Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da suka sa na yi nasara a kirifto - Ahmed XM
Fitaccen ɗan kirifto a arewacin Najeriya, Ahmed XM, ya ce haƙuri da jajircewa ne sirrukan da duk wani wanda yake son shiga harkar zai riƙa, matuƙar yana so ya samu tarin arziƙi.
Matashin, wanda asalin sunansa Ahmed Yusuf Saifullahi ne ya ce ya fara harkar kirifto ne a lokacin da yake jami'a a shekarar 2018, inda ya ce a hankali ya fara, har ya kai matakin da yake a yanzu.
Ya ce gwagwarmayar karatu da rashin isasshen kuɗi a lokacin da yake makaranta ne suka sauya tunaninsa, har ya fara neman mafita, "Ni ba ɗan masu kuɗi ba ne gaskiya. Lokacin ina makaranta sai ya zama kuɗin da ake ba mu, ba ya isa. Hakan ya sa na fara tunanin wani abu ne ya kamata in fara."
Ko da Ahmed XM ya fara binciken hanyoyin da zai bi na samun kuɗi, sai ya gane cewa akwai hanyoyi da dama, "amma sai na zaɓi in shiga harkar kirifto."
Sai dai ya ce ya yi wa harkar shigar sauri, domin a cewarsa, da farko idan ya saka kuɗi asara yake yi saboda bai da ilimin yadda ake gudanar da harkar.
"Sai na fahimci cewa idan har mutum yana so ya samu kuɗi a harkar, to dole sai ya nemi ilimin yadda ake gudanar da ita," in ji shi, wanda ya ce a dalilin hakan ne ya fara halartar darussa ta intanet yana biya, yan ƙara koya har ya iya, ya goge.
A game da jarin da ya fara harkar da shi, XM ya ce a lokacin da ya fara, "a tsakanin naira dubu 10 zuwa 20 na zuba. Amma a lokacin darajar naira ba ta yi ƙasa ba, don haka a naira dubu 10 za ka ɗan samu dalolin da za ka juya."
Me ya sa ake samun kuɗi ta kirifto?
A game da yadda ake ganin harkar na neman karaɗe duniya, Ahmed ya ce duk wani sabon abu da ya fito a duniya, sai an fara jin tsoro ko rashin yarda da shi. "kirifto sabon abu ne har yanzu, wasu har yanzu ba su ma san meye kirifto ba, wasu kuma sun sani, amma ba su damu da shi ba. Amma a cikin sabbin abubuwa akwai babbar dama."
Ya bayyana cewa har yanzu kashi 1 na mutane ne kawai suka fahimci haƙiƙanin abin da kirifto ke nufi, da yadda ake amfani da shi wajen samun kuɗi. "Wani mutum na iya shiga harkar yau, cikin ƴanwatanni ya yi arziki, saboda har yanzu kasuwar ba ta cika ba, akwai damarmaki."
Bambanci tsakanin Kirifto da Mining da Forex
Wani abu da yake ruɗar da mutane shi ne sanin haƙiƙanin bambancin tsakanin mining da kirifto da forex, lamarin da Ahmed ya ce akwai bambanci sosai a tsakanin su.
- Kirifto yana nufin kasuwancin kuɗaɗen zamani (digital currencies) kamar Bitcoin, Ethereum da sauransu. Yana da sassa biyu: Spot Trading da Futures. Spot Trading: Kamar sayen fili ne: ka saya, ka ajiye, idan farashi ya tashi sai ka sayar. Shi kuma futures: Wannan yana buƙatar ilimi sosai domin gudanar da bincike da nazarin yadda kasuwar take tafiya, da hasashen yadda za ta kasance.
- Mining: Wannan kuma wani ɓangare ne na kirifto, wanda kamar mutum ne idan ya ƙirƙiri sabon kuɗin intanet, sai ya ba mutane su tallata masa, idan ya shiga kasuwa kuma ya biya su kuɗin lada.
- Forex: Shi kuma forex yana nufin musayar kuɗin ƙasashe. Bambancin shi ne kirifto kuɗaɗen intanet ake kasuwanci, shi kuma forex kuɗaɗen ƙasashen waje.
Nasarori da ƙalubale
Matashin, wanda yanzu yake cikin attajirin matasan da ake gani a arewacin Najeriya, ya ce ya sha gwagwarmaya sosai, wanda a cewarsa hakan ya sa ya miƙe domin 'yaƙi da talauci'.
Ya ce mahaifinsa soja ne, kuma sun taso a gida mai ɗaki daya da falo daya su biyar. Ya ce wani lokaci har kuɗin ɗakin makarantarsa ya zuba a kirifto – kuma ya yi asara. "Sai na koma zama a ɗakin abokina, kuma abincinsa nake ci," in ji shi.
A ɓangaren nasarori ya ce kyautata wa iyayensa da yake, suke rayuwa cikin jin daɗi ne babbar nasarar da ya samu.
"Bayan haka na samu lambar girmamawa a Dubai da Singapore da sauran wurare da dama. Bayan haka kuma akwai motoci da gidaje da nake da su."
Ya kuma ce buɗe makarantar koyar da ilimin cyrpto na cikin abubuwan da yake alfahari da su, domin a cewarsa,"hakan zai ba ni damar taimakon wasu."
Haka kuma matashin ya bayyana assasa gidauniyarsa ta XM Foundatin, wadda yake amfani da ita wajen ayyukan jin ƙai a matsayin nasara, domin a cewarsa, yana amfani da ita wajen sanya farin ciki a zukatan mutane.
Sirrin nasara
A game da hanyoyin da ya bi ya samu nasarar da ya kai, XM ya bayyana wasu abubuwa a matsayin sirrukan nasararsa kamar haka:
- * Neman ilimi
- * Rashin jin cewa ya fi kowa
- * Tsara rayuwa da kyau
- * Tunawa da inda ya fito
"Ban taɓa jin cewa na fi kowa ba. Ina koyar da mutane, har Turawa, amma har yanzu kullum ina neman ilimi."
Shiga nan domin kallon cikakkiyar hira.