Ramadan: Bambanci tsakanin azumin Musulmi da na Kirista

Azumi

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 6

Azumin watan Ramadan yana ɗaya daga cikin ginshikan Musulunci guda biyar da suka wajaba a kan kowane Musulmin da ya kai munzalin yi - baligi, mai hankali, kuma mai cikakkiyar lafiya.

Kamar yadda yake a Musulunci, mabiyan wasu addinai ma kamar addinin Kirista suna gudanar da azumi.

Sai dai akwai bambance-bambance tsakanin azumin mabiya addinin Musulunci da na Kirista - ko da yake dukkansu suna yin azumin domin neman kusanci ga Ubangiji.

Malamai da dama sun bayyana cewa bambance-bambancen sun haɗa da cewa Musulmai na yin azumi na kwana 29 ko kuma talatin kamar yadda hadisi ya tabbatar daga Manzon Allah (SAW) cewa, wata a Musulunci yana yin kwana 30 ne ko kuma 29, don haka azumi zai iya kasancewa kwana 30 ko 29.

Amma kuma bayanai sun nuna cewa a addinin Kirista ba haka ba ne wanda su azuminsu na kwana 40 ne domin sun yi imanin cewa annabi Isa (AS) ya zauna kwana 40 bai ci abinci ba wanda aka ruwaito cewa a wannan lokacin ya yi sadaka ya yi addu'oi yayin azumin.

Ustaz Murtala Muhammad Gusau, limamin Masallacin Jumma'a ne da ke garin Okenen jihar Kogi a Najeriya, kuma shugaban wata cibiyar yaɗa addinin Musulunci da karantarwa a garin na Okene, kuma a tattanawarsu da BBC ya ce akwai bambance-bambance sosai tsakanin azumin Muslmai da na Kirista har ma da na Yahudanci.

''Azumi dai shi ne bautawa Allah ta hanyar kamewa daga cin abinci da abin sha da jima'i, tun daga hudowar alfijir har zuwa faɗuwar rana."

A kowace shekara cikin watan Ramadan Musulmai a faɗin duniya na gudanar da azumin kwana 29 ko 30, wanda ya sha bamban da na mabiya addinin Kirista da na Yuhudanci da su kan yi azumin kwana 40 ne.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ƙara da cewa ''Amma duka manufarsu kusan ɗaya ne - Musulmai na yin azumi a bisa bin umarnin Allah da nufin gyara ɗabi'u da halayyar al'umma ta zama mai tsoron Allah, sannan kuma a tunatar da Musumai game da watan da aka saukar da Alƙur'ani mai girma wato cikin watan Ramadan.''

Sheik Ibrahim Adamu Disina wani fitattaccen malami ne a jihar Bauchi arewa maso gabashin Najeriya, ya yi wa BBC ƙarin bayanin cewa Musulmai kan fara azumi tun daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana inda sukan kauracewa ci da sha da jima'ai.

''Musulmai na azumtar kwana 29 ko 30, yayin da Kiristoci ke azumtar darare 40 da yini 40 ko kuma kwana 40, amma kowanne akwai bambance-bambance wajen yanayin da ɓangarori biyu ke azumin''.

''Kiristoci kan yi azumin ne ba tare da ya hana musu cin wasu abubuwa ba,'' in ji shi.

Haka shi ma Ustaz Murtala ya yi ƙarin bayani cewa , Kiristoci na yin azumin a duk shekara amma kuma kamar yadda Musulunci ya tanada cewa ya zama wajibi a kan duk Musulmi baligi, mai cikakkiyar lafiya ya ɗauki azumin watan Ramadan, su Kiristoci ba kowa ne ya ke yi.

''Yawanci malamansu da sauran jagororinsu ne kawai suke yin azumin, sannna kuma suna iya zamantowa mutum gashi yana azumi amma zai iya cin wasu abubuwa abin sha ne kawai ba za sha ba, ko kuma ya kasance ba zai ci ba gaba ɗaya har tsawon kwana 40,'' in ji malamin.

Yahudawa ma na azumi

Malam Murtala Muhammad ya bayyana cewa baya ga mabiya addinin Kirista, mabiya addinin Yahudanci ma na nasu azumin, kuma yana kaman da na Kiristoci.

''Kamar yadda muke da azumi a addinan Musulunci da na Kirista haka su ma mabiya addidin Yahudanci ke yi, domin tunawa da Annabi Musa (AS) a lokacin da ya je ya karɓo wa allunan nan masu ƙunshe da umarni goma daga Ubangiji a tsaunin Sinai", ya ce.

''Duka dai don kauce wa aikata ayyuka marasa kyau - manufar ita ce a samar da al'umma masu tsoron Allah, masu imani, masu tausayi''.

''Masu addinin Yahudanci suma kamar mabiya addinin Kirista, ba kowa ba ne ke yin azumi, amma Musulmi duk kowa da malamai da masu arziki da talakawa ya wajaba a kan su.''

Azumi a addinin Kirista

A ɓangaren azumin mabiya addinin Kirista, Rabaren Joseph John Hayab shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Katsina, ya yi wa BBC ƙarin bayani cewa Littafin Injila mai tsarki ya koya wa mabiya addinin Kirista su yi azumi.

