulki ne kuma Shugaban Ƙasa Mohammed Shahabuddin ya ba da umarnin sakin tsohon firaminista kuma jagoran adawa Khaleda Zia daga gidan yari.
Ajiye mulkin Hasina ya zo ne bayan dubban masu zanga-zanga sun fantsama kan titunan ƙasar suna neman ta sauka daga muƙaminta.
Kwana ɗaya kafin ajiye mulkin Hasina, an samu mummunar arangama tsakanin masu zanga-zanga da ƴansanda, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 90.

Asalin hoton, EPA
Kimanin mutum 300 ne aka kashe a ƙasar ta Bangaladesh bayan kwashe wata ɗaya ana zanga-zangar adawa da gwamnatin ƙasar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A watan da ya gabata ne ɗalibai suka fara wata zanga-zangar lumana suna neman gwamnati ta yi watsi da tsarin raba-daidai na ayyukan gwamnati, sai dai tun daga wancan lokacin lamarin ya ƙazance zuwa adawa da gwamnatin ƙasar baki ɗaya.
Daga nan ne masu zanga-zangar suka koma kiraye-kirayen saukar firaiministar daga kan muƙaminta.
Sheikh Hasina ƴar shugaban kasar da ya kafa Bangladesh ce kuma ita ce macen da ta fi kowacce dadewa a kan mulki a duniya.
A shekaru 15 da ta shafe a kan mulki, akwai zargi mai karfi na cewa mutane na bacewa, ana gallaza wa masu adawa. Zarge-zargen da ta musanta.
A cikin 'yan makonnin nan, Hasina da jam'iyyarta ta Awami sun zargi 'yan adawa da jawo rikici a kasar.
An kiyasta cewa dubun dubatar jama'a ne suka shiga zanga-zangar ba ɗalibai kawai ba. Wannan kuma shi ne kalubale mafi girma da ta fuskanta tun bayan sake zabenta a yanayi me cike da cece-kuce a watan Janairu.
Hasina ta soke tsarin guraben aiki da ya janyo bore tun daga farkon watan Yuli. Amma kuma dalibai sun ci gaba da zanga-zanga suna kira ta sauka daga kujerarta.

Asalin hoton, Reuters
'An yi wa mahaifiyata butulci'
Abokan siyasar Hasina sun ce ba za ta sake shiga siyasar ƙasar ba bayan ta shafe jimillar shekara 20 a gadon mulkin ƙasar tun daga shekarar 1996.
Ɗanta mai suna Sajeeb Wazed ya faɗa wa BBC cewa: "Ta kai sama da shekara 70. Tana baƙinciki a ce bayan duk ƙoƙarin da ta yi, amma a ce wasu tsiraru sun kore ta, ina ganin shikenan kuma.
"Ni da dangina mun gama da wannan."
Sai dai masu adawa da ita kan ce mulkin Hasina na cike da korar mutane, da kisan azarɓaɓi, da kuma muzguna wa 'yan'adawa.
Amma Wazed, wanda mai bai wa tsohuwar firaministan shawara ne kan harkokin fasaha ya kare ayyukan mahaifiyar tasa.
"Ita ce ta sauya Bangladesh cikin shekara 15 da suka wuce.
"Ana kallon ƙasar a matsayin ƙasƙantaciya lokacin da ta hau mulki. Matalauciyar ƙasa.
"Amma a yanzu ana yi mata kallon masu tashe a nahiyar Asiya."











