Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ta yaya tashin farashin Bitcoin zai shafi sauran kuɗin Kirifto?
A karon farko a tarirhi farashin kuɗin kirifto na Bitcoin ya zarta dala 100,000.
Farashin Bitcoin ya ci gaba da samun tagomashi ne tun bayan da Donald Trump ya lashe zaɓen shugaban Amurkaa watan Nuwamba.
Ana hasashen cewa zaɓaɓɓen shugaban na Amurka zai sauƙaƙa ƙa'idodin da ke tattare da yadda ake gudanar da harkokin kirifto, kuma ya yi alƙawarin mayar da Amurka ta zama cibiyar kirifto ta duniya.
A ranar Laraba, Mista Trump ya zaɓi Paul Atkins, wani babban ma'abocin kudin kirifto a matsayin shugaban hukumar SEC - wadda ke kula da ɓangaren hada-hadar kuɗi ta Amurka.
Ba Bitcoin ne kaɗai kuɗin kirifto ba, to sai dai shi ne ya fi kowane tagomashi da karɓuwa tsakanin ma'abota kirifto a faɗin duniya.
To ko ta yaya tashin darajar Bitcoin ɗin zai shafi sauran kuɗin kirifto da ake ta'ammali da su a faɗin duniya?
Zarta dala 100,000 da darajar Bitcoin ɗin ya yi a baya-bayan nan ya sa ma'abota harkar kirifto a faɗin duniya na ta murna.
Muhammad Inuwa Ali, wani masanin hada-hadar kuɗaɗen kirifto ne a Najeriya ya kuma shaida wa BBC cewa abubuwa biyu ne suka haddasa tashin darajar Bitcoin ɗin a duniya.
Abin da ya sa darajar Bitcoin ta ɗaga a duniya
Muhammad Inuwa Ali ya ce akwai abubuwa har uku da suka sanya darajar Bitcoins ya ɗaya a dunya.
Abu na farko a cewarsa akwai nasarar da Donald Trump ya samu a zaɓen shugabancin Amurka.
''Tun a lokacin yaƙin neman zaben yake alƙawarta cewa idan Amurka wa suka zaɓe shi zai ƙarfafa harkar kirifto, to kuma idan ka duba tun lokacin da ake bayyana sakamakon zaɓen, musamman da sakamakon jihohin bakwai marasa tabbas a zaɓen ƙasar, daga lokacin ne darajar Bitcoin ya fara ɗagawa," in ji shi.
Ya ƙara da cewa hakan ya sa an samu ƙarin masu zuba jari a harkar kirifto, kasancewa zaɓaɓɓen shugaban Amurka - wadda ita ce ƙasar da ta fi kowace ƙarfin tattalin arziki a duniya - ya alƙawarta aiki da harkar kirifto.
Abu na biyu a cewar masanin kirifton shi ne yadda Donald Trump ke ci gaba da naɗa mutanen da ke mu'amala da harkar Kirifto.
''Idan ka duba Elon Musk da ya naɗa a matsayin shugaban hukumar da ke lura da inganta harkokin gwamnati, mutum ne mai mu'alama da kuɗin kirfto, to hakan ya ƙara wa masu zbua jari a harkar kirifto ƙwarin gwiwa'', in ji shi.
Masanin ya ƙara da cewa akwai wasu biliyoyin daloli da kamfanin Tesla mallakin Elon Musk, ya ajiye a Bitcoin ɗin.
Abu na uku shi ne raɗe-raɗin da ake yi cewa China za ta ɗage takunkumin da ta sanya wa Bitcoin, kamar yadda Muhammad Inuwa Ali ya bayyana.
''Mafi yawan ƙasashen yankin Asiya da masu tafiya a kan tsarin kwamunisanci ba sa ta'ammali da Bitcoin, abin da ya sa wasu ƙasashen yankin irin China da Indiya suka sanya wa kuɗin takunkumi, wani abu da ya haifar da fargaba ga masu zuba jari a harkar''
Amma a wannan makon sai aka yi ta raɗe-raɗen cewa China za ta ɗage takunkumin, lamarin da ya sa Muhammad Inuwa Ali ke ganin cewar hakan ya taimaka wajen ƙara wa masu zuba jari ƙarfin gwiwa.
