Dalilai shida da ke sa ƴan bindiga satar ɗalibai a Najeriya

Leah Sharibu na daga cikin ɗalibai mata da mayaƙan ISWAP suka sace a makarantar mata ta Dapchi a watan Maris ɗin 2018, kuma har yanzu ab a sako ta ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Leah Sharibu na daga cikin ɗalibai mata da mayaƙan ISWAP suka sace a makarantar mata ta Dapchi a watan Maris ɗin 2018, kuma har yanzu ab a sako ta ba
Lokacin karatu: Minti 6

Sace-sacen ɗalibai da aka yi a Najeriya cikin watan Nuwamban 2025 ya sake tuno wa al'ummar ƙasar wannan mummunar hanya da ƴan bindiga ke amfani da ita wajen cuzguna wa yara da iyayensu da kuma hukumomi.

Ƴan bindiga sun shiga makarantar St Mary's Catholic School da ke jihar Neja a ranar 20 ga wata, inda suka sace ɗalibai da malamai, waɗanda yawansu ya kai kimanin 300.

Hakan na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya bayan wasu ƴan bindigar sun kwashe yara 25 a makarantar sakandaren mata da ke garin Maga a jihar Kebbi.

Hukumomi sun karɓo yara 23 na jihar Kebbi bayan biyu daga cikinsu sun dawo tun daga farko, amma har yanzu waɗanda aka sace a jihar Neja na hannun waɗanda ke garkuwa da su.

Waɗannan sace-sace su ne na baya-baya, tun bayan na farko da ƙungiyar Boko Haram ta yi a watan Afrilun 2014, inda ta sace ɗalibai mata 276 a makarantar Chibok da ke jihar Borno.

Har yanzu, wasu daga cikin daliban da aka sace a shekarar ta 2014 a Chibok ba su koma hannun iyayensu ba.

Baya ga satar ɗaliban Chibok, ƙungiyoyin masu ɗauke da bindiga sun sace ɗalibai a makarantu da dama, kamar: Sakandiren mata ta Dapchi a jihar Yobe a 2018 da na Sakandiren Kankara a jihar Katsina a 2020, da Makarantar mata ta Jangebe a 2021, da Kuriga a jihar Kaduna da dai sauran su.

Mene ne abin da ke kwaɗaita wa ƴan bindiga ɗaukar irin wannan mataki na sace ɗalibai a makarantu?

BBC ta tuntuɓi Kabiru Adamu, wanda masani ne kan tsaro a yankin Sahel, inda ya ce dalilan da ƙungiyoyi ke amfani da su wajen satar ɗalibai a Najeriya sun dogara ne da ƙungiyar da ta aiwatar da satar.

Sai dai ya lissafa wasu daga cikin manyan abubuwan da ke sanya ƙungiyoyi aikata irin haka:

Kuɗin fansa/Musaya

Wadanda suka sace ɗalibai a makarantar gwamnati da ke Kuriga sun buƙaci a biya su maƙudan kuɗaɗe

Asalin hoton, NIGERIAN ARMY

Bayanan hoto, Wadanda suka sace ɗalibai a makarantar gwamnati da ke Kuriga sun buƙaci a biya su maƙudan kuɗaɗe
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kabiru Adamu ya ce abu na farko da ke haifar da ke ingiza ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai satar yara ɗalibai irin wanda ke faruwa a Najeriya shi ne domin yin musaya.

Ya bayyana cewa wannan ya kasu zuwa gida biyu: wato musaya domin karɓar wani nasu ko kuma musaya domin karɓar kuɗi.

Karɓar kuɗi

"Kusan dukkanin garkuwa da ɗalibai da aka yi a baya-bayan nan a Najeriya sai sun buƙaci wani abu, in ban da na Kebbi wanda gwamnati ta ce ba ta ba su komai ba," a cewar Kabiru Adamu.

Sai dai ya ce a yadda ya fahimci abin, niyyar ƴan bindigan ita ce domin su karɓi kuɗin fansa. Sai dai ya ce akwai lokutan da ƴan bindigar ke yin nasarar cimma manufarsu, a wasu lokutan kuma sukan samu akasain hakan.

Masanin tsaron ya bayar da misalin sace ɗaliban makarantar mata ta Chibok da ke jihar Borno, da na makarantar gwamnati ta Kuriga a jihar Kaduna, da kwashe ɗalibai da aka yi a jihohin Kebbi da Katsina "dukkaninsu an yi ne domin karɓar kuɗi," in ji masanin.

Hukumomin Najeriya sun sha musanta cewa suna biyan kuɗin fansa domin karɓo dalibai da aka sace daga makarantun gwamnati a ƙasar.

Musayar mutane

A ɓangaren musaya kuwa, Kabiru Adamu ya ce ƙungiyoyin da ke garkuwa da ɗaliban kan yi hakan ne domin "da niyyar cewa a sakar musu ƴan'uwansu wadanda gwamnati ta kama".

Sai dai masanin ya ce a wasu lokuta ƴan bindigar kan hada buƙatu biyu: wato a biya su kuɗi sannan kuma a sakar musu mutanen da aka kama.

