Manyan alƙawurra uku da C.G. Musa ya ɗauka game da tsaron Najeriya

Musa

Asalin hoton, X/Defence Headquarters

Lokacin karatu: Minti 7

"Bayan shafe shekaru 39 na rayuwata a cikin aikin soja, na ga duk abin da ke faruwa, na fahimci duk abin da ke faruwa kuma na san abin da muke bukata," kamar yadda Janar Christopher Musa mai ritaya ya bayyana lokacin da majalisar dattijan Najeriya ke tantance shi a ranar Laraba.

Ya kara da cewa "Za mu iya cin nasara a wannan yaki, amma wajibi ne mu yi aiki tare, wajibi ne mu samu taimako da muke bukata.”

Nadin Christopher Musa - wanda majalisar dattijan Najeriya ta tantance shi a ranar Laraba bayan shugaba Bola Tinubu ya mika sunansa - a matsayin ministan tsaro na zuwa ne yayin da kasar ke cikin wani mawuyacin hali game da tsaro.

Yayin da hankalin duniya ya juyo kan kasar bayan shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin ana kashewa da cin zarafin Kiristoci saboda addinisu, sai kuma ga karuwar hare-hare kan wuraren addini da makarantu, inda aka sace dalibai sama da 300 cikin mako daya da kuma sace masu ibada a coci.

Haka nan an kai wasu hare-haren a jihohi irin su Sokoto da Kogi, inda duk aka sace mutane, ciki har da amarya da kawayenta.

Duk da gwamnatin Najeriya ta musanta zargin ‘kisan kiyashi kan Kiristoci‘ a kasar, amma tana ci gaba da fuskantar matsi, domin kuwa ko a ranar Laraba ‘yan majalisar dokokin Amurka - a wani zama da suka yi - sun sake nanata cewa “ana kashe Kiristoci da yawa a Najeriya”.

Bayan jawabin da ya yi a gaban majalisar dattijan Najeriya kan yadda yake sa ran bullo wa matsalar tsaron kasar, sabon ministan tsaron ya kuma amsa zafafan tambayoyi daga sanatocin, kuma ya yi alkawurra wadanda suka hada da:

Bincike kan kisan Janar Uba da sace dalibai a Kebbi

Amincewa da Musa a matsayin ministan tsaro na zuwa ne yayin da Najeriya ke jimamin sace-sacen dalibai da suka faru a arewacin kasar a baya-bayan nan.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai kuma kisan Birgediya-Janar M Uba da mayakan Iswap suka yi a jihar Borno.

Bayanai sun ce mayakan Iswap sun yi wa tawagar Janar Uba kwanton-bauna ne bayan dawo daga sintiri a wani yanki na dajin Sambisa.

Duk da cewa janar din ya tsira da farko har ma ya yi magana da 'yan'uwansa, tare da bayyana musu inda yake, amma daga baya ba a sake jin duriyarsa ba.

Bayan kwana biyu ne kungiyar Iswap ta fitar da hoton janar din tare da sanar da cewa ta kama tare da kashe shi a cikin dajin Sambisa.

Lokacin da yake jawabi a gaban sanatoci, Christopher Musa ya ce "abin takaici ne a ce an kama kwamandan birged din soji, kuma abin da ya faru da shi abin damuwa ne.

"Ina tabbatar wa 'yan Najeriya cewa ba za mu bari 'yan ta'adda su rika irin haka ba, za mu yi cikkaken bincike," in ji Musa a cikin jawabin nasa.

Ya kara da cewa "na yi mamakin yadda janar din ya zama shi kadai, bayan ya kamata a ce akwai sojojinsa tare da shi, saboda haka akwai tambayoyi da ke bukatar amsa.

"Ina tabbatar maka cewa za mu yi bincike mu gano abin da ya faru, har ma da batun satar dalibai a Maga."

"Abin takaici ne a ce akwai sojoji a wurin, sai su tafi, ba da jimawa ba kuma sai wani abu ya faru.

"Ba za a lamunci hakan ba, ina tabbatar muku cewa za mubyi bincike, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci daidai da abin da ya aikata," in ji Musa.

