Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa ake wahalar ruwan sha a cikin birnin Kano?
Al'ummar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, musamman cikin birnin jihar ana fuskantar matsalar karancin ruwa sha, lamarin da ke tilastawa magidanta sayen ruwa daga masu tura kurar ruwa.
Magidantan na ci gaba da kokawa kan tsadar ruwan shan da masu kurar ruwa ke sayarwa, inda a yanzu farashin kowacce jarka daya yake kamawa daga naira 100 zuwa 150.
Unguwanni da dama suna fama da matsalar ruwan, inda wasu suka shafe lokaci mai tsawo ba tare da samun ruwan fanfo ba.
Ga alama a iya cewa jama'a a cikin birnin Kano sun shiga halin rashin tabbas saboda yadda ruwan sha ke neman ya gagaresu.
Bayanan da BBC ta tattaro na cewa unguwannin cikin birnin Kano da dama ne suka jima ba su ga ruwan fanfo ba, wasu kuwa ana samu jifa-jifa.
Magidanta da dama da BBC ta zanta da su a wasu unguwannin cikin birnin Kano, sun nuna yadda suke shan wahalar ruwan da kuma tsadarsa.
Wani magidanci da BBC ta tattauna da shi ya ce, " Muna cikin matsanancin rashin ruwa a cikin gari domin rabon mu da muga ruwa fanfo tun lokacin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau."
A yankin Jan-Bulo ma haka matsalar take, inda wani magidancin ya koka da cewa al'amarin na neman ya fi karfin jama'a.
Ya ce," Sama da shekara 20 ba mu da ruwan fanfo, abin da yawancin jama'a ke amfani da shi wajen samun sha shi ne rijiyar burtsatsai."
Wani wurin da ke kofar Nasarawa a karamar hukumar Birni, na daga cikin wuraren da masu baro ke sayen ruwan suna sayarwa jama'a musamman a unguwannin da ke fama da matsalar ruwan da ke kusa.
Wani mai kurar ruwa da ke sayar ruwan ya shaida wa BBC cewa suna sayen ruwan kura guda akan Naira 300, sannan kuma suna sayarwa jama'a akan naira 1000.
Jihar Kano mai madatsun ruwa da dama da kuma yawan jama'a, matsalar karancin ruwan sha kuma tsaftacce na ci wa al'ummar birni da kauye tuwo a kwarya, inda masu lura da al'amura ke ganin muddin hukumomi a jihar suna son magance matsalar dole a samar da kayan aiki da bin diddigi da kuma yi wa ma'aikatu da manufofin gwamnati garambawul.