'Ya kamata a ɗauki mataki mai tsauri kan masu cin zarafin ƴan wasa'

Mike Maignan

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban hukumar Fifa, Gianni Infantino ya yi kira da a dauki hukunci mai tsauri ga kungiyar da magoya bayanta suka yi kalaman wariya lokacin wasan tamaula.

An dakatar da wasan da AC Milan ta yi nasara a gidan Udinese na ɗan wani lokaci, bayan da ƴan kallo daga masu masaukin baki suka yi wa golan Milan, Mike Maignan kalaman wariya.

Infantino ya sanar a shafinsa na sada zumunta wato X cewar ya kamata a dauki hukuncin mai tsauri ga waɗanda ke kalaman wariya ga ƴan wasa.

Ƴan wasan AC Milan sun fice daga fili, lokacin da Maignan ya yi korafin ya ji kalaman wariya daga wani sashen ƴan kallo a filin Stadio Friuli.

''Bai kamata ake yi wa ƴan wasa kalaman wariya ba lokacin taka leda, amma abin takaici da hakan ke faruwa a shekaru da yawa'', inda golan mai shekara 28.

''Duk da cewar akwai kamara da yawa a filaye da hukuncin da ake dauka ya kamata a dauki matakin da zai kawo karshen wannan dabi'ar.

Milan da Inter suna goyon bayan Maignan, Serie A ta sanar cewar ta yi alla- wadai da kalaman wariya lokacin wasa, shi kuwa Kylian Mbappe ya buƙaci a kawo ƙarshen lamarin.