Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buƙatu 7 da ke sa ASUU shiga yajin aiki
Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya, ta ASUU, ta mayar da kakkausan martani ga gwamnatin kasar, bayan ta zargi ministan ilimi, Dokta Tunji Maruf Alausa, da yin wasu bayanai masu cike da kura-kurai, dangane da batun cika alkawuran da gwamnati ta yi a yarjejeniyoyin da ta kulla da ma'aikatan jami'o'in kasar.
Kungiyar ta ASUU ta ce har yanzu romon baka kawai gwamnatin kasar ke yi wa ma'aikatan jami'o'i.
Ga dukkan alamu dai har yanzu tana kasa tana dabo, dangane da ja-in-jar da ke tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar malaman jami'o'in kasar, ta ASUU.
Rahotanni sun ambato ministan ilimi na Najeriya, Dakta Tunji Maruf Alausa, na cewa, gwamnatin tarayya ta cimma nasarori cikin alkawuran da ta daukar wa ma'aikatan jami'oin, kamar fara biyan kudaden shirin nan na tallafa wa ma'aikatan manyan makarantun kasar, da biyan bashin wasu alawus-alawus na malaman jami'o'i, da dai sauransu.
To sai dai kungiyar malaman jami'o'in ta ce ba ta gani a kasa ba.
Farfesa Ibrahim Tajo Suraj, shi ne shugaban reshen kungiyar na jami'ar Bayero ta Kano, ya shaida wa BBC cewa sun ji maganganun da ministan ya yi to amma duk alkawuran da ya ce an cika wa malama jami'oi su dai ba su gani ba.
Ya ce," Sannan maganar sabunta yarjejeniya ma har yanzu ba a sabunta ba, haka batun biyanmu albashin na wata uku da rabi har yanzu shiru haka batun karin girma ma ba a yi ba, ariya-ariya ma ba a biya ba kai abubuwa da dama babu abin da muka gani, amma kuma sai gashi minista ya zo ya ce duka an biya, abubuwa kalilan ne gwamnati ta iya yi shi ma ba duka ba."
Buƙatun ASUU bakwai
Shugaban ƙungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU) reshen Jami'ar Bayero ta Kano (BUK), Farfesa Ibrahim Tahir Suraj, ya bayyana irin buƙatun da ASUU ke nema daga gwamnatin tarayya yayin tattaunawa da BBC.
Ya ce ƙungiyar ta jima tana neman gwamnati ta biya hakkokinta da sauran buƙatu da suka haɗa da:
- Sabunta yarjejeniyar shekarar 2009: ASUU na son gwamnati ta sabunta yarjejeniyar da aka cimma tun 2009, wadda ta shafi yadda ake gudanar da ayyukan jami'o'i da yanayin aiki da kula da koyarwa. Wannan yarjejeniya ta haɗa da batutuwan zamantakewar ɗalibai da ikon jami'o'i su gudanar da harkokinsu ba tare da tsoma bakin gwamnati ba wato da bai cin gashin kansu kenan.
- Bayar da kuɗaɗen gudanarwa ga jami'o'i: Ƙungiyar na buƙatar gwamnati ta riƙa ba da kuɗaɗen gudanarwa na jami'o'i domin a inganta:Azuzuwa da ɗakunan gwaje-gwaje da ɗakunan ɗalibai da asibitocin jami'o'i da kuma ɓangaren wasanni. ASUU na ganin wannan zai inganta karatu da bincike a jami'o'in ƙasar.
- Biyan su haƙƙinsu na aikin da suka yi a baya na wata uku da rabi: Malaman jami'a sun ce suna da haƙƙin albashi na wata uku da rabi da suka yi aiki amma ba a biya su ba. ASUU na so gwamnati ta biya wannan bashin nan da nan.
- Biyan su cikon ƙarin albashin da aka yi wa malaman jami'a: Ƙungiyar na neman a biya cikon ƙarin albashin da aka yi wa malaman jami'a fiye da shekara guda da ta wuce, wanda ba su ne suka nema ba amma gwamnati ta kasa cikawa.
- Tabbatar da an tura kuɗaɗensu da ake cirewa daga albashinsu zuwa ƙungiyoyinsu: ASUU ta bayyana cewa ana cire wasu kuɗaɗe daga albashin malaman da ake cewa za a tura su zuwa ƙungiyoyinsu amma har yanzu ba a tura ba. Wannan na haifar musu da matsala wajen biyan bukatunsu da suka dogara da wadannan kungiyoyi.
- Biyan ƙarin albashi ga malaman da aka ƙara musu muƙami: Wasu malaman da aka ƙara musu muƙami a jami'o'i sun ce har yanzu ba a biyasu ƙarin albashin da ya zo da sabon muƙaminsu ba, don haka ASUU na so gwamnati ta biya su bisa sabon matsayin da suke kai yanzu.
- Dakatar da korar ma'aikatan jami'o'i ba bisa ƙa'ida ba: ASUU ta nemi gwamnati ta dakatar da korar ma'aikata haka kawai, wanda shugaban ya kira da "victimization"
Kungiyar malaman jami'o'in ta ASUU dai tana ta kokantawa cewa, tun shekara ta 2009 take zama tana kulla yarjejeniyoyi da gwamnatin tarayya, amma har yanzu jifa ba ta dace da waiwaye ba, dangane da aiwatar da su yadda suka kamata.
Hakan ne kuma ke ta haddasa yaje-yajen aikin malaman jami'o'i a kasar.
Kungiyar ta ASUU dai na son gwamnatin tarayya ta cika mata alkawura da dama ciki har da batun sabunta yarjejeniyar da aka cimma tun 2009, wadda ta shafi yadda ake gudanar da ayyukan jami'o'i da yanayin aiki da kula da koyarwa.
Wannan yarjejeniya ta haɗa da batutuwan zamantakewar ɗalibai da ikon jami'o'i su gudanar da harkokinsu ba tare da tsoma bakin gwamnati ba wato da bai cin gashin kansu kenan.
Kazalika ASUU na son gwamnati ta Bayar da kuɗaɗen gudanarwa ga jami'o'i da Biyan su haƙƙinsu na aikin da suka yi a baya na wata uku da rabi da Biyan su cikon ƙarin albashin da aka yi wa malaman jami'a.
Sauran bukatun da ASUU ke son gwamnati ta biya musu su ne Tabbatar da an tura kuɗaɗensu da ake cirewa daga albashinsu zuwa ƙungiyoyinsu da Biyan ƙarin albashi ga malaman da aka ƙara musu muƙami da kuma Dakatar da korar ma'aikatan jami'o'i ba bisa ƙa'ida ba.