Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasashen Afrika ba su da godiyar Allah - Macron
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce har yana jiran ƙasashen yankin Sahel su gode wa asarsa bisa taimakon su da ta yi wajen kauce wa faɗawa hannun mayaƙa masu iƙirarin jihadi, kuma ya yi watsi da cewa an tilasta wa ƙasarsa ficewa daga yankin.
Macron ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin jawabi ga jakadun ƙasar a wajen taro kan harkokin waje na shekarar 2025, inda ya ce Faransa ta yi daidai wajen shiga tsakani a 2013 domin yaƙi da masu iƙirarin jihadi, koda kuwa waɗannan ƙasashe sun daina dogaro da taimakon soji na ƙasar.
"Ina ganin sun manta ba su yi mana godiya ba, amma babu komai, lokaci na nan zuwa," kamar yadda Macron ya faɗa cikin shaguɓe.
A baya-bayan nan sojojin Faransa sun fice daga Mali da Nijar da kuma Burkina Faso bayan juyin mulki a waɗannan ƙasashe, kuma suna kan hanyar ficewa daga Chadi da Senegal da kuma Ivory Coast.
"Babu wani daga cikinsu da zai samu ƙasa mai ƴanci idan da a ce ba a tura sojojin Faransa zuwa yankin ba," in ji Macron.
Macron ya kuma yi watsi da batun cewa an tursasa wa Paris fita daga yankin na Sahel, inda ya ce sun yanke shawarar sake tsari.
"Ba haka ba ne, Faransa ba ta samun koma-baya a Afrika, kawai dai mun ɗauki aniyar sake shiri," in ji shi.
Martanin ƙasashen Afirka
Tuni da wasu ƙasashen suka fara mayar wa shugaban na Faransa martani game da kalaman nasa.
Ministan harkokin waje na Chadi, Abderaman Koulamallah ya ce "Ƙasashen Afirka, ciki har da Chadi sun taka muhimmiyar rawa wajen ceto Faransa a lokacin yaƙe-yaƙe na duniya, wani abu da har yanzu Faransa ba ta yi godiya akansa ba."
Ya ƙara da cewa "Wajibi ne shugabannin Faransa su martaba al'ummar Afirka su kuma ga girman sadaukarwar da suka yi".
Haka nan ministan na Chadi ya zargi Faransa da fakewa da shirye-shiryenta a Afirka wajen kare muradunta a maimakon taimakon ƙasashen da take hulɗa da su.
Ya ce "gudunmawar Faransa ya taƙaita ne kawai ga wuraren da take da wata manufa a kai" yayin da Chadi take fama da matsaloli na ruɗanin siyasa da yaƙin basasa da masu tayar da ƙayar baya a tsawon shekara 60 na alaƙar soji da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Cote d'Ivoire dai ta zamo ƙasa ta baya-bayan nan da ta umarci dakarun Faransa su fice daga cikinta bayan Chadi da Senegal.
Firaministan Senegal Ousman Sonko ya yi watsi da iƙirarin da Macron ya yi kan cewa Faransa ta fice daga ƙasashen ne bayan tattaunawa tsakaninsu, inda ya ce Senegal ta ayyana korar Faransa ne ba tare da an guidanar da wata tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu ba.
Ya ce "Har yau ɗin nan babu wata tattaunawa tsakaninmu, kuma Senegal ta ɗauki matakin korar Faransa ta yi ne don ƙashin kanta a matsayinta ta ƙasa mai ƴanci."
Ya kuma yi watsi da batun cewa Faransa ta taimaka wa ƙasashen Afirka zama masu ƴanci.
Sonko ya ce "Ya kamata kowa ya sani cewa Faransa ba ta da ƙarfi ko ikon tabbatar da tsaro ko ƴancin ƙasashen Afirka.
Ya kumja zargi Faransar da ruruta wutar rikici a wasu ƙasashen Afirka, ciki har da Libya.