Amfani da fasahar zamani

Janar Musa ya bukaci al'umma da su "daina biyan kudin fansa" wanda yan fashin daji kan bukata daga gare idan sun sace musu wani na kusa da su.

Sai dai tsohon babban hafsan sojin na Najeriya ya ce idan har mutane suka ci gaba da biyan kudin fansar, to "za mu yi amfani da fasahar zamani wajen bibiyar kudin."

"Amfani da fasahar zamani na da matukar muhimmanci. Idan kowane dan Najeriya na da wata lambar shaida wadda kunshi duk bayanansa - zai ba mu damar bibiyar komai," in ji Janar Musa.

Babu sulhu da 'yan bindiga

C.G. Musa ya bayyana bukatar watsi da batun yin sulhu da 'yan bindiga, lamarin da ya ce yana yin "cikas ga tabbatar da tsaro".

Ya bayyana cewa yin sulhi da yan bindiga na ba su damar sake dunkulewa domin aikata ta'asa da kuma ba su damar sayen makamai.

”Babu tattaunawa da kowane mai aikata laifi, ina ganin ya kamata mu bayyana hakan karara.

”Za mu yi aiki da ofishin mai bai wa shigaban kasa shawara kan tsaro ta yadda babu wata jiha da za ta yi hakan, domin ko an yi sulhi da su ba za su taba yin biyayya ga yarjejeniyar da aka kulla ba.

”Mun ga haka a wurare da dama, akwai kauyukan da suka yi sulhi da su amma sun dawo suna kai musu hari, za mu haramta wannan baki daya,” in ji janar Musa.

Wadanne kalubale ne a gaban C.G. musa?

Kusan za a iya cewa babban kalubalen da ke gaban sabon ministan tsaron na Najeriya shi ne batun kawar da matsalolin tsaron da ke addabar kasar ta bangarori da dama.

Boko Haram a arewa maso gabas, yan bindiga a arewa maso yamma, rikicin kabilanci da na manoma da maikiyaya a tsakiyar kasar da na Ipob a kudu maso gabas.

To amma baya ga wadannan, akwai kuma wasu kalubalen da masana ke ganin zai fuskanta, wadanda suka hada da:

Soja zuwa siyasa

Janar C.G. Musa soja ne da ya yi sama da shekara 30 yana aikin ɗamara kafin ya yi ritaya. Wannan ya sa ake ganin rayuwarsa daga samarkata zuwa manyantaka ta fi yawa ne a cikin soja.

Sai dai kasancewar yanzu ya yi ritaya, ya koma farin hula, ana ganin dole rayuwa ta zama masa daban. Sannan kuma yanzu zai maye gurbin ministan tsaro, kujerar da take ta siyasa ce.

A baya, ya fara daga ƙaramin hafsa, har ya kai ƙololuwar aikin soja, inda ya kasance wanda ya fi bayar da umarni, maimakon siyasa wanda tsari ne daban kacokam ɗinsa da aikin soja, don haka dole rikiɗewa zai iya masa wahala.

Domin jin irin yadda siyasa za ta iya masa ƙalubale, Audu Bulama Bukarti mai bincike da sharhi kan harkokin tsaro ya ce yana fata sabon ministan zai yi ƙoƙari ya janye jikinsa daga rigingimun siyasa.

Bulama ya ce ya ce suna fata ya samu nasara saboda "yana da gogewa ta sama da shekara 30 a aikin soja, don haka ya san abubuwan da sojoji suka yi na daidai, da waɗanda aka yi ba daidai ba waɗanda za a gyara."

Amma ya ce, "muna fata ba zai shiga rirgingimun ƴan siyasa ba, sannan ba zai zama irin ƴan siyasar nan da ba sa jin magana ba. Haka kuma muna fata ya zama mai kwantar da kansa wajen koyon abun da bai iya ba," in ji shi.

Bulama ya ƙara da cewa kasancewar yawanci rayuwar Musa ta fi yawa a aikin soja, dole akwai abubuwa da yawa da ya kamata ya koya waɗanda ba na aikin soja ba ne, "saboda ko a cikin aikin tsaron akwai aikin ƴansanda da sauransu da suka kamata ya natsu ya gane."

Sakar masa mara

Wani ƙalubalen da ake hasashe shi ne ko zai samu damar da yake buƙata ta juya akalar tsaron ƙasar.

