Mene ne ƙarfin sojin Najeriya?

Asalin hoton, DefenseNigeria
Tun bayan ɗaukin gaggawa da sojojin saman Najeriya suka kai ƙasar Benin inda suka taimaka wajen daƙile yunƙurin juyin mulki da sojoji suka so yi, ƴan Najeriya da ma Afirka sanin irin karfin da Najeriya ke da shi idan aka kwatantan da sauran ƙasashen Sahel.
Baya ga tura jiragen yaƙi, majalisar dokokin Najeriya ta kuma amince da buƙatar Bola Tinubu na aikewa da rundunar soji zuwa Benin ɗin domin wanzar da zaman lafiya.
Ana cikin haka ne kuma sai hukumomin Burkina Faso suka riƙe wani jirgin sojin Najeriya ƙirar C-130 tare da mutane 11 da yake dauke da su.
Ƙungiyar ƙasashen Sahel, wadda ta ƙunshi Jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso sun zargi jirgin na Najeriya da keta hurumi ta hanyar tsallake iyaka ba bisa ƙa'ida ba.
Najeriya a nata ɓangaren ta ce jirgin yana kan hanyarsa ce ta zuwa ƙasar Portugal, inda ya samu tangardar na'ura, lamarin da ya tursasa masa yin saukar gaggawa a ƙasar ta Burkina Faso, kuma hukumomin sun ce an yi komai ne "a kan tsari."
Shin irin wadannan jirage nawa ne Najeriya ta mallaka?
Bugu da ƙari, alƙaluman World Factbook sun nuna cewa dakarun Najeriyar 180 na aikin wanzar da tsaro a ƙasashen Sudan da Sudan ta Kudu, inda ta aike da dakaru 200 zuwa Gambia a ƙarƙashin ƙungiyar Ecowas sai kuma 150 da ke Guinea-Bissau nan ma a ƙarƙashin ƙungiyar Ecowas.
Wannan ne ya sa ƴan Najeriya da ma Afirka ke tambayar shin Najeriyar ce ta fi kowace ƙasa ƙarfin soji? Yaya za a kwatanta ƙarfin sojin na Najeriya da sauran ƙasashen Afirka ta yamma?

Asalin hoton, Getty Images
Yawan sojoji

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa babu tabbatattun alƙaluma dangane da yawan dakarun Najeriya, alƙaluma daga majiyar World Factbook da ke intanet sun nuna cewa Najeriya na da yawan sojoji 140,000 ya zuwa shekarar 2025.
Sai dai kuma alƙaluma daga World Bank Group sun nuna cewa Najeriya na da dakaru 223,000 ya zuwa shekarar 2020.
Ƙasar da ta kusa nunka Najeriya a yawan sojoji a fadin Afirka ita ce Masar, mai yawan dakaru 836,000 sai kuma Algeria mai 326,000, Morocco na da 246,000 ita ma Eritrea na da 202,000, Sudan tana da 144,000, Ethiopia na 138,000, Mali na 41,000.
Yawan jiragen yaƙi

Asalin hoton, Getty Images
Wasu alƙaluma game da rundunar sojin saman Najeriya kan yawan jiragen yaƙin da rundunar ke da su ya zuwa 2025 sun nuna cewa Najeriya na da jiragen yaƙi 142 waɗanda lafiyayyu ne sannan suna zaman ko-ta-kwana.
Shafin da ke bayyana ƙarfin sojin saman ƙasashen duniya na WDMMA ya zayyana yadda ake amfani da jiragen inda 35 daga cikin 142 suka kasance na zuwa filin daga da 80 da ake kai ɗauki da su da kuma 27 na atisaye.
Bayanin ya ce jiragen yaƙin Najeriya sun haɗa da:
- Alpha Jet A/E: ƙirar Faransa - 12
- F-7NI: ƙirar China - 11
- JF-17A: ƙirar Pakistan hadin gwiwa da China - 3
- A-29B Super Tucano: Daga Amurka - 12
- Jirgin soji mai saukar ungulu - 51
- Jirgin soji na jigila - 20
- Jirgin soji na bayar da horo - 27
- Jiragen sojin aiki na musamman - 9
- Jiragen yaƙi da aka yi oda - 56
To sai dai shafin World Directory of Modern Military Aircraft wanda ke wallafa yawan jiragen yaƙin dukkannin ƙasashen duniya ya nuna cewa ƙasar Masar na da jiragen da suka kai 1,065, Algeria na da 618, Angola 286, Afirka ta Kudu 225, Morocco na da 285, Kenya na da jirage 144, Habasha na da 88 sai kuma jamhuriyar Nijar da ke da 18 da Libya mai 13.
Sai dai babu bayani kan yawan jiragen ƙasashen Mali ko Burkina Faso a shafin.
Kashe kuɗi kan tsaro

