Hanyoyi biyar da Najeriya za ta iya bi don karɓo sojojinta daga Burkina Faso

Jirgin sojan Najeriya C-130H

Asalin hoton, Nigerian Airforce

Bayanan hoto, Najeriya ta ce jirgin sojanta ƙirar C-130 ya yi saukar gaggawa ne ɗauke da mutum 11 saboda matsalar na'ura
    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Kimanin mako daya kenan da Burkina Faso ta tsare dakarun sojan Najeriya 11 bayan jirginsu ƙirar C-130 ya yi saukar gaggawa a ƙasar sakamakon matsalar da ya samu.

A ranar Litinin ta makon jiya ne ƙungiyar Association of Sahel States (AES) - wadda ta ƙunshi Burkina da Nijar da Mali - ta yi tir da abin da ta kira keta musu sararin samaniya da jirgin sojin Najeriya ya yi ba bisa ƙ'aida ba.

Har yanzu hukumomin AES na ci gaba da tsare dakarun sojan, waɗanda suka ƙunshi soja tara da ma'aikatan jirgi biyu, yayin da suka ce suna ci gaba da bincike kafin ɗaukar mataki na gaba.

"Muna ƙoƙarin kammala bincike game da abin da ya faru kafin mu ɗauki mataki na gaba," kamar yadda Daoud Aly Mohammedine, ministan tsaro na ƙasar Mali, ya shaida wa BBC ranar Juma'a.

"Mun saka wa makaman tsare sararin samaniyarmu na ƙasashen AES ƙaimi. Yanzu mun tsara su ta yadda za su harbe duk wani jirgi da ya keta alfarmar sararin samaniyarmu."

Zuwa yanzu Najeriya ba ta bayyana salon yunƙurin da take yi na karɓo sojojin nata ba, amma masana shari'a sun bayyana hanyoyin da za ta iya yin hakan.

Sai dai alaƙa tsakanin Najeriya da Burkina Faso ta lalace tun lokacin da sojoji suka ƙwace mulki a Burkina, musamman bayan kafa ƙungiyar AES wanda ya jawo ficewar Nijar da Mali da Burkina daga ƙungiyar Ecowas mai raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma.

Difilomasiyya ta hannun Ecowas

Ɗaya daga cikin hanyoyin da Najeriya za ta iya amfani da su wajen 'yanto dakarun nata ita ce ta hannun ƙungiyar Economic Community of West African States (Ecowas).

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An kafa Ecowas ne da zimmar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma, kuma Najeriya ce mafi girman tattalin arziki da al'umma a ƙungiyar mai mambobi 12, bayan Nijar da Mali da Burkina Faso sun fita a 2024.

Masanin shari'a kuma mai bincike kan ayyukan 'yanbindiga a yankin Sahel, mazaunin Birtaniya, Audu Bulama Bukarti ya shaida wa BBC cewa yana ganin amfani da Ecowas zai bai wa Najeriya damar saka bakin duka ƙasashen ƙungiyar.

"Idan Najeriya ta yi hakan zai zama ba ita kaɗai take matsa lamba ga Burkina Faso ba, duka ƙasashen Ecowas ne ke neman mafita," in ji shi.

"Amma dole ne sai Najeriya ta nemi hakan a hukumance, wanda zai iya kaiwa ga taron gaggawa na Ecowas domin naɗa wani manzo na musamman."

Sai dai masanin na ganin saka bakin Ecowas na da ɗan haɗari idan aka yi la'akari da yadda ƙasashen AES ke nuna ƙiyayya ga ƙungiyar.

"Mun san cewa ƙasashen AES na ci gaba da maganganu na ƙiyayya kan Ecowas, kuma shigar Ecowas maganar zai iya jawowa Burkina ta ƙi tattauna matsalar gaba ɗaya."

Tsakanin Tinubu da Traore

Sanannen abu ne a hulɗar ƙasashen duniya cewa duk lokacin da aka samu matsala shugabannin ƙasashe kan tuntuɓi juna kai-tsaye domin warware ta.

A wannan karon, Bukarti na ganin hanyar da ta fi kowacce sauƙi ita ce wadda Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai tuntuɓi takwaransa na Burkina Kyaftin Ibrahim Traore.

"Ya kamata [Tinubu] ya tuntuɓe shi [Traore], su tattauna kuma ya ci gaba da yin hakan har a samu a fita daga cikin matsalar nan," a cewar Bukarti.

Ya ƙara da cewa Najeriya za ta iya amfani da wata ƙasa ta daban domin ta shiga tsakani saboda rashin kyawun alaƙa tsakaninta da Burkina.

"Idan aka samu ƙasashe kamar Ghana, ko Aljeriya, ko Togo, ko Rwanda, waɗanda aka san ƙawayen Burkina ne."

Matakin Afirka ko na duniya

Haka nan, Najeriya na da zaɓin kai koke ƙungiyar Tarayyar Afirka ta African Union (AU), ko kuma ma Kwamatin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

Ƙungiyar AU na da hukumar da ke kula da sufurin jiragen sama mai suna African Civil Aviation Commission (AFCAC), wadda za ta iya shiga maganar domin samar da mafita.

Kwamitin Tsaro na MDD kuwa, muhimmi daga cikin aikinsa shi ne ɗaukar mataki kan rikici tsakanin ƙasashen duniya, kamar yadda aka gani tsakanin Lebanon da Isra'ila, da kuma tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewa.

Matakin shari'a

A gefe guda kuma, Najeriya na da zaɓin kai Burkina Faso Kotun Duniya ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya.

Najeriya za ta iya shigar da ƙara a International Court of Justice (ICJ), wadda aikinta shi ne raba gardama tsakanin ƙasashe, amma dole ne sai duka ƙasashen biyu sun amince su bayyana a gabanta.

Kotun za ta duba ko tsare sojojin da Burkina ta yi ya saɓa wa dokokin sufurin jiragen sama da suka danganci saukar gaggawa, da kuma ko dakarun sun shiga sararin samaniyarta ba bisa ƙa'ida ba.

Sai dai kuma, ba dole ne Burkina ta yi wa hukuncin da kotun za ta bayar biyayya ba saboda ba ta da jami'an tsaron da ke tilasta aiki da umarninta, sannan kuma shari'ar za ta iya ɗaukar lokaci.

Barazana da ƙarfin soja

Barazana da ƙarfin iko na soja na cikin hanyoyin da Najeriya za ta iya zaɓa domin nema wa dakarunta 'yanci, duk da cewa ita ce hanya mafi haɗari.

Dr. Bukarti na ganin idan komai ya ci tura, wannan ce hanya ta ƙarshe da za a bi.

"A yi wa Burkina barazanar kama nata sojojin ita ma, ko kuma a yaƙe ta, da kuma sanya mata takunkumin tattalin arziki.

"Amma wannan hanyar ta fi kowacce haɗari, saboda Burkina za ta iya kai su kotu ta ce sun shiga ƙasar ne domin tayar da fitina, wanda kuma za a iya yanke musu mummunan hukunci."