Bayern na nazari kan Rashford, Arsenal ta kusa kammala cinikin Gyokeres

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gaban Manchester United da Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, bayan ta yi amanna da hazaƙar da ya nuna a zaman aron da ya yi a Aston Villa a kakar da ta gabata. (Sun)
Arsenal na dab da ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan gaba na Sporting Viktor Gyokeres. Ɗan ƙasar Sweden mai shekara 27 ya shaidawa kulob ɗinsa cewa yana son ya koma Gunners. (L'Equipe)
Crystal Palace ta cimma yarjejeniya kan farashin fam miliyan 47 don siyan Ousmane Diomande, mai shekara 21, daga Sporting, inda ake ganin ɗan wasan baya na Ivory Coast zai iya maye gurbin ɗan wasan Ingila Marc Guehi mai shekara 24 . (A Bola)
Manchester United ta tuntuɓi Inter Milan game da cinikin ɗan wasan Italiya Davide Frattesi, mai shekara 25. (Caught Offside)
Arsenal ta gabatar da tayi kan ɗan wasan Ingila Noni Madueke, mai shekara 23, wanda ake ganin wataƙila ya bar Chelsea a bazara. (Sky Germany)
Juventus na dab da ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan gaban Canada Jonathan David, mai shekara 25, wanda kwantiraginsa da Lille ya ƙare a ƙarshen kakar wasan da ta gabata. (Fabrizio Romano)
Ɗan wasan Colombia Jhon Duran, mai shekara 22, ya tashi daga ƙasarsa zuwa Turkiyya domin kammala yarjejeniyar zaman aro daga Al-Nassr ta Saudiyya zuwa Fenerbahce. (Athletic)
AC Milan na fatan ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Switzerland Ardon Jashari, mai shekara 22, daga Club Brugge kan farashin da ya kai kusan fam miliyan 30. (La Gazzetta dello Sport)
Newcastle na zawarcin ɗan wasan bayan Marseille da Argentina Leonardo Balerdi, mai shekara 26, wanda kuma ke jan hankalin Juventus. (Mail)
Burnley na ƙoƙarin farauto ɗan wasan gaba da kocinta Scott Parker ke buƙata, inda ta sanya ido kan ɗan wasan Genk daNajeriya Tolu Arokodare, mai shekara 24. (Telegraph)
Manchester City za ta ɗauki Caelan-Kole Cadmarteri mai shekara 15 daga Sheffield Wednesday a kan farashin fam miliyan 1.5. (Mail)
West Ham na ƙoƙarin shawo kan Slavia Prague don ta sallama ma ta da ɗan wasan bayan Senegal El Hadji Malick Diouf, mai shekara 20. (Guardian)











