Toney ba zai je Arsenal ko Chelsea ba, Trippier na nan daram a Newcastle

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan gaban Brentford Ivan Toney, na Ingila wanda ake alaƙanta shi da Arsenal da Chelsea ba zai matsa kan barinsa ƙungiyar ba a watan nan na Janairu, har ma ya shirya ci gaba da zama zuwa bazara. (Mirror)
Newcastle United ba za ta sayar da ƴan wasanta biyu na Ingila ba, ɗan baya, Kieran Trippier wanda Bayern Munich ke so ko kuma ɗan gaba Callum Wilson, wanda ake cewa Atletico Madrid na naman shi, a wannan watan. (Telegraph)
Trippier da Wilson ba za su matsa lamba ba don su tafi ba, amma Bayern za ta yi ƙoƙarin jarraba sa'arta ta hanyar gabatar da tayi mai armashi fiye da na baya, bayan Newcastle ta yi watsi da tayin farko. (Guardian)
Ita dai Newcastle tana son yuro miliyan 15 a kansa daga Bayern Munich, to amma kuma ƙungiyar ta Jamus tana son ta karɓe shi a matsayin aro ne. (Sport Bild)
Zai zama dole Newcastle United ta sayar da ɗan wasanta na tsakiya ɗan Brazil Bruno Guimaraes, da kuma ɗan gabanta na Sweden Alexander Isak, domin kar ta saɓa ƙa'idar cinikayyar ’yan wasa. (Football Insider)
Idan so samu ne Jose Mourinho ya fi so ya ci gaba da zama a Italiya bayan da Roma ta kore shi kuma tuni ma yana shirin tattaunawa da shugaban Napoli Aurelio de Laurentiis don karɓar zakarun na Serie A da ke fama a gasar a bana. (Times )
Crystal Palace ta fara duba sunayen wadanda za ta zaɓa domin maye gurbin kocinta Roy Hodgson, inda ta fara nazarin tsohon kocin Nottingham Forest Steve Cooper, da tsohon kocin Wolves Julen Lopetegui, da kocin Ipswich Kieran McKenna da tsohon kocin Mainz Bo Svensson da sauransu. (Mail)
Tottenham ta yi watsi da tayin fam miliyan 20 daga Al-Nassr a kan ɗan bayanta na Brazil Emerson Royal, kuma ƙungiyar ta Saudiyya na duba yuwuwar ƙara farashin. (Talksport)
Har yanzu Juventus na son ɗan wasan tsakiya na Tottenham Pierre-Emile Hojbjerg, amma kuma ita Spurs tana son sayar da shi ne gaba ɗaya ko kuma ta bayar da aronsa da sharaɗin sayen ɗan wasan na tawagar Denmark. (Sky Sports)
Wataƙila ɗan bayan Everton Ben Godfrey ya za zama zaɓin AC Milan, kuma da alama Sheffield United da Leeds United na sha'awar ɗan wasan ɗan Ingila.(Calciomercato)
Aston Villa ta yi watsi da tayin West Ham na aron matashin ɗan gabanta na Colombia Jhon Duran tare da yuwuwar sayensa a gaba. (Guardian)
Liverpool na son fam miliyan 20 a kan golanta ɗan Jamhuriyar Ireland Caoimhin Kelleher, wanda aka ce Celtic na so. (Football Insider)
Eintracht Frankfurt ta Jamus ta cimma yarjejeniyar baka da matashin ɗan gaban PSG Hugo Ekitike, na Faransa a kan sayensa. (Sky Sports)
Ƙungiyoyin La Liga Cadiz da Getafe sun gabatar da tayin sayen ɗan wasan tsakiya na Sporting Gijon Jonathan Varane, wato kanin Raphael Varane na Manchester United. Haka su ma ƙungiyoyin gasar ƙasa da Premier ta Championship Norwich da QPR sun gabatar da tayi a kan ɗan Faransar mai shekara 22.. (L'Equipe )










