Barcelona ta kammala daukar Lewandowski kan fam miliyan 42.6

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta kammala daukar dan kwallon tawagar Poland, Robert Lewandowski daga Bayern Munich kan yarjejeniyar kaka hudu kan fam miliyan 42.6.
Mai shekara 33 yana da saura kwantiragin kaka daya a Bayern Munich, sai dai a watan Mayu ya sanar cewar yana son ya koma wata kungiyar.
Tuni dan kwallon yana tare da sauran 'yan wasan Barcelona a Amurka, wadda ta shirya yin wasan sada zumunta hudu, domin tunkarar kakar da za a fara cikin watan Agusta.
Barcelona ta gindaya fam miliyan 429.9 ga duk wadda za ta dauke Lewandowski idan yarjejeniyarsa bai kare ba a Camp Nou.
Dan wasan ya koma Bayern Munich da taka leda a 2014 a lokacin da yarjejeniyarsa ta kare a Borussia Dortmund.
Ya ci kwallo 50 a wasa 46 a kakar da ta wuce, ya kuma taimakawa Bayern ta dauki Bundesliga na 10 a jere.
Lewandowski ya zura kwallo 344 a raga a wasa 374 a Bayern, shi ne na biyu a tarihin cin kwallaye a kungiyar bayan Gerd Muller.
Dan wasan ya lashe Bundesliga a dukkan kaka takwas da ya yi a kungiyar, ya kuma dauki Champions League a 2019-20.
Lewandowski shi ne na hudu da Barcelona ta dauka a bana, bayan dan kwallon Brazil, Raphinha daga Leeds United da Franck Kessie da AC Milan da Andreas Christensen daga Chelsea.
Haka kuma Bayern ta sayi dan wasan tawagar Netherlands, Matthijs de Ligh daga Juventus kan yarjejeniyar kaka biyar kan fam miliyan 65.6










