Ƴan wasa shida da za su haska a gasar cin kofin Afirka ta 2025

Mohamed Amoura and Victor Osimhen are established players for Algeria and Nigeria, while Ibrahim Mbaye is the new man on the scene for Senegal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mohamed Amoura da Victor Osimhen garnannun yan wasa ne na tawagar Algeria da Najeriya yayin da shi kuma Mbaye sabon zuwa ne a Senegal
Lokacin karatu: Minti 5

Za a fara gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Afirka karo na 35 a Moroko a ranar 21 ga watan Disamban 2025, kuma za a buga wasan karshe ne ranar 18 ga watan Janairun 2026.

Mai masaukin za ta so ta dauki kofin karo na farko tun 1976, yayin da shi kuma Mohammed Salah zai so manta da abin da ke faruwa a Liverpool ta hanyar taimaka wa kasarsa Masar ta lashe kofin tun bayan hakan da ta yi a 2010.

Daga cikin sunayen ‘yan wasan da ake hasashen za su taka rawar gani, BBC ta tattaro wadanda ake ganin taurarinsu za su fi haskawa a lokacin gasar.

Azzedine Ounahi (dan wasan tsakiya, Moroko)

Azzedine Ounahi,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Azzedine Ounahi a yanzu na tare ne da kungiyar Girona da ke Spain bayan kwashe kakar da ta gabata a kungiyar Pananthinaikos a matsayin aro

Dan wasan Real Madrid dan asalin Moroko Brahim Diaz shi ne ya fi jefa kwallaye a wasan neman gurbi, to amma Azzesina Ounahi, wanda shi ne ke kokari wajen raba kwallo a tsakiyar tawagar Atlas Lions shi ne dan wasan da ‘yan Moroko za su so su ga yana taka rawar gani.

Matashin wanda ya samu horo a shahararriyar cibiyar horas da yan wasa ta Sarki Mohammed VI, Ounahi ya daure zaman takaici a kungiyar Marseille bayan tafiya kungiyar sanadiyyar rawar gani da ya taka a gasar kofin duniya ta 2022.

Sai dai bayan komawar dan shekara 25 din zuwa kungiyar Girona a Spain cikin watan Agusta, ya gano bakin zaren.

Moroko, wadda za ta kara da kasashen Comoros da Mali da kuma Zambia a rukunin A, suna kuma da kwararrun 'yan wasa a fagen tamaula, kamar mai tsaron raga Yassine Bonou da dan wasan gaba Youssed En-Nesyri.

Mohamed Amoura (dan wasan gaba, Algeria)

Maxamed Amoura

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dan wasn Wolfsburg Mohamed Amoura ya ci kwallo 10 wa kasarsa wadda ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya

Dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya Amoura ya haskaka sosai a 2025.

Dan wasan gaban na Wolfsburg ya jefa kwallo 11 wa kasarsa cikin wasa takwas tun daga watan Maris, ciki har da kwallo uku rigis da ya zura a ragar Mozambique.

Wannan bajinta da ya yi ta sa ya zama zabi farko a tawagar kasarsa.

Duk da cewa Riyad Mahrez ne ginshiki a tawagar, to amma Amoura ya gina kansa a cikin tawagar.

Dole ne kasashen Sudan da Butkina Faso da kuma Equatorial Guinea da suke tare a rukunin E su yi taka-tsantsan da shi.

Victor Osimhem (dan wasan gaba, Nigeria)

Victor Osimhen, oo xiran shaarka cayaartoyda xulka Nigeria

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Victor Osimhen ya taimaka wa Najeriya a wasanninta na neman gurbin gasar cin kofin duniya sai dai DR Congo ce ta cire su

Nasarar Najeriya kusan za a ce ta ta’allaka ne ga rawar da wannan matashin da ke wasa a kungiyar Galatasaray ke takawa.

Super Eagles ta samu maki 4 ne kacal a cikin 15 da za ta iya samu lokacin da dan wasan mai shekara 26 ba ya nan, a wasannin neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya.

Osimehn na cikin ginshikan kungiyar a karkashin mai horaswa Eric Chelle, kuma Nakeriya ta kasa lashe wasanta na neman cike gurbi da DR Congo, lokacin da aka cire shi a hutun rabin lokaci.

Rawar da Osimhen zai taka za ta taimaka matukar kasar na son ta matsa gaba daga matsayi na biyu da ta samu a gasar da aka buga a Ivory Coast.

Najeriya, wadda ta lashe kofin sau uku za ta kara ne da kasashen Tanzania da Uganda da kuma Tunisia a rukunin C.

Ibrahim Mbaye (dan wasan gaba, Senegal)

Ibrahim Mbaye oo sita shaarka nambar 17 ee Senegal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ibrahim Mbaye, 17, ya fara buga wa Senagal wasa ne a watan da ya gabata a karawarta da Brazil

Sadio Mane ne ginshikin kasar a gasar Afcon ta 2021, yayin da Iliman Ndiaye da Ismaila Sarr suke taka rawar gani a gasar Premier, lamarin da ya sa aka samu 'yan wasan gaba uku gogaggu.

Tsohon dan wasan tawagar matasa ta kasar Faransa, ya samu shiga tawagar manya ta kungiyar PSG a wannan kaka, inda ya fara a wasan da kungiyarsa ta doke Barcelona a farkon kaka

Mbaye ya fara buga wa Senegal wasa ne a watan da ya gabata a karawarsu da Brazil, sannan ‘yan kwanaki bayan ya zama dan wasa mafi karancin shekaru a kungiyarsa,inda yana da shekra 17.

Rogers Mato (dan wasan gaba, Uganda)

Rogers Mato, oo wata shaarka Uganda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rogers Mato (hagu)

Uganda ta dawo Afcon tun daga shekara 2019 lokacin da aka fitar da sa a zagayen ‘yan 16, yanzu kuma suna hankoron kaiwa wasan karshe a wannan gasa.

Kungiyar da ke karkashin jagorancin Paul Put dun kammala a mataki na biyu a rukuninsu na wasannin neman gurbin gasar cin kofin duniya, a bayan Algeria.

Uganda za ta fuskanci jarrabawa a rukunin C inda za ta kara da kasashe kamar Najeriya da Tunisia.

Reinildo (mai tsaron baya, Mozambique)

Reinildo, wearing a red and white vertical striped Sunderland shirt, visible from waist up running during a football match with big droplets of rain falling around him

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Reinildo ya zama dan wasan Mozambique na farko da ya buga gasar Premier bayan komawa kungiyar Sunderland

Mozambique za ta isa Moroko a matsayin kasar da ba ta taba zuwa zagayen kifa daya kwala ba a karo biyar da ta halarci gasar Afcon.

Sai dai a karon farko tana alfahari da kasancewar daya daga cikin 'yan wasan gasar Premier a tawagarsu, bayan da Reinildo ya zamo dan kasar Mozambique na farko da ya taka wasa a gasar Premier bayan ya koma kungiyar Sunderland daga Atletico Madrid a watan Yuli.

Wanda ke wasa ta bangaren hahu, dan wasan mai shekara 31 ya taimaka wa kungiyarsa wajen yin ba-zata