Asalin hoton, Getty Images
Masana harkar tsaro na da fahimtar cewa yawan kashe kuɗi a harkar tsaro na da alaƙa da ƙarfin ƙasa a fannin ciki har da ƙarfinta na soji.
BBC ta yi bincike dangane da ƙasashen Afirka 10 da suka fi kashe kuɗi a kan harkar tsaro kamar yadda wani shafi na intanet kan harkokin bayanan soji na duniya (2025 Global Firepower),
- Masar: Wani rahoto ya yi ƙiyasin kasafin kuɗin tsaro na sojin Masar ya kai dala biliyan 5.88 a duk shekara.
- Algeria: Kasafin kuɗi na shekara-shekara na sojojin na Aljeriya kamar yadda rahoton ya nuna ya kai dala biliyan 25.
- Nigeria: Rahoton ya ce kasafin kuɗin tsaro na Najeriya ya kai dala miliyan 3.16.
- Afirka ta Kudu: Ba a san yawan kasafin kuɗi na sojojin yake ba amma ana ganin zai iya kaiwa dala biliyan 3.1 a wannan shekara ta 2025.
- Ethiopia: Rahoton ya yi ƙiyasin cewa a bana kasafin kuɗin sojin ƙasar ya kai dala biliyan 2.10.
- Morocco: Shafin tattara bayanan tsaron na duniya ya ce kasafin kuɗin sojin ƙasar ya fi dala biliyan 13.
- Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo: Kasafin sojin ƙasar na wannan shekara ya kai dala miliyan 800.
- Sudan: An yi ƙiyasin kasafin kuɗin sojin ƙasar a shekara-shekara ya kai dala miliyan 342.
- Libya: Kasafin kuɗinta na soji na shekara ya kai dala biliyan uku in ji rahoton.
Ƙarfin sojin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bisa abubuwan da aka gani a sama za a iya fahimtar cewa Najeriya ce mafi ƙarfin soji a Afirka ta yamma sannan kuma mafi ƙarfin soji a tsakanin ƙasashen Sahel.
Dangane da yawan sojoji, za a iya cewa babu wata ƙasa a yankin Afirka ta yamma da take da yawan sojojin Najeriya 223,000.
Ƙasar Mali wadda tana Afirka ta yamma sannan kuma tana cikin ƙasashen Sahel ita ce mai biye wa Najeriya da yawan sojoji 41,000.
Idan kuma aka yi batun yawan jiragen yaƙi, to nan ma Najeriya ta yi zarra a Afirka ta yamma da yankin Sahel kasancewar tana da jirage 142, inda ƙasar da ke biye mata ita ce jamhuriyar Nijar da ke da guda 18.
Idan kuma ana maganar irin kuɗin da ake kashewa a kan sha'anin tsaro, a nan ma Najeriya ta yi wa ƙasashen Afirka ta yamma da na Sahel Zarra, duk kuwa da cewa ita ma ana yi mata kallon gazawa a nan.
Ƙasar da ke biye da Najeriya wajen zuba kuɗi a harkar tsaro ita ce Libya da ke kashe dala biliyan uku.
Hakan ne ya sa masana ke harkar tsaro suke ganin cewa Najeriya na da ƙarfin soji da za ta iya kai ɗaukin soji ga ƙasashen Afirka ta yamma da ma na yankin Sahel.