A Najeriya, akwai manyan hafsoshin tsaro, waɗanda kuma suke ƙarƙashin shugaban ƙasa, sannan akwai babban mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro.

Hakan ya sa yawanci ake gani ba a fayyace aikin ofishin ministan tsaro ba, saboda yawanci ayyukan tsaro suna hannun manyan hafsoshin tsaro ne, da kuma mai ba shugaba ƙasa shawara kan tsaro.

A game da wannan, Bulama Bukarti, ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar da ikon juya sojoji ne ga shugaban ƙasa.

"Idan har ana so ya yi aiki da kyau ya samu nasara, dole sai shugaban ƙasa ya sakar masa mara, sannan ya sakar masa wasu daga cikin ikonsa domin ya samu damar gudanar da ayyukansa da kyau," in ji shi.

Matsaloli da yawa

Wani abun da ke faruwa shi ne matsalolin tsaron ƙasar sun yi yawa, inda a yanzu haka ƙasar ke fama da ƙungiyoyin ƴanbindiga da dama da suke addabar ƙasar kusan a tare.

A yanzu haka ƙasar na fama da matsalar yaƙin Boko Haram a arewa maso gabas, da matsalar ƴanbindiga a arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, da matsalar ƴan awaren Biafra a yankin kudu maso gabas da ma masu fasa bututu a kudu maso kudancin ƙasar.

Haka kuma a cikin maharan da suke addabar ƙasar, akwai ƙungiyoyi daban-daban, ƙarƙashin jagorori daban-daba, waɗanda har rikici suke yi a tsakaninsu.

Haka kuma wasu na ganin Janar C.G Musa ya riƙe muƙamin babban hafsan tsaro, kuma ko a lokacin an fuskantar matsalolin hare-hare da ake magana yanzu a wasu yankunan ƙasar da dama.

Sai dai a wata tattaunawa da BBC, Group Captain Sadiq Garba Shehu mai ritaya ya ce ko wancan muƙamin da ya riƙe ta babban hafsan tsaron ba a fayyaca bayani gamsasshe ba kan aikinsa da ma aikin da ke ofishin, "amma da ya shiga ofishin ya ɗan gyara ofishin an ɗan samu tagomashi," in ji shi.

A nasa ɓangaren, Bulama Bukarti ya ce ba maganar mutum ba ne, magana ce ta dabaru, "kawai don ka canja wani ka saka saka wani ba za a samu nasara ba. Na farko wannan dabarar yaƙin da muke amfani da ita kusan shekara 15 ke nan ana yi amma ba a samu nasara ba. Ba abun da zai canja idan ba an canja dabarar yaƙin ba," in ji Bulama.

Masanin tsaron ya ƙara da cewa akwai buƙatar a canja dabarar yaƙin daga yaƙin gaba da gaba zuwa wani sabon salo, "sannan a canja salon jibge sojoji a riƙa tura su cikin dazuka."

Alaƙa da manyan hafsoshin tsaro

Wani ƙalubalen da wasu ke hasashe shi ne alaƙarsa da manyan hafsoshin tsaron ƙasar, waɗanda sojoji ne a yanzu.

Ana dai ganin kasancewar shi ma tsohon babban hafsan tsaro ne, kuma sun kasance a ƙasa da shi, hakan zai iya taimaka masa wajen samun goyon bayansu ba kamar yadda ake zargin ana samun takun-saka ba tsakanin hafsoshin idan suna aiki da farin hula.

Sai dai kuma wasu na ganin yawanci manyan hafsoshin suna alaƙa ne kai-tsaye da shugaban ƙasa, wanda ke nufin sai dai idan an ba shi ikon sa ido kan harkokin manyan hafsoshin.

Sai dai shi Audu Bulama Bukarti na ganin kasancewarsa tsohon sojan, manyan hafsoshin tsaro na yanzu za su saurare shi matuƙa.

Sai dai masanin tsaron ya yi kira ga Musa da ya zauna ya yi dogon nazari kan ayyukan da ya yi a baya, "domin yanzu ya sake samun dama. Inda ya gane akwai kuskure ya gyara, wuraren da aka yi daidai kuma a inganta su."