Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bayanan da kuke son sani kan fashewar sabon nau'in kuɗin kirifto na Notcoin
A ranar Alhamis ɗin nan ne dai sabon nau'in kuɗin intanet na Kirifto da ake kira Notcoin ya fashe, bayan da manyan kamfanoni masu hada-hadar kuɗin na intanet suka ayyana shi a matsayin kuɗin da za a iya hada-hadarsa wato 'Exchanger'.
Fashewar dai ta faru ne bayan kimanin watanni shida masu bibiyar kirifton suna renon sa da ake kira da "mining".
Hakan ce ta sa muka tambayi Sagiru Abdullahi Ɓuruku wani wanda ya ci gajiyar Notcoin kuma masanin hada-hadar kuɗin intanet na kirifto. Ga kuma ƙarin hasken da ya yi mana kan fashewar sulanlan Notcoin.
Mene ne Notcoin?
"Notecoin sulanlan intanet ne na kirifto da ake samarwa ta hanyar 'mining'.
Shugaban kamfanin mai suna Sasha Plotvinov ya ƙirkiri tsarin ne mai kama da wasa ko kuma 'game' ta hanyar manhajar Telegram.
Ana aikewa da adireshin ga mutane inda su kuma za su bi adireshin a kowane lokaci domin buga game ɗin har ka tara 'points' da ake kira sulanla.
Daga nan kuma sai aka haɗa 'points' ɗin, inda aka mayar da su zuwa wata takardar shaidar mallakar kuɗi da ake kira 'voucher'.
To wannan 'voucher' ɗin ce masu 'mining' za su sayarwa masu son saya - abin da ake kira fashewa." In ji Sagiru Abdullahi Ɓuruku.
Dangane kuma da darajar notcoin Sagiru ya ce an sayar da kowane sulan na notcoin a kan 0.1$, a ranar Alhamis.
"Idan ka haɗa notcoin guda 1000 farashinsa zai zama dala 100, kwatankwacin naira 150,000 na Najeriya. Sai dai kuma a ranar Alhamis ɗin sakamakon cunkoso da aka samu ba kowane ya samu wannan tagomashin ba." In ji Sagiru.
Me ya sa Notcoin ya samu tagomashi?
Masana hada-hadar kuɗin intanet na kirifto sun ce ya zamo tsarin da ya fi kowanne samun tagomashin fashewa a baya-bayan nan.
"Dalili shi ne yadda shugaban tsarin ya yi amfani da manhajar Telegram inda suka rinƙa aike da adireshi domin jama'a su bibiye shi.
Saɓanin sauran sulanlan inda suke amfani da manhajar da za a sauke a waya. To ka ga ba kowane yake da wayar da zai sauke manhaja ba.
Shi kuwa notcoin sun yi wayo inda suka yi amfani da Telegram wanda yana da mabiya da yawa.
Sannan wani ƙarin dalilin shi ne yadda notcoin ya samu masu 'mining' da yawa fiye da mutum miliyan 35." In ji masanin kirifton.
'Notcoin zai ci gaba da zama a fashe'
Sagiru Abdullahi wanda shi ma ya samu amfani daga fashewar sulanlan na notcoin ranar Alhamis ya ce kuɗin zai ci gaba da samun tagomashi "har sai illa masha Allahu ".
"Ai yanzu tunda ya riga ya samu ayyanawa daga kamfanonin hada-hadar kuɗaɗen intanet na kirifto irin su Binance da sauran su, ai ya riga ya zama abin warwaso har duniya ta tashi." In ji Sagiru.
To sai dai da alama duk wanda bai bautawa tsarin ba har zuwa yanzu bayan fashewar sulallan, to fa shi sai dai ya siya da kuɗinka daga wurin waɗanda suka yi 'mining' din.
Mene ne kuɗin intanet na Kirifto ko Bitcoin?
An fara wallafa Bitcoin ne a wani jerin sakonni na intanet ga masana kimiyyar komfuta da ke karantar yadda za a iya aika sako ta intanet cikin tsaro a 2008.
Wanda ya fara wallafa shi na da wani suna na bogi Satoshi Nakamoto amma babu wani mutum ko mutane kawo yanzu da aka tabbatar shi ne Satoshi.
Bitcoin wani nau'i ne na kuɗin intanet. Ba shi da siffa ta zahiri. Madadin haka, ana sayar da rukunin kuɗin a intanet da sauran shafukan sada zumunta.
Ba shi da wata iyaka, ma'ana iya shafukan da za a iya amfani da su, sannan ba su da banki, kamar kudin zahiri da aka sani.
A maimakon haka, yana aiki ne a hanyoyin intanet da wasu dubban na'urori da ke hadawa da ajiye bayanan yadda ake kasha kuɗin.