Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Trump ya ɗora wa Ukraine laifin ɓarkewar rikicinta da Rasha
- Marubuci, Bernd Debusmann
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, in Palm Beach, Florida
- Lokacin karatu: Minti 6
Donald Trump ya mayar da martani ga shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, bayan da ya ce ya ji mamakin cewa ba a gayyaci ƙasarsa zuwa tattaunawa kan kawo karshen yaƙinsu da Rasha a Saudiyya ba.
Trump ya ce abin takaici ne irin martanin da Ukraine ta yi, ya kuma ɗora laifin fara yaƙin kan Ukraine, inda ya ce da ƙasar ta cimma yarjejeniya tun da farko.
Mamayar da Rasha ta yi kan Ukraine ya janyo ɓarkewar faɗa da aka shafe tsawon shekara uku ana gwabzawa.
Tun da farko ranar Talata, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya haɗu da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio a Riyadh domin tattaunawar fuska da fuska karon farko tsakanin ƙasashen biyu tun bayan mamayar, sun amince su kafa kwamitoci don fara tattaunawar kawo karshen yaƙin.
Lavrov ya ce ƙasarsa ba za ta amince da kasancewar dakarun wanzar da zaman lafiya daga ƙasashen Nato ba a Ukraine a duk wata yarjejeniyar zaman lafiya, wani kuduri da aka fito da shi a zama da ƙasashen Turai mambobin Nato suka yi a Paris ranar Litinin.
Ƙasashen Nato, waɗanda suke da burin ci gaba da taimakawa Ukraine a yaƙinta da Rasha, suna ci gaba da jin mamakin yadda Trump ba ya saka su cikin yarjejeniyar samar da zaman lafiya, ba kamar yadda wanda ya gada Joe Biden yake yi ba.
Zelensky ya zargi tawagar Rasha da ta halaraci tattaunawa a Riyadh da yin karya, inda ya ƙara da cewa Rasha ba abin yarda bane kuma dole a tilasta mata don samun zaman lafiya.
Da yake tattaunawa da manema labarai a gidansa na Mar-a-Lago, BBC ta tambayi Trump kan sakon da yake da shi ga ƴan Ukraine da suke jin cewa an yaudare su.
"Na ji cewa suna ɓacin rai saboda ba a gayyace su wajen tattaunawa ba, suna da kujera na tsawon shekara uku kafin yanzu. Wannan batu ne da za a warware cikin sauki," in ji shi.
"Da ba ku fara yaƙin nan ba. Da kun cimma yarjejeniya," in ji Trump.
"Da ni ne da na nema wa Ukraine mafita," in ji shi. "Watakila da hakan zai saka su mallaki dukkan yankin, komai - kuma babu wanda za a kashe, sannan babu birnin da za a lalata.
Bayan tattaunawar a Riyadh, Trump ya ce "yana cike da ƙwarin gwiwa".
"Tattaunawar mai kyau ce," in ji shi. "Rasha na son yin wani abu. Suna son dakatar da mummunan abu da ake yi."
"Ina tunanin ina da ikon kawo karshen wannan yaƙi," in ji shugaban na Amurka.
Trump ya kuma soki tsawon lokaci da aka ɗauka ba a sake yin zaɓe a Ukraine ba, lokacin da aka tambaye shi ko Amurka za ta goyi bayan Rasha kan ganin a yi zaɓe.
"Suna son samun wakilci... amma shin ƴan Ukraine ba za su iya fita su faɗi ra'ayinsu bane? an ɗauki tsawon lokaci ba a yi zaɓe ba," kamar yadda shugaban ya faɗa.
Ya kuma yi iƙirarin cewa Zelensky - wanda ya lashe zaɓe na tsawon shekara biyar a 2019 - ya rasa kashi huɗu na magoya baya.
Zelensky ya ci gaba da riƙe iko yayin da ƙasar da take karkashin dokoki na tsarin mulkin soja bayan ɓarkewar faɗa. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ya nuna cewa kashi 52 na ƴan Ukraine sun yarda da Zelensky.
A ɗaya gefen, yayin da aka tambayi Trump kan yiwuwar ƙasashen Turai su aika dakarunsu zuwa Ukraine, ya ce: "Idan suna son yin hyaka, abu ne mai kyau, ina goyon baya."
Sai dai ya ce ba mai yiwuwa ba ne Amurka ta tura dakarunta zuwa Ukraine, saboda suna da nisa da can.
Bayan tattaunawar da aka yi a Paris ranar Litinin, Firaiministan Birtaniya Sir Keir Starmer ya ce duk wata yarjejeniyar zaman lafiya a Ukraine zai buƙaci Amurka ta dakatar da Rasha daga sake far wa Ukraine.
