Me ya sa Trump ya haramta wa wasu ƴan Najeriya da ɗaukacin ƴan Nijar shiga Amurka?

Shugaban Amurka Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump
Lokacin karatu: Minti 5

A daidai lokacin da ake ci gaba da tafka muhawara kan zargin ana cin zarafi ko kuma yi wa Kiristocin Najeriya kisan kiyashi, musamman a arewacin ƙasar, gwamnatin Amurka ta ɗauki matakin hana wasu ƴan Najeriyar shiga ƙasarta.

Wata sanarwa da fadar gwamnatin Amurka ta fitar a ranar Talata ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da za a taƙaita wa mutanenta shiga Amurka.

Wannan na cikin matakin da ƙasar ta Amurka ta ɗauka wajen hana al'umma daga ƙasashe da dama shiga cikinta bisa dalilai daban-daban.

A kwanakin baya Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar shiga Najeriya da sojoji, inda ya ce zai je ne domin yaƙi da ta'addanci matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta ɗauki matakin gaggawa ba.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta zargin, inda ta bayyana cewa tabbas tana fama da matsalolin tsaro, amma kashe-kashe da garkuwa da mutane da ake yi a ƙasar ba su da alaƙa da addini ko ƙabila.

Ko waɗanne dalilai Amurkar ta dogara da su wajen taƙaita shigar ƴan Najeriya cikin ƙasarta?

Boko Haram: A sanarwar da gwamnatin Amurka ta fitar, ta ce masu tsattsauran ra'ayin addini kamar Boko Haram da tsagin ISWAP suna gudanar da hare-hare a wasu sassan Najeriya yadda suke so.

Zaman wuce wa'adin biza: Sanarwar ta ƙara da cewa akwai waɗanda suke shiga ƙasar da bizar ɗan ƙanƙanin lokaci, amma sai su ci gaba da zama bayan wa'adin ya ƙare. Ta ce masu na'ukan bizar B-1/B-2 kusan kashi 5.56 ne suke zaune a ƙasar duk da bizarsu ta ƙare, sannan masu na'ukan bizar F da M da J kusan kashi 11.90 ne suke zaune ba bisa ƙa'ida ba.

Matsalar tantancewa: A wani ɓangaren kuma, fadar gwamnati Amurka ta ce matsalolin tsaron, suna kawo tsaiko wajen tantance ƴan ƙasar, lamarin da bai rasa nasaba da gane baƙin haure da masu zuwa wani aikin daban.

Don haka ne gwamnatin ta ce za ta taƙaita bayar da biza ga ƴan Najeriya masu kwarara ƙasar domin samun mafaka wato baƙin haure da ma waɗanda suke zuwa ƙasar domin wasu ayyukan daban bisa ƙa'ida.

Su wane ne abin ya shafa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sanarwar gwamnatin Amurkar ta kasafta mutanen da aka haramta wa shiga ƙasar bisa nau'in bizar da ake ba su.

Amurka ta kasa masu shiga ƙasarta zuwa manyan gidaje biyu:

  • Masu shiga na wucin-gadi
  • Masu ƙaura

- Masu shiga na wucin-gadi sun hada da ƴan yawon shaƙatawa, da ɗalibai da masu aikin wucin-gadi da kuma masu zuwa domin kasuwanci.

- Masu ƙaura kuma su ne wadanda ke neman komawa Amurka da zama, wadanda suka hada da iyali da masu aiki na dindindin.

An karkasa wadannan zuwa nau'ukan biza daban-daban.

Nau'ukan bizar da haramta shiga Amurkar ta shafe su daga Najeriya su ne:

B-1: Bizar B-1 bizar shiga Amurka ce ta wucin-gadi da ake ba ƴan kasuwa ko kuma wani aikin da ke nuna ƙwarewa kamar harkar ilimi da kimiyya ko kwantiragi ko neman horaswa, ko kuma wanda zai ratsa ta Amurka. Biza ce ta wata 1 zuwa wata shida, amma za a iya tsawaitawa zuwa shekara 1.

B‑2: Ita ma kusan irin B-1 ce, amma domin masu zuwa hutu ko ziyarar ƴan'uwa da abokan arziki da asibiti, kuma wa'adin kusan iri ɗaya ne.