'Bitcoin zai iya kai wa dala 200,000'
Masanin kuɗin kirifton ya ce ana hasashen cewa idan aka rantsar da Donald Trump a watan gobe, to darajar Bitcoin za ta ci gaba da ɗagawa, saboda yadda gwamnatinsa za ta ƙara inganta alaƙa da kirifto.
''Idan ba ka manta a lokacin yaƙin neman zaɓensa ya alƙawarta cewa zai bai wa harkar kirifto muhimmanci a gwamnatinsa''.
''Ana hasashen cewa darajar Bitcoin zai iya kai wa dala 200,000 ko ma fiye, kuma ba abin mamaki ba ne, domin idan ka duba shekara 10 da suka wuce Bitcoin bai ma kai ala 12,000 ko ƙasa da haka'' a cewarsa.
Ta yaya hakan zai shafi sauran kuɗin kirifto da ake minning?
Masanin ya ce tashin kuɗin Bitcoin zai shafi duka sauran kuɗaɗen kirifton da ake mainin musamman a ƙasashen na Afirka kamar Najeriya, saboda ai duka harkar kirifto ce ta samu tagomashi.
''Akwai wani abu da ake kira 'Bull run', wato lokacin da kuɗin kirfito ke hauhawa sosai, wanda sau ɗaya ake samunsa cikin shekara uku ko huɗu,'' in ji shi.
Ya ƙara da cewa lokaci na ƙarshe da aka samu Bull run shi ne a 2021 bayan hawan shugaba Biden.
Ya ci gaba da cewa a duk lokacin da aka samu wannan yanani na 'Bull run' to kowane kuɗin kirfto darajarsa na tashi sosai.
''Don haka muna sa ran ganin cewa nan da wani lokaci duk wani kuɗin kirifton da ake mining darajarsu zai tashi ya ɗaga sasai'', in ji masanin na kirifto.
Wannan zai shafi duk wani kuɗin kirifto ne da aka ƙaddamar da shi a kasuwar hada-hadar kirifto ta duniya.
Me ya sa ƴan Najeriya ba su amfani da Bitcoin sosai?
Masanin Kirifton ya ce abin da ya sa ƴan Najeriya ba su ta'ammali da Bitcoin shi ne tsadarsa.
''Abin da yake faruwa yanzu shi ne gaskiya ba kowa ne zai iya cire kuɗi ya sayi Bitcoin har dala 100,000 a Najeriya ba, idan ka lissafa kudin ya kai miliyoyin naira''.
Sai ya ce hakan ba zai hana a samu ƴan Najeriyar da ke ta'ammali da kuɗin na Bitcoin ba, amma dai ba su da yawa a cewarsa, kamar na sauran kudin kirifton da ake mainin.
Yaushe aka fara amfani da Bitcoin?
An fara wallafa Bitcoin ne a wani jerin sakonni na intanet ga masana kimiyyar komfuta da ke karantar yadda za a iya aika sako ta intanet cikin tsaro a 2008.
Wanda ya fara wallafa shi na da wani suna na bogi Satoshi Nakamoto amma babu wani mutum ko mutane kawo yanzu da aka tabbatar shi ne Satoshi.
Bitcoin wani nau'i ne na kuɗin intanet. Ba shi da siffa ta zahiri. Madadin haka, ana sayar da rukunin kuɗin a intanet da sauran shafukan sada zumunta.
Ba shi da wata iyaka, ma'ana a wasu shafuka ne kaɗai za a iya amfani da shi da sauran na'ukan kuɗin na kirifto, sannan ba su da banki, kamar kuɗin zahiri da aka sani.
A maimakon haka, yana aiki ne a hanyoyin intanet da wasu dubban na'urori da ke haɗawa da ajiye bayanan yadda ake kashe kuɗin.