Ya kuma bayyana cewa wata buƙata da irin waɗannan ƙungiyoyi kan gabatar - wadda ya ce ba a cika gani a Najeriya ba - ita ce neman a ba su magani idan wani daga cikinsu ba shi da lafiya.

Neman shahara

A lokacin da mayaƙan ISWAP suka sace ɗalibai mata a garin Chibok na jihar Borno, lamarin ya yadu a fadin duniya tamkar wutar daji.

Shahararrun mutane kamar uwargidar shugaban Amurka na wancan lokacin Michelle Obama da Hillary Clinton da sanannun mawaƙa irin su Angelina Jolie da Chris Brown sun yi tsokaci kan buƙatar ceto ɗaliban.

Wannan ya sanya sunan ƙungiyar da ta sace ɗaliban ya karaɗe duniya.

A cewar Kabiru Adamu irin wadannan ƙungiyoyi kan yi amfani da garkuwa da yara domin neman suna a duniya, wani abu da suke ganin zai ƙara musu tasiri.

Ya ƙara da cewa a wasu lokuta "yawan ɗaliban da suka sata na ƙara musu shahara a duniya."

Aƙida

Mayaƙan Boko Haram tare da Abubakar Shekau

Asalin hoton, Boko Haram

Akwai ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi waɗanda ke adawa da ilimin zamani, kamar Boko Haram, wadda ke ganin cewa bin wata doka baya ga ta addinin Musulunci 'kafirci ne'.

A cewar Kabiru Adamu, ƙungiyoyi masu irin wannan aƙida za su ga cewa nasara ce gare su idan suka kai hari a makarantun boko, domin kawo cikas ga abin da suke adawa da shi.

Rashin tsaro a makarantu

Makarantar gwamnati da ke Kuriga a jihar Kaduna

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Makarantar gwamnati da ke Kuriga a jihar Kaduna

Bayan satar ɗalibai da ta ɗauki hankalin duniya - na makarantar mata ta Chibok da ke jihar Borno - an ƙaddamar da wani shirin kare makarantu, wanda aka yi wa laƙabi da 'safe school initiative'.

Shirin ya samu goyon baya daga ƙungiyoyin tallafi na duniya tare da kuɗi daga gwamnatin tarayya da na jihohi.

Sai dai duk da haka makarantu sun ci gaba da kasancewa sakaka, ba tare da isasshen tsaro ba, lamarin da ya kai ga ci gaba da sace ɗalibai a lokuta daban-daban.

Kabiru Adamu ya ce "makarantu ba su da ingantacciyar kariya ko da an kawo musu hari".

Ya bayyana cewa akasarin makarantu a Najeriya ba su da tsaron da za su iya hana ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai afka musu, wanda hakan ya sanya suka zama wuri mai sauƙi da za a iya kai wa hari domin ɗaukar hankalin hukumomi da ma duniya.

Cimma burin yaƙi/ɗaukar matasa aiki

Kabiru Adamu ya ce sace ɗalibai na daga cikin dabarun da ake amfani da su wajen samun nasarar yaƙi, wanda ya kira "Psychological warfare'.

Tsari ne da ya ƙunshi yin amfani da farfaganda da cusa wani abu a tunanin al'umma domin sauya ra'ayi ko tursasa wa abokin gaba nuna gazawa ko kuma miƙa wuya.

Adamu ya kuma ce daga abin da suka gani a Najeriya wani lokaci ƙungiyoyin ƴan bindiga na amfani da irin wannan tsari wajen ɗaukar yara aiki, inda ya bayar da misali da satar ɗaliban Chibok da kuma na Kuriga.

Ko ƙungiyoyin da ke satar ɗalibai a Najeriya sun cimma burinsu?

Kabiru Adamu ya ce a wani ɓangare za a iya cewa ƙungiyoyin da ke sace ɗalibai a Najeriya ba su cimma burin da ya sa suke yin satar ba.

"Idan ka yi amfani da mizani, kan masu ƙoƙarin yaƙi da ilimin nasara, ai har yanzu ana ci gaba da karatun Boko, saboda haka ba su cimma burinsu ba a wannan ɓangare.

"A ɓangaren satar jama'a domin kudin fansa za ka cewa a lokuta da yawa ba su samun nasarar karɓar kuɗin.

"Za ka ga sun yi satar, amma ba su samun karɓar kuɗaden, haka nan ma sauran ɓangarorin," in ji Kabiru Adamu.

Sai dai wasu masana na ganin cewa tasirin da irin wannan sace-sacen dalibai ke yi ga ilimi na da matuƙar muni.

Tun bayan satar dalibai a baya-bayan nan, jihohi da dama har ma da gwamnatin tarayyar Najeriya sun sanar da rufe makarantu a sassan ƙasar.

Jihohi irin su Katsina da Kebbi da Neja da Zamfara duk sun sanar da rufe makarantu, yayin da ita kuma gwamnatin tarayya ta sanar da rufe makarantun haɓɓaka haɗin kan al'umma da ke wasu sassan ƙasar.