F biza: F-1 ita ce bizar ɗalibai da za su je ƙasar domin karatu a kwaleji da jami'ai ko sakandare, amma za su iya zama a ƙasar na kwana 30 kafin fara karatu da zuwa kwana 60 bayan kammala karatu.

M-1: Irin bizar F-1 ce, amma a wannan an haɗa da ɗaliban da za su je karatun sana'ar hannu kuma suma za su iya zama kwana 30 kafin fara karatu da kwana 30 bayan kammala karatu.

J - Biza ce ta musamman da ake bai wa masu zuwa Amurka domin koyarwa ko bincike ko nazari ko wani karatu na musamman a ɓangaren lafiya da ilimi wanda shi ya sa ake kiransa 'exchange visitor'. Yawanci ana bayar da bizar ne daidai da wa'adin aikin da mutum ya je yi, idan an tsawaita aikin, shi ma za a tsawaita zamansa, sannan za su iya zama na kwana 30 kafin fara aikin da kwana 30 bayan kammalawa.

Haramcin shiga Amurka ga dukkanin baƙi daga Nijar

A ɓangaren Jamhuriyar Nijar kuwa, gwamnatin Amurka ta ce ta gano cewa, "ƴan ta'adda da masu goya musu baya na garkuwa da mutane sosai a Nijar, kuma za su iya kai hari a duk inda suke so a ƙasar.

Ta ce alƙaluma sun nuna cewa waɗanda suka wuce ƙa'idar bizarsu a na'ukan bizar B-1/B-2 sun kai kashi 13.41, sannan a na'ukan F,M da J kuma sun kai kashi 16.46.

Don haka ne gwamnatin Amurka ta ce ta dakatar da bayar da biza ga baƙin haure da waɗanda suke zuwa wani aikin daban baki ɗayansu.

Ƙasashen da aka haramta wa ƴan ƙasarsu shiga Amurka

Afghanistan

Burkina Faso

Burma

Chad

Equatorial Guinea

Eritrea

Haiti

Iran

Laos

Libya

Mali

Nijar

Congo

Saliyo

Somalia

Sudan ta Kudu

Sudan

Syria

Yemen

Waɗanda gwamnatin Falasɗinu ta ba izinin tafiya.

Ƙasashen da aka haramta wa wani ɓangare

Angola

Antigua da Barbuda

Benin

Burundi

Côte d'Ivoire

Cuba

Dominica

Gabon

Gambia

Malawi

Mauritania

Najeriya

Senegal

Tanzania

Togo

Tonga

Venezuela

Zambia

Zimbabwe

Dakatarwa ta uku

Wannan ne karo na uku da Trump ke ayyana dokar dakatarwa ko taƙaita shiga Amurka ga wasu ƙasashen na duniya.

A zangon mulkinsa na farko, ya ayyana a shekarar 2017 ce zai dakatar da ƴan wasu ƙasashn zuwa ƙasarsa, lamarin da ya tayar da ƙura da zanga-zangar, inda aka kai shi ƙara kotu, har zuwa kotun ƙoli, wadda ta tabbatar da buƙatarsa.

A lokacin ne fadar gwamnatin Amurka ta ce dakatarwar za ta ci gaba da aiki ne zuwa lokacin da za a samu abin da ta bayyana da "cigaba" a ƙasashen, musamman a ɓangaren ƙididdige ƴan ƙasa da ba gwamnatin Amurka haɗin kai wajen kula da kwararar baƙin haure.

A watan Yuli, Trump ya ayyana dakatar da ƴan ƙasashe 12 da zuwa ƙasar, sannan ya taƙaita ziyarar wasu ƴan ƙasashen guda bakwai, sai kuma wannan sabuwar dokar da ya sanya wa hannu.

A sanarwar da fadar gwamnatin Amurka ta fitar, ta ce Trump ya sanya hannu a dokar, "domin faɗaɗawa da kuma ƙarfafa dakatarwar da aka yi wa wasu ƴan ƙasashe shiga Amurka musamman daga ƙasashen da suke fuskantar tsaiko wajen tantance bayanan ƴan ƙasarta da rashin ba Amurka haɗin kai wajen daƙile kwararar baƙin haure."