Xavi ya tsawaita Kwantiraginsa a Barcelona

Xavi Hernandez

Asalin hoton, Getty Images

Kociyan Barcelona Xavi Hernandez ya tsawaita kwantiraginsa a kungiyar har zuwa shekara ta 2025 tare da zaɓin ƙarin shekara ɗaya, a cewar kungiyar a wata sanarwa a ranar Juma'a.

Kocin mai shekaru 43 ya karɓi ragamar Barcelona kan kwantiragin shekaru uku bayan tafiyar Ronald Koeman ɗan ƙasar Holland a karshen shekarar 2021.

Tsohon ɗan wasan ƙasar Sifaniya Xavi ya jagoranci Barca a wasanni 96, inda ya samu nasara a 61, da canjaras guda 16, sannan ya yi rashin nasara a 19.

Ya lashe kambun farko a kakar wasan da ta wuce inda ya lashe kofin Spanish Super Cup sannan ya jagoranci kungiyar ta lashe gasar La Liga ta 27 wanda shi ne na farko cikin shekaru huɗu.

Xavi ya shafe tsawon shekaru 17 a matsayin ɗan wasa a kungiyar ta Camp Nou da ke Catalonia, inda ya lashe kofuna 25 - ciki har da kofunan La Liga takwas da na gasar Zakarun Turai huɗu a wasanni 767.