China ta harba makamai a kusa da Taiwan bayan ziyarar Nancy Pelosi

Asalin hoton, Getty Images
China ta harba makamai masu linzami da dama cikin teku da ke kusa da maƙwabciyarta Taiwan.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wata majiya daga rundunar sojan Taiwan na cewa China ta harba makamin Dongfeng, wanda rundunar sojan ƙasar ke amfani da su.
Rundunar sojan Taiwan ta ce ta ƙaddamar da shirin kare ƙasar sakamakon makaman da China ta harba, tana mai yin wadai da matakin da kira "na rashin tunani".
China ta soma atisayen soji na musamman a cikin teku kusa da Taiwan bayan ziyarar da Shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi a tsibirin.
Ms Pelosi ta bar Taiwan ɗin a ranar Laraba, bayan wata gajeruwar ziyara mai cike da taƙaddama da ta kai tsibirin, wadda China ke kallo a matsayin wani lardinta da ya ɓalla.
Domin mayar da martani, China ta sanar da gudanar da atisayen soji na tilas wanda aka soma ranar Alhamis.
Tsibirin na Taiwan ya ce jiragen yaƙin China 27 ne suka shiga ta sarararin samaniyarsa, sai dai tun a ranar Laraba ma'aikatar tsaron Taiwan ta tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro ta hanyar watsa jiragenta a sararin samaniya domin gargaɗin na China da ke mata barazana.
China dai ta ce wannan atisayen za a gudanar da shi ne a wasu daga cikin hanyoyin teku da ake samun yawan hada-hadar jiragen ruwa, kuma ta ce a yayin atisayen za a rinƙa harba makamai masu cin dogon zango.
China dai ta buƙaci jiragen ruwa da atisayen zai shafi zirga-zirgarsu da su canza hanya domin guje wa atisayen inda a halin yanzu ƙasar ke tattaunawa da Japan da Phillipines masu maƙwaftaka domin neman wasu hanyoyin da jiragen za su bi.
Shugaba Tsai lng-wen ta Taiwan ta ce ƙasarta na fusƙantar babbar barazanar soji dagangan.
A yunƙurin yayyafa wa ƙurar da aka tayar ruwa, ministocin harkokin wajen ƙasashen G-7 da suka haɗa da Canada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan da Birtaniya sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa inda suka ce yadda China ke neman zuzuta lamura zai iya jefa Yankin Asia cikin wani hali.

Asalin hoton, Getty Images











