Abin da tawagar Najeriya ta shaida wa Amurka kan zargin kisan Kiritoci

Asalin hoton, Presidency
Wakilan Najeriya da Amurka sun gana domin tattauna yadda ƙasashen biyu za su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tabbatar da tsaron ƴan Najeriya.
Gwamnatin Najeriya ta tura wakilai zuwa Amurka ne domin ganawa da hukumomin Amurka domin lalubo hanyoyin da za a bi domin magance matsalar, wadda ta daɗe tana addabar ƴan ƙasar.
Wannan na zuwa ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar aika sojojin zuwa Najeriya bayan ya bayyana ƙasar a "matsayin ƙasar da yake sa ido' sannan kuma ya yi barazanar 'shiga domin fatattakar' ƴan ta'adda.
Haka kuma Trump ya yi barazanar dakatar da dukkan tallafin da yake bai wa Najeriya.
A wata sanarwa da ya fitar, ya ce, "na umarci sashen yaƙi na Amurka da ya fara shirin ɗaukar mataki. Idan za mu kai hari ne, to za mu kai ne da zafi-zafi kamar yadda ƴan ta'addan suke kai hari kan kiristocin da muke matuƙar ƙauna," in ji shi, sannan ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakin gaggawa.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta sha nanata cewa babu batun kisan kiyashi a Najeriya, inda ta nanata cewa matsalar tsaron ƙasar na shafar Musulmi da Kirista ne baki ɗaya.
Daga cikin abubuwan da Najeriya ta nema akwai buƙatar a taimaka mata da kayan yaƙi da sauran abubuwan da ake buƙata domin ta kawo ƙarshen matsalar.
A makon da ya gabata, Najeriya ta fuskanci hare-haren masu zafi da suka ɗaga hankalin ƙasar.
Ƴanbindiga sun kai hari a makarantar sakandiren mata da ke garin Maga a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi, inda suka yi garkuwa da ɗalibai.
Haka kuma ƴanbindiga sun kai wani harin a Cocin Christ Apostolic da ke Oke Isegun a ƙaramar hukumar Ekiti da ke jihar Kwara, inda suka kwashe masu ibada.
A wani ɓangaren kuma an kai hari a makarantar St Marys's da ke jihar Neja, inda suka yi garkuwa da ɗalibai 315 da malamai.
Sace-sacen ɗaliban sun zo ne a daidai lokacin da ake jimami bayan shugaban ƙasar ya tabbatar da kashe Birgediya Janar Musa Uba bayan maharan sun musu kwanton ɓauna.
Waɗannan matsalolin duk sun faru a tsakankanin mako ɗaya.
Su wane ne a cikin tawagar?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tawagar ta Najeriya ta gana da ɗanmajalisar Amurka Riley Moore, wanda ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda Trump ya naɗa domin su riƙa sa ido kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya.
A ganawarsu ce wakilan Najeriya suka bayyana masa matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta da yadda suke shafar ƙasar da ƴan ƙasar baki ɗaya.
"A ganawarmu, wakilan Najeriya sun bayyana mana matsalolin da suke fuskanta wajen yaƙi da masu tada ƙayar baya da sauran matsalolin da suke fama da su ciki har da rashin isassun kayan aiki," in ji Riley.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce tawagar ta Najeriya ta isa Amurka ne a ƙarƙashin jagorancin mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, kuma sun gana ne da manyan jami'an gwamnatin Amurka ciki har da ƴan majalisa da ofishin kula da addinai na fadar gwamnatin Amurka da ma'aikatar harkokin waje da majalisar tsaron ƙasar da sashen yaƙin ƙasar.
Tawagar Najeriya ta ƙunshi:
- Mallam Nuhu Ribadu – Mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro
- Bianca Ojukwu - Karamar ministar harkokin waje
- Kayode Egbetokun - Babban sufeto janar na ƴansanda
- Lateef Olasunkami Fagbemi, SAN - Ministan shari'a
- Janar Olufemi Oluyede - Babban hafsan tsaro
- Laftanar janar Emmanuel Undiandeye - Babban hafsan tattara bayanan sirri
- Ms. Idayat Hassan - Hadima a a ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro
- Ambasada Ibrahim Babani - Daraktan harkokin waje a ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro
Abubuwan da suka tattauna
Shugaban Amurka Trump dai ya yi barazanar ɗaukar matakin soji a Najeriya ne idan gwamnatin ƙasar ta bari aka ci gaba da kashe Kiristoci a ƙasar.
Sai dai Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ya ce Trump bai fahimci haƙiƙanin abubuwan da ke faruwa a Najeriya ba game da yanayin matsalolin tsaron.
Hakan ya sa Najeriya ta yi amfani da damar ganawar domin musanta zargin kisan kiyashi a ƙasar.
"A ganawar da wakilan Najeriya ta yi da hukumomin Amurka, sun musanta dukkan zarge-zargen kisan kiyashi a ƙasar, inda suka nanata cewa kashe-kashen suna shafar dukkan addinai da dukkan ƙabilu ne ba tare da bambanci ba.
"Haka kuma wakilan sun musanta yadda ake bayyana matsalolin tsaron ƙasar, inda suka ce hakan zai ƙara raba kan ƴan ƙasar ne maimakon kawo gyara."
A cewar Onanuga, gwamnatin Amurka ta bayyana amincewarta ta yin aiki tare da Najeriya ta hanyar bayar da gudunmuwar makamai da ɓangaren tattara bayanan sirri.
Haka kuma ya ce gwamnatin Amurka ta bayyana shirinta na bayar da gudunmuwa "ga mutanen da matsalolin tsaro suka illata."
"Sannan kuma ƙasashen biyu sun amince da haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen fitar da tsari na bai-ɗaya da za a yi amfani da shi wajen fuskantar lamarin," in ji Bayo Onanuga a sanarwar da ya fitar.






