Ko kun san illar yawa ko ƙarancin shan ruwa ga lafiyar ɗan'adam?

Lokacin karatu: Minti 5

Ruwan sha na da matuƙar muhimmanci ga rayuwa. Hukumomin Duniya da dama sun bayar da shawarar cewa mata su riƙa shan aƙalla lita biyu na ruwa a kowace rana yayin da aka buƙaci maza su riƙa shan lita biyu da rabi.

To sai masana kimiyya na cewa ruwan da buƙa buƙatar sha ya danganta da wasu dalilai.

Rashin shan wadataccen ruwa kan haifar da rashn ruwa a jiki, to sai dai shan ruwan da yawa kuma kan zama matsala.

Ruwa shi ke samar da kashi 60 cikin 100 na nauyin jikinmu, yakan shiga cikin ƙwayoyin halitta da gaɓoɓi da jini da kuma hanyoyi masu yawa na jikinmu.

''Ruwa babban sinadari ne'', in ji Dakta Nidia Rodriguez-Sanchez, ƙwararriya a fannin nazarin matsalolin rashin ruwa a jikin ɗan'adam da ke Jami'ar Stirling da ke Scotland.

"Mukan mayar da hankali wajen nau'ikan abinci masu gina jiki da masu bayar da kariya da masu ƙara kuzari da masu ɗauke da sinadarn narkar da abinci, amma ba ma tunani game da ruwan sha wanda kuma shi ne ke ɗauke da muhimman sinadaran rayuwarmu.''

Ruwan sha kan taka muhimmiyar a kusan kowane aiki da jikinmu ke yi.

Makarantar nazarin kiwon lafiya da ke Havard ta ce wasu daga cikin aikin da ruwa ke yi ya haɗa da:

  • Kai sinadarai da iska ga ƙwayoyin halitta
  • Wanke ƙwayoyin cuta daga mafitsara
  • Taimaka wa narkar da abinci
  • Kariya daga matsalolin ba-haya
  • Daidaita hawan jini
  • Taimaka wa motsin gaɓoɓi
  • Bai wa sassan jiki da tsoka kariya
  • Daidaita zafin jiki

Me zai faru idan ba ku sha isasshen ruwa ba?

Galibi ruwa kan ƙare a jikinmu saboda zufa da muke fitarwa, da fitsari da kuma numfashi.

Domin ci gaba da aiki yadda ya kamata akwai buƙatar maye gurbin ruwan da ake rasawa sanadiyyar waɗannan abubuwa, wani abu da a kimiyyance ake kira ''daidaita ruwa ''

Idan ruwan da muke fitarwa ya fi wanda muke sha yawa, to za a samu rashin ruwa a jikinmu.

Kuma hakan zai haifar da manyan matsalolin lafiya masu yawa.

Alamomin rashin ruwa a jikin ɗan'adam

  • Fitsari mai launin ruwan ɗorawa mai warin gaske
  • Ƙarancin fitsari yadda ya kamata
  • Jin kasala ko ganda
  • Yawan jin gajiya
  • Bushewar baki da laɓɓa da harshe
  • kwarmin idanu

A lokuta da dama, rashin ruwa a jiki kan haifar da rashin tabbas, yawan bugun zuciya, da kuma ciwo gaɓoɓi a cewa hukumar Lafiya ta Duniya. (WHO).

Idan shan ruwa ya yi yawa zai zama matsala?

Ƙwarai kuwa - kuma manyan matsaloli ma.

Shan ruwan da ya wuce ƙima kan haifar da matsalar ''hyponatraemia'', wadda ake samu idan gishirin da ke cikin jininmu ya yi ƙasa, da ke janyo a samu kumburi a wasu sassan jikinmu

Alomomin da ake gani idan gishiri ya yi ƙasa jikinmu sun haɗa da:

  • Tashin zuciya da amaig
  • Ciwon kai
  • ka rasa me ke damunka
  • Rashin kuzari da jin bacci da kuma jin kasala
  • Daina jin gajiya ko da ka huta da yawan jin haushi
  • Rashin ƙarfin gaɓoɓi
  • Rashin sanin halin da kake ciki

A shekarar 2018, Johanna Perry an atisaye tare da ƴarta da kuma surukinta domin shiga gasar tseen gudu ta London. Ranar ana tsananin zafi, don haka ta riƙa shan ruwa mai yawa da masu sa kai ke bai wa masu gudu.

