Man City na gaban Real Madrid a zawarcin Bellingham, Liverpool za ta yi cefane

Jude Bellingham

Asalin hoton, LEE SMITH/REUTERS

Bayanan hoto, Tun a makarantar firamare Jude Bellingham ya yi fice

Manchester City na gaban Real Madrid a zawarcin Jude Bellingham na Borussia Dortmund bayan da Liverpool ta hakura da sayen matashin dan wasan na Ingila mai shekara 19. (ESPN)

Dan wasan West Ham na Ingila Declan Rice, da na Brighton mai shekara 21 dan Ecuador Moises Caicedo da na Inter Milan dan Italiya Nicolo Barella da dan Wolves na Portugal Matheus Nunes, har yanzu suna cikin jerin 'yan wasan tsakiya da Liverpool ke zawarci. (Florian Plettenberg)

Barcelona za ta kara tashi tsaye a zawarcin da take yi na Ilkay Gundogan sakamakon irin kokarin da dan wasan na tsakiya na Jamus ya yi a karawar da Manchester City ta doke Bayern Munich a gasar Zakarun Turai. (Sport)

Arsenal da Liverpool da kuma Manchester United na sa ido a kan matashin dan wasan tsakiya na Bayern Munich Ryan Gravenberch dan Netherlands (Footmercato)

Tottenham da West Ham da Crystal Palace na sha'awar daukar Arne Slot a matsayin kociya ganin yadda Bajamushen ya yi a Feyenoord. (Times)

Arsenal na son sayen dan wasan gaba na gefe na Crystal Palace da tawagar 'yan kasa da shekara 21 ta Faransa Michael Olise, wanda aka yi wa farashin sama da fam miliyan 40. (Football Transfers)

Fulham da Aston Villa da kuma Crystal Palace na sha'awar dan wasan tsakiya na Besiktas Gedson Fernandes, dan Portugal. (Calciomercato)

Liverpool ta sha tura masu sa ido domin su yi mata nazari a kan dan wasan tsakiya na Fulham Joao Palhinha a kokarin da take yi na zawarcin dan wasan na tawagar Portugal a bazara. (Football Insider)

Arsenal da Bayern Munich da Borussia Dortmund da kuma Monaco sun nuna sha'awarsu a kan dan gaban Crystal Palace da Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 30, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara. (Footmercato)

Tsohon dan bayan Ingila Chris Smalling, mai shekara 33, zai kulla sabuwar yarjejeniya ta shekara biyu da Roma a wannan makon duk da sha'awarsa da Inter Milan da Juventus da kuma wasu kungiyoyin Premier ke yi. (i Sport)

Arsenal za ta bukaci fam miliyan 35 a kan matashin dan wasanta na gaba Folarin Balogun mai shekara 21 na Ingila wanda ke zaman aro yanzu a Reims wanda kuma RB Leipzig ke so. (Florian Plettenberg).

Kungiyar Barcelona ta mata za ta gwada cinikin Ada Hegerberg ta Lyon da Norway, inda kungiyar ta Sifaniya za ta saye ta a farashin da ba a taba sayen wata 'yar wasa ba a duniya fam dubu 420 kan mai shekara 27 din. (90min)