Me ya sa jirgin sojin Najeriya ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso?

Asalin hoton, NAF
A daren ranar Litinin ne ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel ta AES, wadda ta ƙunshi Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar suka fitar da sanarwar yin tir da abin da suka kira keta musu sararin samaniya da wani jirgin sojin Najeriya ya yi ba bisa ƙ'aida ba.
An bayyana cewa jirgin ƙirar C-130 na rundunar sojin Najeriya ya sauka ne a garin Bobo Dioulasso da ke ƙasar ta Burkina Faso, a ranar Litinin.
A cewar sanarwar da ƙungiyar AES ta fitar, matakin jirgin na Najeriya ya saɓa ka'idojin ƙasashen duniya, sannan suna daukar irin wannan a matsayin "laifi kan ƴancin ƙasa".
Sai dai jim kaɗan bayan haka, hukumomin Najeriya sun fitar da nasu bayanin inda suka ce "tangarɗar na'ura ce ta sanya jirgin ya sauka a ƙasar ta Burkina Faso".
Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan da Najeriya ta sanar da cewa ta kai ɗaukin gaggawa zuwa Jamhuriyar Benin, inda jiragen samanta suka daƙile ayyukan masu yunƙurin juyin mulki.
Dangantaka tsakanin ƙasashen Sahel (Nijar, Mali da kuma Burkina Faso) ta yi rauni tun bayan juyin mulkin soji da aka samu a ƙasashen.
Duk wani yunkuri da Najeriya da ma ƙungiyar ci gaban ƙasashen yammacin Afirka suka yi na ganin ƙasashen sun koma mulkin dimokuraɗiyya, abin ya ci tura.
Lamarin ya kai ga cewa ƙasashen sun bayyana ficewarsu daga ƙungiyar ta ECOWAS, tare da kafa ƙungiyar ƙasashen Sahel ta AES.
Wannan ne ya sanya sanarwar da ƙasashen Sahel suka fitar bayan saukar da jirgin sojin na Najeriya ya yi a Burkina Faso ta tayar da raɗe-raɗin ko rashin jituwar da ke tsakanin ɓangarorin biyu za ta iya ƙazancewa sanadiyyar hakan.
Muna cikin shirin ko-ta-kwana - Burkina Faso
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sanarwar ƙasashen AES ta bayyana cewa binciken hukumomin Burkina Faso ya tabbatar da cewa jirgin C130 na Najeriya ya shiga kasar ba tare da izini ba kuma jirgin na ɗauke da mutum 11 da suka haɗa da ma'aikatan jirgi biyu da sojoji tara.
Ministan harkokin cikin gida na Burkina Faso, Emile Zerbo, ya ƙara jaddada cewa jirgin ya karya dokokin kasarsu na shawagi a sararin samaniyarta ba tare da izini ba.
AES ta bayyana lamarin a matsayin abin da ya saɓa wa dokokin kasa da kasa sannan ta ce an sanya dukkan kayan kare sararin samaniya cikin shirin ko ta kwana, tare da izinin dakile duk wani jirgi da ya kuskura ya shigo ba tare da izini ba.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin ɗaukar mataki kan duk wani jirgi da ya ratsa ta sararin samaniyar duk wata ƙasa da ke yankin ba tare da izini ba ta hanyar harbo jirgin.
Wannan lamarin ya faru ne kwanaki bayan Najeriya ta tabbatar da tura jiragen yaƙi da sojojinta domin taimakawa gwamnatin Benin wajen daƙile yunkurin juyin mulki da aka yi a can.
Ƙasashen AES kuwa wato Burkina Faso, Mali da Nijar waɗanda suka fice daga ƙungiyar ECOWAS, na iya kasancewa cikin damuwa sosai kan duk wani sabon motsi na tsaro a yankin musamman ganin cewa ECOWAS ta taba barazanar shiga tsakanin soji a Nijar bayan juyin mulkin 2023
Dukkan kasashen uku, karkashin mulkin soja, na fama da dogon rikicin ta'addanci da ya daɗe yana addabar su.
Abin da ya sa jirginmu ya sauka a BF - Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Najeriya sun ce jirgin saman sojin ƙasar na NAF C-130 da ya yi saukar gaggawa a Burkina Faso yana kan aikin jigilar kaya ne zuwa Portugal, lokacin da ya karkata akala zuwa ƙasar saboda tangarɗar na'ura.
A wata sanarwa da rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta fitar, ta bayyana cewa jirgin ya tashi ne daga birnin Legas, amma sai matuƙan jirgin suka lura da wata tangarɗa, wanda hakan ya sa dole suka yi saukar gaggawa a Bobo-Dioulasso, filin jirgin sama mafi kusa.
Sanarwar ta ce: "Jami'anmu suna cikin koshin lafiya, kuma an karɓe su cikin mutunci daga hukumomin Burkina Faso."
"Ana ci gaba da shirye-shiryen kammala aikin da aka tura su. Rundunar na godiya ga goyon bayan da aka ba su, kuma muna tabbatar wa jama'a cewa rundunar za ta ci gaba da bin ƙa'idojin aiki da matakan tsaro, tare da kare lafiyar jami'anta yayin cika aikinta na kare ƙasa." in ji sanarwar.
Me ya sa bayani ya sha bamban?
Bayanin da hukumomin Najeriya suka fitar ya sha bamban da na gwamnatin sojin Burkina Faso da ƙungiyar AES, wadda ta ce jirgin Najeriya ya shiga sararin samaniyar ƙasar ba tare da izini ba, lamarin da ya sa aka kama sojojin da kuma riƙe jirgin a ƙasar.
AES ta bayyana lamarin a matsayin "karya dokar sararin samaniya da tauye ikon kasashe mambobinta." Ta ce an yi saukar ne cikin rashin mutunta dokokin kasa da kasa na jiragen sama.
Kama sojojin Najeriya da kuma rike jirgin na nuni da yadda AES ke son tabbatar da ikon sararin samaniya a sabon tsarin da suke kokarin ginawa.
Yanzu da AES ta umarci kasashenta da su harbo duk wani jirgi da ya karya musu doka, abin da a baya za a ɗauka a matsayin tangarɗar na'uara ta yau da kullum na iya rikidewa zuwa babban rikici.
Ga Najeriya, wannan lamarin na iya dagula hulɗa da makwabtan Sahel, ya kawo cikas ga zirga-zirgar jirage a yankin, tare da raunana rawar da take takawa wajen yaƙi da ta'addanci.
Wane jirgi ne Lockheed C-130 Hercules?
Rundunar sojin saman Najeriya dai ta mallaki irin waɗannan jirage na Lockheed C-130 Hercules wadanda take amfani da su domin jigilar kayan yaƙi ko kuma dakaru.
Yana ɗaya daga cikin jiragen rundunar masu muhimmanci, wanda yake taimakawa wajen safarar kayan yaƙi ko na agaji ko dakaru a ciki da wajen Najeriya.
C-130 Hercules jirgin soji ne mai inji huɗu, ƙirar ƙasar Amurka, wanda aka ƙera shi ta yadda zai iya sauka da kuma tashi a filaye, ko da ba wurin da aka gina domin saukar jirage ba.
Baya ga ɗaukar kaya, an ƙera jirgin ta yadda a wasu lokutan ana iya sarrafa shi domin wasu amfanin, kamar kai hari a sama da sintiri, da ƙara wa jiragen yaƙi mai, da neman waɗanda suka ɓace da kuma gudanar da bincike na kimiyya.
Shi ne jirgin da mafi yawan ƙasashe ke dogaro da shi wajen safarar kayan yaƙi a duniya.










