Yankunan da Rasha ta mamaye a Ukraine tun bayan ƙaddamar da samame

    • Marubuci, By the Visual Journalism Team
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shekara uku ke nan ana gwabza yaƙi tun bayan da Rasha ta ƙaddamar da gagarumin samamenta a kan Ukraine. Rasha ta ci gaba da faɗaɗa yankunan da take iko da su a cikin Ukraine musamman a shekara ɗaya da ta gabata, sai dai su ma dakarun Ukraine sun taɓuka abin da za su iya inda suka samu nasarar kutsawa zuwa cikin wasu yankuna na Rasha.

Ga bayani a taƙaice kan yadda al'amura suka kasance a ƙasar ta Ukraine.

Yayin da za a cika shekara uku cif da fara samamen Rashar a Ukraine ranar 24 ga watan Fabarairu, sabon shugaban Amurka, Donald Trump ya ce shugaban Rasha Vladimir Putin ya amince a fara tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin.

Wannan na zuwa ne yayin da dakarun Rasha ke ci gaba da samun nasara wajen faɗaɗa samamen da take a yi Ukraine tamkar wutar daji.

Rasha na dannawa ta ɓangaren gabas

A gabashin Ukraine, dakarun Rasha na dannawa suna ƙwace yankuna taƙi bayan taƙi a yankin Donbas, inda suke mamaye garuruwa da ƙauyuka.

Babban abin da Rasha ke cin gajiya shi ne yawan dakarunta, inda a shirye take ta baza sojojinta a yankunan Ukraine a duk lokacin da take son ta mamaye wani yanki.

Masana a Cibiyar nazarin yaƙe-yaƙe sun bayyana cewa suna ganin dakarun Rasha za su mayar da hankali wajen ƙwace biranen da ke kusa da fagen daga a lokacin sanyi - a baya-bayan nan sun ƙwace garin Kurakhove kuma suna ci gaba da dannawa zuwa arewa maso gabas, zuwa yankin Pokrovsk.

Mamayar da Rasha ta yi zuwa yankin birnin Pokrovsk shi ne mafi shahara a baya-bayan nan a ɓangaren Donestsk, to sai dai dabarun da sojojin Ukraine suka yi amfani da su ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa da dakarun ƙasa ya taƙaita samamen na Rasha.

An kwashe kimanin shekara ɗaya kafin sojojin Rasha su samu damar matsawa kimanin kilomita 40 ta yammaci - an tursasa wa Ukraine janyewa daga Avdiivka, da ke arewacin Donestsk a Fabararirun 2024, bayan shafe watanni ana gwabza faɗa.

Kusan ɗaukacin al'ummar Avdiivka sama da 30,000 sun tsere daga garin, inda ya zamo tamkar kufai da aka dagargaza.

Kutsawar Rasha a arewacin Kharkiv

Baya ga kutsen da ta yi ta gabashi, Rasha ta ƙaddamar da wani samame ta arewacin birnin Kharkiv a watan Mayun 2024. Ta ƙwace ƙauyuka da dama sannan fararen hula da dama sun watse.

Ƙaimin da Rasha ta sanya wajen samamen ya faru ne a ƙarshen wata huɗu da Amurka ta daina tura wa Ukraine makamai sanadiyyar turkaturkar da ta wanzu a majalisar dokokin Amurka, wanda aka warware a watan Afrilu.

Dakarun Ukraine sun dage sosai, kuma duk da cewa Rasha ta yi amfani da makamai masu linzami wajen kai hari a kan Kharkiv, birnin ya yi nisa ga makaman atilare na Rashar.

Ukraine ta bayar da shawarar yin musayar yankuna

Gabashin Ukraine yanki ne da aka riƙe takaddama a kansa tun cikin 2014, lokacin da Rasha ta ƙwace iko da yankuna masu girma na gabashin Donetsk da Luhansk.

A wannan lokaci Rasha ta riga ta ƙwace iko da yankin kudancin Crimea a Fabarairun 2014, kafin karɓe shi baki ɗaya.

Trump ya bayyana cewa zai yi wahala a sake mayar wa Ukraine yankunanta kamar yadda suke kafin shekarar 2014, to amma lokacin da ya amsa tambaya daga BBC, Trump ya ce "za a dawo da wasu daga cikin yankunan".

A wata tattaunawa da aka wallafa a jaridar The Guardian ranar 11 ga watan Fabarairu, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce za a iya yin musayar yankunan da Rasha ke riƙe da su a Ukraine da yankunan da Ukraine ta ƙwace a yankin Kursk da ke yammacin Rasha a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar samar da zaman lafiya.

Ukraine ta ƙwace iko da wani ɓangare na yankin ne lokacin da ta ƙaddamar da wani samame na ba-zata a watan Agusta, inda ta nausa har kilomita 30 zuwa cikin ƙasar Rasha.

Rasha ta kwashe mutanenta kimanin 200,000 daga yankin, sannan Putin ya yi alla-wadai da lamarin tare da bayyana shi a matsayin 'gagarumin tsokalar faɗa'.

Bayan mako biyu da samamen, babban hafsan sojin Ukraine ya yi iƙirarin cewa ƙasarsa tana iko da yanki mai girman sama murabba'in kilomita 1,200 da ƙauyuka 93 a cikin Rahsa.

Rasha ta samu nasarar sake ƙwace wani ɓangare na yankin, sai dai har yanzu akwai dakarun Rasha a yankin na Kursk.

Dmitry Peskov, wanda shi ne mai magana da yawun shugaba Vladimir Putin ya bayyana shawarar Zelensky ta yin musayar yankuna a matsayin "abin da ba zai yiwu ba".

Shekaru uku na samamen Rasha

Samamen Rasha ya fara ne lokacin da ta ƙaddamar da hare-haren makami mai linzami kan biranen da ke faɗin Ukraine da asubahin ranar 24 ga watan Fabarairun 2022.

Daga nan ne dakarun Rasha suka danna ta ƙasa cikin hanzari, inda a cikin makonni kaɗan suka ƙwace iko da yankuna da dama a cikin Ukraine sannan kuma suka danna zuwa kusa da Kyiv, babban binrin ƙasar.

Sai dai dakarun Rasha sun ci karo da turjiya mai ƙarfi daga Ukraine a kusan duk ɓangarorin ƙasar, lamarin da ya haifar musu da cikas.

Haka nan sojojin Rasha sun kasance ba su da ƙwarin gwiwa, kuma sun yi fama da ƙarancin kayan aiki da abinci da kuma ruwan sha.

Ukraine ta kuma gaggauta amfani da makaman da ta samu gudumawa daga ƙasashen yammacin duniya, kamar makamin tarwatsa tankokin yaƙi na Nlaw, wanda ya yi amfani sosai.