Da me Ɗangote ya dogara a zarge-zarge kan Farouk Ahmad na NMPDRA?

Haɗakar hoton Aliko Dangote da Ahmed Farouk duka a baƙaƙen kwat.

Asalin hoton, Getty Images/NMDPRA website

Lokacin karatu: Minti 4

A karo na biyu shugaban rukunin kamfanin Aliko Dangote ya fito fili ya yi zargi shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da kuma sufurin man fetur a Najeriya, NMDPR.

Attajirin mafi kuɗi a Afirka ya zargi Farouk Ahmed cewa yana biya wa yaransa guda huɗu kuɗin makarantar da ya kai dalar Amurka miliyan 5 a wata sakandire a Switzerland.

Ɗangote ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya kira a birnin Legas ya ce bai ga ta hanyar da Farouk wanda ma'aikacin gwamnati ne zai iya samun waɗannan kuɗin da har zai biya wa yaransa kuɗin makaranta ba a ƙasar waje.

"Ya kamata shi Farouk ya zo ya bayar da bahasi dangane da abin da ya yi ya kuma tabbatar bai yi abin da zai jefa ƴan Najeriya cikin ƙangin wahala ba, abin da ka iya zama yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa," in ji Ɗangote.

" Ya kamata Hukumar Ɗa'ar Ma'aikata ta Najeriya ko kuma duk wata hukuma da ke da ruwa da tsaki kan wannan batu da ta binciki al'amarin. Idan ya ƙi amincewa da zargin to ba wai kawai zan wallafa kuɗin makarantar da yake biya ba, zan kai makarantun kotu domin a matsa musu sao sun bayyana abin da shi Farouk yake biyan su."

Wane martani Farouk Ahmad ya mayar?

Wannan dai ba ƙaramin zargi ba ne da Ɗangoten ya yi wa shugaban hukumar ta NMDPR wani abun da ƴan Najeriya ke yi wa kallo sabon al'amari daga wurin mutumin da ba a cika jin ƙorafi daga bakinsa ba.

Yayin wannan zargin ne a daida lokacin da yake magana cewa har yanzu ana shigar da ɗanyen man fetur Najeriya duk da cewa Najeriya na da ƙarfin tace ɗanyen man da kuma sarrafa shi da dangoginsa domin wadatar da ƙasar da ma sauran ƙasashen Afirka ta yamma, kamar yadda ya yi iƙrari.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Harkar man fetur a Najeriya cike take da son rai. Abin yana da ban takaici a ce wao ƙasar Afirka na ci gaba da shigar da ɗanyen man fetur duk kuwa da cewa ana ta kiraye-kirayen cewa ya kamata a inganta wanda ake da shi a gida. Irin man da ake shigarwa da shi cikin ƙasar bai kamata ba kuma ba zai taimakI Najeriya ba, in ji Ɗangote.

BBC ta yi ƙoƙarin tuntuɓar George Ene-Ita wadda shi ne mai magana da yawun NMDPRA, dangane da zarge-zargen to amma ya ce ba shi da abin faɗi.

Hukumar ta NMDPRA dai ita ma a baya-bayan nan ta zargi matatar Ɗangoten cewa tana son kankane harkar man fetur a Najeriya, inda ta ce man da matatar ke samarwa bai wadatar da buƙatun Najeriya ba.

Najeriya dai ita ce ƙasa mafi yawan albarkatun man fetur a Afirka inda ƙasar ke fitar da ɗanyen mai domin tacewa a waje sannan kuma ta shigar da tataccen zuwa cikinta.

To sai dai kuma matatar da Ɗangote na da ƙarfi tace gangar ɗanyen mai 650,000 a kullum, sannan an yi matatar ne da manufar tace mai a cikin gida kuma a sayar da kuɗin ƙasar wato Naira wadda masana ke cewa hakan zai rage yawan dogaro a kan kuɗin ƙasashen waje.

Me ya sa Ɗangote yin wannan zargi?

Alhaji Bashir Danmalam mai sharhi ne kan harkokin man fetur da dangoginsa sannan kuma mai kamfanin mai ya ce ba wani abu ba ne ya saka Ɗangote yin waɗannan zarge-zarge illa ƙoƙarin mayar da martani ga hukumar NMPDRA.

"Shi Ɗangote bai kamata ya yi haka ba saboda kawai hukumar da ke da alhakin sa ido a harkokinka ta faɗa maka gaskiya. Kawai fa saboda NMPDRA ta ce matatar Ɗangote ba ta iya wadatar da Najeriya man da ƙasar ke buƙata shi ne ake ta wannan abu," in ji Alh Bashir Danmalam.

Sai dai kuma Alh Bashir ya ce ya kamata waɗanda za su iya shiga tsakanin Ɗangote da ita NMPDRA.

"Muna da ministan mai da shugaban kamfanin NNPC da sauran masu ruwa da tsaki. Ya kamata su shiga tsakani su faɗa wa mutanen gaskiya. Amma kuma shi Ɗangote ya kamata ya fahimci cewa fa ita wannan hukumar ita ce da alhakin sa ido a matatarsa. Idan yana faɗa da shugabanninta to lallai zai ci gaba da fuskantar matsala.

Mene ne aikin hukumar NMDPRA?

hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da kuma sufurin man fetur a Najeriya, NMDPR ta fara aiki ne a watan Agustan 2021, a ƙarƙashin dokar harkokin man fetur ta ƙasa, PIA.

NMPDRA ta samu ne bayan haɗe hukumomin gwamnati masu saka ido kan harkokin fetur guda uku wuri guda.

Ayyukan hukumar sun haɗa da:

  • Kyautata tsarin gasa da kuma saka hannun jari a harkar albarkatun man fetur.
  • Tantance tsarin biyan haraji.
  • Gindaya tsarin yadda za a gudanar da ayyukan harkokin man fetur.
  • Bai wa gwamnati da masu ruwa da tsaki shawara dangane da batutuwan da suka jiɓanci haraji da fitar da farashi.
  • Sama wa abokan hulɗa matakan kariya
  • Sa ido kan iya yawan man da za a iya adanawa da za a raba da tallatawa da tura mai da dangoginsa ta bututu
  • Sanya ido da kuma tabbatar da an bi dokokin lasisi da shaidar yin aiki daga hukumar

Wane ne Farouk Ahmad?

Farouk Ahmad sanye da kwat.

Asalin hoton, NMPDRA/WEBSITE

Shi ne shugaban farko na hukumar mai kula da harkokin sarrafawa da tacewa da kuma sufurin man fetur a Najeriya, NMDPRA, inda ya fara jagorantar ta a 2021.

Kafin nan yana ɗaya daga cikin manyan shugabannin hukumar da ke tallata hajar albarkatun man fetur ta Najeriya wato PPMC.

Farouk Ahmad ya yi aiki da kamfanin mai na Najeriya, NNPC.

Farouk ya yi digirinsa a fannin injiniya a jami'ar Southern Illinois University, da ke Carbondale, Amurka.

Ya kwashe shekaru fiye da 35 yana aiki a fannin man fetur da dangoginsa.