Wane zaɓi ya rage wa gwamnoni bayan kotun ƙoli ta bai wa Tinubu ikon tuɓe su?

Shugaba Tinubu ya ƙaƙaba dokar ta-ɓaci ta watanni shida a jihar River a watan Maris

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Tun bayan da kotun ƙoli ta bai wa shugaban Najeriya, Bola Tinubu ƙarfin ayyana dokar ta-ɓaci a kan jihohi da ma ikon tuɓe zaɓaɓɓen gwamna da ƴanmajalisa, ƴan Najeriya ke ta bayyana ɗarɗar dangane da ƴancin zaɓaɓɓun shugabanni a jihohi.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Kotun Ƙolin Najeriyar ta yanke hukunci cewa shugaban ƙasa na da ikon dakatar da zaɓaɓɓen jami'in gwamnati a lokacin da aka ayyana dokar ta-ɓaci a wata jiha.

Kwamitin alƙalai bakwai ne dai suka yanke hukuncin, inda shida daga ciki suka amince da matsayar kotun, yayin da alƙali guda ɗaya ya bayar da ra'ayi na daban.

Wannan hukunci ya zo kusan watanni uku bayan an kawo ƙarshen dokar ta-ɓaci a jihar Rivers tare da mayar da gwamnan da majalisar jihar kan mukamansu.

Me ya haifar da hukuncin a yanzu?

Ƙarar dai ta fito ne daga gwamnatin jihar Adamawa tare da wasu jihohi guda goma da gwamnoninsu ke ƙarƙashin jam'iyyar PDP suka shigar,

Jihohin sun ƙalubalanci matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers a watan Maris na wannan shekara, tare da dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da dukkan 'yan majalisar jihar na tsawon watanni shida.

Masu ƙarar sun bayar da hujjar cewa kundin tsarin mulki bai ba wa shugaban ƙasa ikon dakatar da jami'an da aka zaɓa da ke kan mulki ba.

Sai dai, a hukuncin da Alƙali Mohammed Idris ya karanta, Kotun ta bayyana cewa Sashe na 305 na ƙundin tsarin mulki ya bai wa Shugaba damar ɗaukar "matakan gaggawa" domin dawo da zaman lafiya da daidaito a duk inda aka ayyana dokar ta ɓaci.

Kotun ta ce tunda ƙundin tsarin mulkin bai fayyace irin matakan gaggawar da za a ɗauka ba, hakan na bai wa shugaba damar amfani da fahimtarsa wajen yanke hukunci kan matakin da ya dace.

Duk da haka, alƙali ɗaya daga cikin kwamitin ya yi fatali da wannan matsaya, inda ya ce ko da yake Shugaba na da ikon ayyana dokar ta ɓaci, bai kamata ya yi amfani da ikon wajen dakatar da jami'an da aka zaɓa ba kuma ke kan mulki kamar gwamna da 'yan majalisa ba.

Tasirin hukuncin

Dakta Kabiru Sufi wanda malami ne a kwalejin share fagen shiga jami'a da ke Kano, CAS kuma masanin kimiyyar siyasa ya shaida wa BBC cewa hukunci ne daga kotun ƙoli sannan ba yanzu dokar ta fara ba.

"Wannan doka ta faro ne tun lokacin shugaba Obasanjo lokacin da ya sanya dokar taɓaci a jihar Plateau abin ya janyo cece-kuce kuma haka ake yawan samu a duk lokacin da aka sanya dokar - dacewar dokar ko akasin haka," in ji dakta Kabiru Sufi.

Sai dai kuma masanin ya ce hukuncin zai yi tasiri ga gwamnoni ta fuska biyu:

  • Ɗari-ɗari: Hukuncin sai sa gwamnoni da ma duk zaɓaɓɓu yin ɗari-ɗari da shugaban ƙasa. Za su zama tamkar ƴan amshin shata saboda tsoron ka da su saɓa wa shugaban ƙasa ko da kuwa abin daidai ne.
  • Biyayya ga shugaban ƙasa fiye da ƙima: Hukuncin zai sa zaɓaɓɓnun shugabanni yin biyayya da rige-rigen nuna goyon baya ga shugaban ƙasa domin gudun ka da ayyana jihohinsu a matsayin masu dokar ta-ɓaci.

Wane zaɓi ya rage wa gwamnoni da ƴan majalisa?

Dakta Kabiru Sufi ya ce zaɓin da ya rage wa gwamnoni da ƴan majalisa shi ne su koma su nemi a yi gyaran kundin mulkin da ya bai wa shugaban ƙarfin iko.

"Su yi ƙoƙarin komawa baya domin gyaran tsarin mulki saboda su tabbatar da ikonsu da ƴancin kan da suke da su. Sannan kuma su yi amfani da ƴan ƙasa da ƙungiyoyi wajen tabbatar da kare musu ƴancin cin gashin kansu (a matsayinsu na zaɓaɓɓu)."

A Maris ɗin 2025 ɗin nan ne shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar River ta tsawon watanni shida, inda aka tuɓe gwamnan da ƴan majalisunsa aka kuma maye gurbinsu da gwamnan riƙon ƙwarya wanda shi kuma ya naɗa waɗanda zai yi aiki da su.

Kuma ayyana dokar ta-ɓacin a jihar River shi ne karo na biyar da wani shugaban ƙasa ke ayyana dokar a kan wata jiha a Najeriya.