Ko sarakuna na da rawar da za su taka a siyasar Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da siyasar Najeriya ke ƙara ɗaukar ɗumi gabanin babban zaɓe na 2027, ɗaya daga cikin muhawarorin da ƴan ƙasar ke yi ita ce kan tsoma bakin sarakuna a cikin harkokin siyasa.
Yayin da har yanzu aka kasa cimma wata matsaya a muhawarar, ana ci gaba da zargin wasu manyan sarakuna a ƙasar Hausa da nuna goyon bayansu ƙarara ga wasu ƴansiyasa.
Na baya-bayan nan shi ne bidiyon da aka ga Sarkin Daura Faruk Umar Faruk na yin wasu kalamai masu alaƙa da siyasa a fadarsa da ke jihar Katsina.
Bidiyon ya janyo cecekuce, musamman a shafukan sada zumunta, inda wasu ke muhawara kan irin rawar da sarakunan gargajiya za su iya takawa a fannin siyasa.
Kundin tsarin mulkin Najeriya bai fayyace takamaimiyar rawa da sarakunan za su iya takawa ba a harkokin siyasa, kuma akasarinsu na aiki ne ƙarƙashin jagorancin gwamnonin jiha.
'Malamai da sarakuna'
Tijjani Zangon Daura ɗaya ne daga cikin dattawa a arewacin Najeriya da ke nuna damuwa kan yadda wasu sarakuna da malaman addini ke tsoma baki dumu-dumu kan harkokin siyasar.
A ganinsa, siyasar ma ta samu tazgaro ne kacokan saboda su.
"Siyasa yanzu ta koma ta iyayen gida. A ganina bayan ƴansiyayar, waɗanda suka ɓata tsarin siyasar su ne sarakuna da malaman addini da kuma tsarin mulkin da muke ciki," a cewarsa yayin wata hira da BBC.
"An ga yadda malamai da wasu ƙungiyoyin malamai ke hawa mambari suna kuranta wani ɗansiyasa, su ce a zaɓe shi. Sarakuna kuma sun zubar da martabarsu."
Zangon Daura ya nuna cewa bai kamata sarki na gargajiya ya nuna ra'ayi na siyasa ba, yana mai cewa kalaman da sarkin Daura ya yi ya dame su a matsayin mazauna masarautar.
"Shi ba ɗansiyasa ba ne, bai kamata ya yi waɗannan kalamai ba."
Ita ma Dr Raliya Zubairu Ahmad ta sashen nazarin tarihi a kwalejin ilimi ta Sa'adatu Rimi da ke, ta amince cewa bai kamata sarakuna su dinga saka baki a siyasa ba.
"Kamata ya yi sarki ya zama uban kowa, bai kamata ya sa hannu a cikin siyasa ba," in ji ta.
"Kuma tsoma baki a siyasar ke janyo musu rashin kima a hannun ƴansiyasa. Kamata ya yi sarki ya zama mai sa ido mai kuma bayar da shawara."
Rawar da ya kamata su taka
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ganin Dr Kabir Danladi Lawanti, malami a sashen koyar da aikin jarida na Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria, ba za a iya gane haƙiƙanin rawar da sarakuna za su taka ba har sai an yi gyara a tsarin mulki na Najeriya.
"Abin da ya kamata a fara yi shi ne samar musu da matsayi a tsarin mulkin Najeriya, wanda shi ne zai ba su damar yin wani abu," a cewarsa.
"Saboda haka tsarin dimokuraɗiyya majalisa, da ɓangaren shari'a, da kuma shugaban ƙasa kawai ya tanada, kodayake dai har yanzu ana ganin kimarsu a al'adance a matsayinsu na masu kare al'adu."
Malamin jami'ar ya ƙara da cewa maimakon duba abin da za su iya yi a siyasance, zai fi kyau a duba rawar da za su taka a gwamnatance.
"Amma a yanzu daga cikin rawar da za su taka ba za ta wuce wayar da kan al'umma ba ta hanyar faɗakar da su muhimmancin yin katin zaɓe, da kuma kaɗa ƙuri'ar kanta," a cewar Dr Lawanti.
Sai dai kuma Farfesa Tukur Baba na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto na ganin duk da haka akwai babbar rawar da sarakunan za su taka.
"Saboda kimarsu a tsakanin al'umma, za ka ga 'yansiyasar ma sarakuna suke nema idan suna son yaɗa wata manufa da ta shafi rayuwar al'umma," kamar yadda ya bayyana.
Amma ya gargaɗi sarakunan game da lokacin da ya kamata su haɗa kai da gwamnatin siyasa.
"Lokacin da za a samu matsala shi ne yayin neman ƙuri'a. Idan wani sarki ya goyi bayan wani ɗantakara za a iya samun matsala idan 'yan'adawarsa suka yi nasara."
Lokacin da aka fara karya lagon sarakuna
Farfesa Shu'aibu Shehu Aliyu, shugaban Cibiyar Bincike da Adana kayan Tarihi ta Arewa House da ke Kaduna ya ce tun bayan cire sarakuna da dama da gwamna Lugga (Lord Lugard) ya yi a arewacin Najeriya, babban dalilin da ya fara janyo ƴan siyasa su raina sarakan gargajiya shi ne lokacin da aka fara siyasa a Najeriya a 1952, inda aka zaɓi wakilai daga lardunan uku na Najeriya.
"To a wannan lokaci an samu saɓani tsakanin mutanen da aka zaɓa suka zama ƴan majalisa daga lardin arewa da sarakan yankunansu. Misali an zaɓi mutum ya zama minista kuma idan ya koma garinsu zai shiga fadar sarki da takalmi sannan ya gaisa da sarki.
Wannan ne ya fara janyo rikici tsakanin ƴan siyasa da masarautu. Duk da dai daga baya an sauya cewa dole ne kowa idan ya koma gida ya yi biyayya ga al'adun gargajiya.
A baya kafin juyin mulkin farko, akwai majalisar sarakuna sannan sarakuna na cikin harkokin gwamnati inda wasu sarakunan ma suka zama ministoci kamar sarkin Kano Muhammadu Sanusi I ya taɓa zama gwamnan riƙon ƙwarya. Sannan sarkin Zazzau Jafaru ya taɓa zama minista. Haka ma sarkin Katsina Usman Nagwaggo ya taɓa zama minista". In ji farfesa Shu'aibu Shehu Aliyu.
Farfesa Shu'aibu ya ƙara da cewa an fara karya lagon sarakuna ne a shekarar 1966.
"To amma bayan juyin mulki musamman lokacin da aka yi gyaran tsarin mulki da ya samar da ƙananan hukumomi a 1966 sai aka fara cire wasu iko da sarakan gargajiya ke da su misali 'yan doka da kotuna duk aka cire su daga hannun sarakuna."
Haka aka yi ta yi har karshe lokacin da aka yi wa dokar ƙananan hukumomi kwaskwarima a 1988 wanda aka cire hannun sarakuna daga hannun mulki aka bar su tsurarsu".
Abin da ya fi takaici ma shi ne yadda aka mayar da su ƙarƙashin 'yan siyasa misali hakimi na ƙarƙashin shugaban ƙaramar hukuma. Ko tafiya zai yi sai da izini. Hatta albashinsu na hannu ƙananan hukumomi". kamar yadda farfesa ya ƙara haske.










