Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waɗanne dabaru za a iya amfani da su don kare kai daga ƴan fashin daji?
- Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
- Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Matsalar rashin tsaro ta daɗe ta na addabar yankuna da dama na Najeriya, inda masu ɗauke da makamai ke kashe mutane tare da tarwatsa su daga muhallansu da kuma sace waɗanda suka faɗa hannunsu domin karɓar kuɗin fansa.
Duk da cewa hukumomi na cewa suna bakin ƙoƙarinsu, amma lamarin na ci gaba da laƙume ɗaruruwan rayuka a yankunan da ake fama da irin waɗannan tashe-tashen hankula, kamar arewa maso yamma da arewa maso gabas da kuma arewa ta tsakiyar ƙasar.
Wannan lamari shi ya kai ga har babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa ya shawaraci ƴan Najeriya da su laƙanci dabarun kare kai a matsayin mataki na ko-ta-kwana.
A wata hira da ya yi da kafar talabijin ta Chenels Janar Musa ya danganta koyon waɗannan dabaru da tamkar koyon tuƙi ko ninƙaya inda ya ce abu ne da ake buƙata a rayuwa.
Kalaman hafsan sojin Najeriyar dai sun janyo cece-ku-ce tsakanin al'ummar ƙasar inda wasu ke ganin hakan na nuna gazawa a ɓangaren gwamnati na magance matsalar rashin tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.
Me kalaman Janar Musa ke nufi?
Masana harkar tsaro irin su Dr Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Security and Consulting na ganin kalaman hafsan sojin a matsayin kira ne ga jama'a da su taka rawa wurin taimaka wa jami'an tsaro domin magance wannan matsala ta tsaro, wadda bai kamata a yi mata kallo a matsayin kira da a dauki makamai ba.
''Ya na da kyau ta wani ɓangare amma kuma muna hannunka mai sanda da kuma gargaɗin cewa haka ba ya na nufin mutane sau dauki makamai ba ne domin suna ganin shi ne hanyar kare kai, yana nufin al'umma ta san akwai hanyoyin da za ta bi domin tallafa wa jami'an tsaro a yakin da ake yi da wannan matsalar,'' in ji shi
Dr Adamu ya ƙara da cewa bai kamata jami'an tsaro su yi watsi da haƙƙin da ya rataya a wuyarsu na bayar da tsaro ba, domin tabbatar da tsaro ba haƙƙin al'umma ba ne kuma bai kamata a ɗora ma ta wannan nauyin ba.
Matakan kare kai yayin da aka kawo hari
Masana harkar tsaro kamar su Aliyu Badamasi, tsohon jami'i a rundunar sojin Najeriya sun bayar da wasu shawarwari kan matakan da za a iya ɗauka domin samun kariya a lokacin da ake fuskantar harin ƴanbindiga:
- Kada a ruɗe: Yana da muhuimmanci da a samu natsuwa a fahimci ta wane ɓangare harin ke zuwa saboda guje wa faɗawa hannun maharan a gigice.
- Kada a yi saurin ɓuya: Bayan an yi la'akari da ta inda harin ke zuwa bai kamata a yi saurin ɓuya ba saboda maharan na iya aukawa inda aka ɓuya hakan kuma na iya hana samun damar tserewa.
- Kada a yi gudu a fili: idan aka samu halin gudu a nemi abin da za a yi garkuwa a bayan shi, kamar wata katanga ko bishiya.
- A kwanta a ƙasa: Idan aka samu wurin ɓuya sai a tabbatar da cewa an kwanta a ƙasa domin kauce wa harbin bindiga.
- A yi ƙoƙarin neman taimako: Bayan an tabbatar da samun wurin ɓuya mai aminci kuma idan akwai hali sai a yi ƙokarin kiran hukuma.
Matakan kare kai na yau da kullum
Tsohon jami'in rundunar sojin Najeriya Aliyu Badamasi, ya bayar da wasu shawarwari kan yadda za a ɗauki matakan kariya yayin gudanar da al'amuran yau da kullum:
- Ankarewa a kodayaushe: Ya kamata a tabbatar da cewa ana kula da yadda al'amura ke gudana, ta hanyar kula da yanayin gari ko muhalli da kuma mutanen da ke kai-komo a cikin al'umma.
- Kula da shige da fice baƙi a al'umma: Yana da muhimmanci a tabbatar da ana kula da yadda baƙi da ke kai wa da kawowa a tsakanin al'umma domin akasari baƙi ake zargi da kitsa munanan hare-hare.
- Taimaka wa jami'an tsaro: Jami'an tsaro na buƙatar tallafi wurin tabbatar da tsaro musamman ta hanyar samun bayanan sirri da za su iya amfani da su wurin daƙile hare-hare.
Ko za a iya yin faɗa da ɗan fashi?
Duk da cewa ɗaukar makami ko kuma koyan dambe ko kokawa na iya taimakawa matuƙa wurin kare kai masana harkar tsaro kamar su Badamasi Aliyu na bayar da shawarar cewa a yi amfani da su a matsayin matakan ƙarshe bayan an yi ƙoƙarin kauce wa yin gaba-da-gaba da mahari domin a cewarsa baban burin kare kai shi ne samun tsira da rai da kuma lafiya.
Hare-haren ƴanbindiga dai sun zama tamkar ruwan dare a sassan Najeriya inda ko a baya-bayan nan wasu mahara sun kashe masu ibada aƙalla 28 a wani masallaci da ke karamar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina, a yankin arewa maso yammacin ƙasar.
Haka nan a watan da ya gabata masu garkuwa da mutane sun yi wa mutum 38 yankan rago cikin waɗanda suke garkuwa da su a jihar Zamfara mai maƙwaftaka.