Real Madrid na daf da fitar da Chelsea a Champions League

Karim Benzema

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid ta doke Chelsea 2-0 a wasan farko a quarter finals a Champions League a Santiago Bernabeu ranar Laraba.

Minti 21 da fara wasa Karim Benzema ya ci Chelsea - karo na 20 da ya zura kwalo a ragar kungiyar Ingila a Champions Legue.

Lionel Messi ne kan gaba a yawan cin kungiyoyin Ingila kwallaye a gasar zakarun Turai mai 27 a raga.

Tun kan hutu an buga kwallo ta nufi ragar Chelsea sau takwas, wasan da aka kai wa kungiyar Stamford hare-hare mai yawa a Champions League kenan, bayan kakar 2003-04.

Minti hudu da suka koma zagaye na biyu aka bai wa Ben Chilwell na Chelsea jan kati a karawar

Real ta kara kwallo na biyu ta hannun Marco Asensio, saura minti 16 a tashi a wasan.

'Yan wasan Real uku aka bai wa katin gargadi da suka hada da Eduardo Camavinga da Eder Militao da kuma Daniel Carvajal.

A chelsea kuwa wadanda aka bai wa kati mai ruwan dorawa sun hada da Wesley Fofana da kuma Mateo Kovacic.

Kungiyar Sifaniya ce mai rike da Champions League na bara mai 14 jimilla, ita kuwa Chelsea tana da kofin zakarun Turai biyu.

Real Madrid za ta ziyarci Cadiz ranar Asabar 15 ga watan Afirilu a wasan mako na 29 a La Liga.

Daga nan ne Chelsea za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu zangon quarter finals a Champions League ranar 18 ga watan Afirilu.

Kafin nan Chelsea wadda take ta 11 a teburin Premier League za ta kara da Brighton a Stamford Bridge ranar 15 ga watan Afirilu.

Real Madrid tana ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki 13 tsakaninta da Barcelona mai jan ragamar babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Wasa tsakanin Real Madrid da Chelsea

2022/23 Champions League

  • Real Madrid 2 - 0 Chelsea

2021/2022 Champions League

  • Real Madrid 2 - 3 Chelsea
  • Chelsea 1 - 3 Real Madrid

2020/2021 Champions League

  • Chelsea 2 - 0 Real Madrid
  • Real Madrid 1 - 1 Chelsea

1998/1999 European Super Cup

  • Chelsea 1 - 0 Real Madrid

1970/1971 Euro Cup Winners Cup

  • Chelsea 2 - 1 Real Madrid
  • Chelsea 1 - 1 Real Madrid