Yadda saurayi ya 'fille kan budurwarsa' a Nasarawa

Asalin hoton, FB/Salome Adaidu
Ana ci gaba da alhinin wata budurwa mai suna Salome Adaidu, wadda ake zargin saurayinta da fille mata kai a jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya.
Jami'an tsaro ne suka damƙe saurayin mai suna Timileyin, wanda mawaƙin yabo na addinin kirista ne, ɗauke da kan Adaidu, a ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu, kusa da wani coci.
Lokacin da take bayani kan lamarin, Anibe Treasure, wadda ƙawa ce ga marigayiyar ta ce ta ga labarin cewa wani ya fille kan budurwarsa a shafukan sada zumunta amma ba ta san cewa ƙawarta ba ce har sai lokacin da ta je wurin aikinta, ta ga fayau.
Ta ce abokan aikin marigayiyar ne suka sanar da ita game da lamarin a lokacin da ta tambaye su inda ƙawar tata take.
Ta rubuta a shafinta na facebook cewa "Allah jikan ki Salome kuma wanda ya kashe ki zai fuskanci hukunci."
Yadda ƴansanda suka gano gawar Salome
Mai magana da yawun rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Nasarawa, Rahman Nansel ya ce bayanan da suka tattara sun nuna cewa ɗan acaɓa ne ya ɗauko wani matashi mai shekara 32 mai suna Timileyin a ranar 11 ga watan Janairu, daga Kabba na jihar Kogi zuwa Karu a jihar Nasarawa.
Sai dai daga baya ɗan acaɓan ya gano cewa jini na ɗiga daga jakkar da matashin ke riƙe da ita, lamarin da ya sanya ya nemi ɗaukin mutane, waɗanda suka taru suka riƙa dukan Timileyin.
"Mutane sun yi wa Timileyin duka, sannan wasu daga ciki suka kira ƴansanda. Mun samu nasarar ceto matashin inda muka same shi ɗauke da kan mutum. Daga nan sai muka kai shi asibiti," in ji Nansel.
Nansel ya ce sun ci gaba da bincike kan lamarin, inda suka je gidan Timileyin domin yin bincike, inda a nan ne suka gano gawar Salome Enejo Adaidu, ƴar shekara 24, a cikin buhu.
"Mun samu takardar izinin, inda muka bincika gidansa muka gano gawar matashiyar mai hidimar ƙasa, Salome Enejo Adaidu, wadda aka daddatsa aka zuba a cikin buhu."
Ƴansanda sun ce ba su da masaniya game da alaƙar da ke tsakanin marigayiya Salome da Timileyin.
'Mahaifiyarta ta yanke jiki ta faɗi'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Abby Simon, wadda ƙawa ce ga Salome Adaidu ya shaida wa BBC cewa wannan ba ƙaramin tashin hankali ba ne ga mahaifiyar marigayiyar kasancewar bai fi wata bakwai ba da ta rasa mijintya.
Ta bayyana cewa a lokacin da lamarin ya faru, mahaifiyar Salome ba ta gari, saboda ta yi tafiya domin bikin kirsimeti, amma a lokacin da aka sanar da ita game da rasuwar ƴar tata, nan take ta yanke jiki ta faɗi saboda kaduwa.
"Mahaifiyarta ta yi tafiya tun mako biyu da suka gabata, kuma jiya ne aka kira ta aka sanar da ita game da rasuwar ƴarta," in ji Abby.
"Lokacin da ta isa gida ne suka faɗa mata labarin, nan take ta yanke jiki ta fadi, ba ta iya ko motsi."
Abby ta bayyana cewa a lokacin da ƴar'uwar marigayiyar ta isa gidansu da ke garin Orozo, inda ake zargin Timileyin da kashe Salome, ta iske gidan faca-faca da jini da kuma kayanta a warwatse.
Abby ta ce Salome ta fita daga gida ranar Asabar bayan ta gama kimtsa gidan, da nufin zuwa ganin saurayinta wanda ke zaune a unguwar Karu da ke gefen birnin Abuja, sai dai ba ta ƙarasa gidan nasa ba.
Ta ce a cikin garin Orozo ne Timileyin ya kashe tare da daddatsa Salome, daga nan sai ya kwashi sassan jikinta a cikin buhu ya hau babur zuwa garin Oke a jihar Nasarawa, sai dai a lokacin da suke tafiya ne mai babur ɗin ya gane cewa jini na ɗugowa daga cikin buhun da ke hannun Timileyin.
"A garin Oke aka kama shi bayan da ɗan acaɓar da ya ɗauke shi ya janyo hankalin mutane saboda ya ga jini na ɗiga daga buhun, daga nan ne jama'a suka taru."
Ta ce a lokacin ne mutane suka hau Timileyin da duka, daga nan kuma sai aka kira ƴansanda domin su tafi da shi.
"Ba soyayya suke yi ba, saboda ba ta sanar da iyalinta game da shi ba. Mu a nan al'umma ɗaya ce duk mun san juna, saboda haka ba soyayya take yi da Timileyin ba," in ji ta.
"Babu wani ɗan'adam da ya cancanci a yi masa irin wannan kisa, koda kuwa ita budurwarsa ce bai kamata ya kashe ta haka ba," in ji Abby.










