Abu 5 da suka fito fili a rikicin Ɗangote da Farouk Ahmed

Asalin hoton, Getty Images/BBC
Babban batun da ya fi jan hankalin ƴan Najeriya a makon nan shi ne musayar yawu tsakanin shugaban kamfanonin Dangote, Aliko Dangote da shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya NMDPRA, Ahmed Farouk.
Al'amarin ya yi amon da har ta kai ga hukumar yaƙi da almundahana ta Najeriya ICPC, ta ce za ta yi bincike.
Bugu da kari, rikicin ya raba kan ƴan Najeriya biyu, inda wani ɓangare ke ganin abin da Ɗangote ya yi daidai ne sannan ɗaya ɓangaren yake kallon bai kamata ba inda suke goyon bayan Farouk Ahmed.
BBC ta yi nazari da bibiyar mahawar da al'amarin ya janyo inda ta fito da wasu abubuwa guda 5 da suka fito fili a sa-in-sar.
Tonon silili
Wani abu da ya fito fili daga wannan sa-in-sa shi ne yadda idan rai ya ɓaci ko kuma aka samu banbanci wajen biyan buƙata ko muradi, a kan iya ɗaukar matakin da wasu ka iya ganin na wuce gona da iri ne.
Wasu ƴan Najeriya na yi wa zargin da Aliko Ɗangote ya yi wa Farouk Ahmed cewa yana biya wa ƴaƴansa guda huɗu kuɗin makarantar sakandire a Switzerland da suka kai yawan dala miliyan biyar, kallon tonon silili.
"A shekara shida da suka yi su huɗu abin da ya biya shi ne dala miliyan biyar...Ka ga kuwa mutumin da yake ɗaukar albashi ai ba zai iya biya wannan kuɗi ba. Ko ni kaina da nake ɗan kasuwa ai ba zan yi wannan haukan ba, saboda na san akwai mutane a Kano da ba sa iya biyan kudin makarantar ƴayansu naira 100,000. Kuma mun san babansa ba ɗan kasuwa ba ne," in ji Dangote, a wata tattauna da ya yi da ƴan jarida a Legas.
Kare muradi
Hausawa kan ce wai wanda ruwa ya ci to ko takobi ka ba shi zai kama. Hakan ya nuna yadda shugaban kamfanin Ɗangote, Aliko Ɗangote yake neman wani abu da zai kama domin kare muradinsa da yake tunanin za a illata.
"Ai dole ne na yi hakan saboda idan ban yi ba ai ba zan rayu ba saboda sun matsa cewa lallai sai sun kashe wannan ma'aikata tamu. To ka ga kuwa ai ba zai yiwu ba ka saka dala biliyan 20 sannan wani ya zo ya ce zai kashe maka kasuwanci ba. Dole ne ka yi ƙoƙarin ganin cewa ka rayu," kamar yadda Dangote ya faɗi.
Kafin kafa wannan matata dai ƴan Najeriya sun shaida cewa Ɗangote mutum ne ba mai son magana a kafafen watsa labarai ba amma sai ga shi yana ta tattaunawa da kafafen watsa labaran Najeriya.
Kwarmatawa
Tata-ɓurzar tsakanin mutanen guda biyu ta kuma fito da irin yadda ƴan Najeriya za su iya kwarmata bayanai da ka iya janyo hankalin hukumomi masu yaƙi da rashawa da cin hanci su bibiya domin yin bincike.
Ɗangote ya ce yana kira ga hukumar da ke yaƙi da almundahana ta Najeriya ICPC ta ta yi bincike kan zargin.
" Ya kamata a bincike shi ko kuma ya fito ya gaya wa mutanen idan babansa ne ya biya masa. To amma mun san cewa babansa ba ɗan kasuwa ba ne. Kowaye ya biya a zo a faɗa cewa ga shi," in ji Aliko Ɗangote.
Tuni dai hukumar yaƙi da almundahana ta Najeriya ICPC ta ce za ta yi bincike kan zargin da shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi wa shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya NMDPRA, Ahmed Farouk.
Hukumar ta ce Dangote ya mika mata ƙorafi a ranar Talata, inda ya zargi Farouk da cin hanci da rashawa da almundahanar kuɗaɗen gwamnati.
Rashawa da cin hanci
Rikicin ya fito da irin girman rashawa da cin hanci da ke harkar mai a Najeriya.
Dangote ya yi zargi cewa wani gungun mutane da ya kira "Mafia" waɗanda ya ce su ne suke son hana ruwa gudu a masana'antar tasa saboda rashawar da suke samu daga man da ake shigar da shi Najeriya.
"Man da ake ta ambaliyo shi daga waje domin a tabbatar ba mu sayar da namu ba," in ji Dangote.
Tsorata masu son saka hannun jari
Wannan abu da ya faru tsakanin hukumar NMPDRA da mutumin da ya fi kowane mutum kuɗi a Afirka ka iya jefa tsoro a zukatan duk wani son saka hannun jari a fanni mai da iskar gas a Najeriya.
Fargabar ka iya samuwa saboda ganin abin da ya faru da mutumin da ƴan Najeriya ke ganin ya fi ƙarfin kowa ko kuma zai samu rangwame a hannun hukumomi.
Lokacin da Dangote ya bayyana aniyarsa na kafa wannan matata dai, yana ɗaya daga cikin albishir da masana suka rinƙa shaida wa ƴan Najeriya cewa ƙarshen rashawa da cin hanci a harkar makamashi a Najeriya ya zo.
To sai dai kuma ganin abin da ya faru ga mai kuɗin na Afirka ka iya saka shakku a zukatan ƴan Najeriya da ke da tunanin zuba jari kamar na Aliko Dangote.

Asalin hoton, NMPDRA
A nasa martanin, shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed, ya ce yana maraba da binciken da hukumar ICPC za ta gudanar a kansa.
Ya ce ya yi imanin cewa binciken zai ba da dama a duba lamarin cikin adalci da natsuwa, tare da fayyace gaskiyar al'amura domin wanke sunansa.
Ahmed Farouk ya ƙara da cewa ba zai yi musayar zarge-zarge a bainar jama'a ba yana mai cewa zai bari binciken hukuma ya yi aikinsa yadda ya kamata.