"Abu na ƙarshe da zan iya tunawa shi ne rabin tseren," kamar yadda ta shaida wa shirin sashen abinci na BBC.

Johanna ta farka ne a asibiti sashen kula da masu buƙata ta musamman. Wani bidiyo da mijinita ya ɗauka ya nuna lokacin da take tsallaka layin ƙarshe na tsaren- wani abu da ba ta san lokacin da ya faru ba.

"Abokin zama na da wasu abokai na wurin. Sun yi ta tafa min da taya ni murna - Amma ni ban ma san me ake yi ba. Da muka koma gida ciwo ya kamani na rasa me ke min daɗi,'' in ji ta.

"Na sha ruwa mai yawan gaske, wanda kuma shi ne ya wanke duka gishiri da sauran sinadaran da jiki ke buƙata domin yin aiki.''

Abin da ya faru da Johanna ya nuna abin da zai faru idan aka bai wa jiki ruwan da ba zai iya sarrafawa ba.

Jini yana yawan zuƙe ruwan da ya shiga, ƙoda kan zuƙe ruwan da ba shi da amfani ga jiki, domin mayar da shi fitsari. A kowace sa'a guda, ƙodar ɗan'adam guda biyu kan sarrafa lita guda na ruwa ko abu mai ruwa.

Wane adadi na ruwa muke buƙata?

Domin zama cikin ƙoshin lafiya, hukumomin lafiya da dama sun bayar da shawarar shan kofi shida zuwa takwas na ruwa a kowace rana.

Hukumar lura da cin abinci da Turai ta bayar da shawarar cewa mata su riƙa shan lita biyu na ruwa a kowace rana yayin da ta buƙac maza su riƙa shan lita biyu da rabi.

Da yawa cikin abinci - musamman kayan marmari da gayayyaki da shinkafa har da nau'in gyaɗa - na ƙunshe da ruwa. Alal Misali kashi 92 cikin 100 na kankana duka ruwa ne.

To sai dai duka waɗannan shawarwari ba koyaushe ne za yi amfani ga kowa ba.

Farfesa, John Speakman na JAmi'ar Aberdeen da ke Scotland na ɗaya daga cikin tawagar da ta yi nazarin shan ruwan mutum fiye da 5,000 a ƙasashen duniya 23.

"Maza masu shekaru tsakanin 20 zuwa 60 na ɓukatar aƙalla lita 1.8 na ruwa a kowace rana, yayin da mata da ke waɗannan shekaru ke buƙatar lita 1.5 zuwa 1.6 a kowace rana. Amma idan ka kai shekara 85, lita guda ma ya ishe ka a kowace rana,'' a cewar Farfesa Speakman.

To amma adadin ruwan da kowane mutum ke buƙata ya danganta da wasu dalilai, kamar nauyin jiki da yawan aikin da mutum ke yi da shekaru da jinsi da kuma yanayin muhallin da yake rayuwa.

"Babban abin da yake tasiri kan yadda keke buƙatar ruwa shi ne abin da yake sanyaka buƙatar ruwan," in ji shi.

"I dan kana rayuwa a wani wuri mai zafi to buƙatar ruwa da jikinka zai yi ya fi na wanda ke rayuwa a wuri mai sanyi.''

Ƙishirwa wata alama ce da Allah ya halitta don bayyana buƙatar ruwan ga jiki. Launin fitsari wata ƙari alama ce da ke nuna cewa jiki na buƙatar ruwa - launin ruwan ɗorawa maras yawa a jikin fitsari alama ce da ke nuna cewa akwai wadataccen ruwa a jikinka, amma launin ruwan ɗorawa mai ƙarfi alama ce da ke nuna cewa babu ruwa a jikinka.

Haka akwai buƙatar ka riƙa shan abu mai ruwa, idan baka da lafiya kana kuma amai da gudawa.