Ya kuma ce Yesu Kiristi wanda shi ne tushen addinin nasu shi ma ya yi azumi wanda ya nuna cewa idan akwai wasu matsaloli da suka addabi mutum ko kuma al'umma, hanyar magance su shi ne azumi da addu'a.

Malamin addinin Kiristan ya ce azumi wani babban abu ne a cikin addinin Kirsita, amma sai dai akwai bambanci tsakanin yadda mabiya addinin Kirsita ke yi da kuma na Musulmai.

''Bambancin da ke akwai na azumin da Kirsistoci ke yi da kuma sauran addinai shi ne mu muna azumi ne a kullum domin mu ƙara samun ƙarfi wajen neman albarkar Allah a rayuwarmu.''

''Ba mu da wani ƙayyadadden lokaci da aka ce za mu yi azumi kamar yadda a Musulunci ake yi da watan Ramadan,'' in ji Rabaren John.

Amma kuma Rabaren ɗin ya yi ƙarin bayanin cewa akwai wani lokaci da wasu ɓangarorin mabiya addinin Kirsita ke yin azumin kwana 40 da ake kira ''Lent'' wanda ba kamar na Ramadan ba shi ba doka ba ne sai wanda ya ga zai iya zai yi domin neman kusanci da Allah.

''A Kiristanci idan ka zaɓi za ka yi azumi ya danganta ga yadda ka tsara, ba ma yin kamar yadda musulamai ke da ƙayyadadden lokacin sahur ko kuma lokacin buɗa-baki, da ka gama cin abincin dare ka yi barci za ka tashi da azuminka ne, kuma za ka iya zaɓar lokacin da ka ga dama ka yi buɗa-baki,'' in ji shi.

''Zan iya cewa akasarin Kirsitoci ba sa yin irin wannan azumin, amma kamar masu bin ɗarikar Katolika da Angalika da sauransu, sukan lura da wannan lokaci na Lent su yi azumi,'' ya ce.

''Kuma suna yi ne domin biyayya da kuma bin gurbin Yesu wanda kafin ya fara hidimarsa ta bushara ya ɗauki kwanaki 40 yana azumi, wanda Kiristoci kan yi gabanin bukukuwan Easter,'' ya kara fada.

Azumin mabiya addinin Kirista ɗin a cewar Rabaran John ya bambanta da na Musulmai ta hanyoyi da dama, musamman ma da yake ba kowa ne yake yin azumin ba a Kirstance, kuma waɗanda ke yi suna ɗaukar wa kan su iya lokuta da kuma kwanakin da suke son su yi azumin.

Malamin ya ce galibi Kiristoci kan ƙuduri yin azumi idan suna da wata buƙata da suke so Allah ya biya musu, kamar neman mijin aure, lafiya, gyara rayuwar iyali da ƴaƴa, da neman kariya ko kuma sauƙi daga aukuwar bala'o'i, da dai sauran buƙatu na rayuwa.

Wani bambancin da Rabaran ɗin ya bayyana wanda ke tsakanin azumin Musulmi da mabiya addinin Kirista ba sa bayyana cewa suna azumi kamar yadda Musulmi ke yi idan za su fara da kuma kammala azumin watan Ramadan ba.

''Littafin Bible ya koya mana cewa idan za mu yi ibada mu yi ta da a cikin zuciyarmu ba a bayyane ba don mutane su gani ba, amma duk da haka akwai Kiristoci da suka tallata azumi mukan faɗakar da su cewa wannan wani abu ne tsakanin mai bi da kuma Allah da bai kamata mu bayyana ba.''

Muhimman abubuwa shida da suka bambanta azumin Musulmi da Kirista

Sheikh Disina ya shaida ya yi wa BBC ƙarin bayani cewa akwai wasu muhimman abubuwa shida da suka bambanta azumin Musulmai da kuma na Kirista, kuma ya jero su kamar haka:

  • Azumin Musulmai na amfani da lissafin watan sama ko shekarar ƙamariyya, yayin da Kirstoci ke lissafi da shekarar miladiyya ko shekarar shamsiyya.
  • Musulmai na azumtar azumin watan Ramadan ne a duk shekara, yayin da Kiristoci ke azumtar watan Afrilu da kwana 10 na watan Mayu a kowace shekara.
  • Musulmai na azumtar kawana 29 ne ko 30, amma kiristoci suna azumtar darare 40 ne da yini 40 ko kuma kwana 40.
  • A Musulunci azumi dole ne ga baligi lafiyayye mazaunin gida, sannan ƙin yin azumi ga wanda ya wajaba a kansa yana iya warware Musuluncin mutum, amma a addinin Kirista yin azumi alama ce kawai ta nagartar bawa da cikakkiyar biyayyarsa ga Yesu Almasihu amma rashin yin azumi ba zai iya cire shi daga Kiristanci ko kuma a ce ya yi wani babban laifi ba.
  • Azumi a wurin Musulmai yana farawa ne daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana - mutum zai kame daga ci da sha tun daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana, yayin da su kuma Kiristoci azuminsu yana farawa ne daga cikin dare, daga zarar mutum ya yi barci sai kuma in Allah ya kai mu washegari in rana ta faɗi.
  • A addinin kirstanci an bayyana cewa ana so bawa ya ɓoye azuminsa hatta wa iyalansa, yayin da a Musulunci kuma azumi ibada ce ta gangami da jagoran Musulmai ke sanar da fara shi da kuma kare shi.