Sir Keir ya ce "Ba da tsaro daga wajen Amurka shi ne hanya ɗaya tilo da zai dakatar da Rasha far wa Ukraine", kuma ya sha alwashin tattauna muhimman batutuwan yarjejeniyar zaman lafiya da Trump a mako mai zuwa a Washington.
A tattaunawar da aka yi a Riyadh, manyan jami'ai sun samu halarta kamar jakadan Amurka a Gabas Ta Tsakiya da babban mai ba da shawara kan tsaro na Amurka Mike Waltz da jami'in shugaban Rasha Yury Ushakov da kuma shugaban asusun kuɗi na Rasha Kirill Dmitriev.
Moscow ta ce ba za ta amince da girke dakarun wanzar da zaman lafiya ba daga ƙasashen Nato karkashin duk wata yarjejeniya, a cewar Lavrov.
Ya ce Amurka da Rasha za su naɗa jakadoji zuwa ƙasashen juna ba da jimawa ba, da kuma saka ka'idoji domin mayar da haɗin kai.
"Tattaunawa ce mai muhimmanci. Mun saurari juna da kuma abin da aka faɗa," in ji ministan harkokin wajen Rashan.
Ya sake nanata matsayarsu ta baya na cewa duk wani yunkuri na faɗaɗa tsaron Nato - kuma Ukraine ta shiga ciki - hakan zai zama babban barazana kai-tsaye ga Rasha.
A ɓangaren Rubio ya ce yana gamsu cewa Rasha na son shiga tattaunawar da za ta kawo karshen yaƙi.
"Yau rana ce ta farko mai tsawo kuma mai wahala, amma mai muhimmanci", in ji shi.
Ya ce Tarayyar Turai za ta shiga cikin tattaunawar nan gaba saboda suna da takunkumai da suka kakaba.
A kan rashin kasancewar Ukraine a taron, ya ce hakikance cewa babu wanda aka ware.
"Ana damawa da kowaye da ke cikin wannan rikici, ya kamata su amince da hakan," in ji Rubio.
Tattaunawar da aka yi a Paris, wanda aka shirya don martani kan sake kiran Rasha zama da Amurka ta yi karkashin Trump, bai cimma wata matsaya ba.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce bai kamata a tattauna batun tura dakaru Ukraine ba a bainar jama'a.
Firaiministan Poland Donald Tusk shi ma ya ce bai shirya aika dakaru ba yayin da takwararsa ta Italiya Giorgia Meloni - wadda ita ce kaɗai shugabar da ta halarci rantsar da Trump a Turai - ta nuna shakku.
Ta faɗa wa taron cewa aika dakaru daga Turai zai zama hanya mai tsarkakiya ta samar da zaman lafiya a Ukraine.
An ga shugaban Ukraine cikin gajiya da kuma damuwa lokacin da ya ba da martaninsa kan tattaunawar da ake yi a Saudiyya a wani taron manema labarai a Turkiyya.
"Muna son a yi komai cikin adalci saboda kar wani ya ɗauki mataki a bayan mu," in ji Zelensky.
"Ba za ka yanke shawara ba ba tare da Ukraine ba kan hanyar kawo karshen yaƙin Ukraine."
Yana sane cewa ba shi da wani iko mai karfi da zai sauya duk wani abu da aka amince da shi.
Shugaban na Ukraine ya kuma san cewa ƙasarsa ba za ta iya nuna turjiya ba, har ma ga shan galaba kan dakarun Rasha - muddin ba tare da taimakon Amurka ba.
Lokacin da aka hamɓarar da shugaban Ukaine da ke goyon baya a 2014, Moscow ta ayyana yankin Crimea a matsayin ɓangarenta da kuma marawa ƴan aware masu goyon bayan ƙasar a wani kazamin faɗa a gabashin Ukraine.
Rikicin ya rikiɗe zuwa babban yaƙi lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairun 2022.
An daƙile yunkurin Moscow na karɓe iko da Kyiv, babban birnin Ukraine, sai dai dakarun Rasha sun karɓi iko da kashi ɗaya bisa biyar na yankin ƙasar a gabas da kuma kudanci, kuma ta kai hare-hare ta sama a faɗin ƙasar.
Ukraine ta mayar da martani ta hanyar kai harin makaman atilari da kuma na jirage marasa matuki, har da kaddamar da farmaki ta ƙasa kan yankin Kursk na Rasha da ke yammaci.
Da wuya a faɗi ainihin alkaluman waɗanda yaƙin ya shafa, amma an kiyasta cewa an kashe da kuma jikkata dubun-dubatar mutane, yawanci sojoji, sannan miliyoyin fararen hula daga Ukraine sun tsere.