Real Madrid ta ci Almeria da gumin goshi a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta yi nasara a kan Almeria a wasan mako na 21 a gasar La Liga da suka kara a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.
Minti ɗaya da take leda Almeri ta ci ƙwallo ta hannun Largie Ramazani, sannan Edgar Gonzalez Estrada ya ƙara na biyu daf da za su je hutu.
Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Real ta zare ɗaya ta hannun Jude Bellingham a bugun fenarity, sannan Vinicius Junior ya farke na biyu.
An ci karo da takaddama, bayan da alkalin wasa ya soke kwallon da Almeria ta ci na uku da cewar an yi wa Bellingham ƙeta, bayan da ya je ya kalli abin da ya faru a VAR.
Haka kwallon da Vinicius ya farke sai da alkalin wasa ya je na'urar da take taimaka wa alkalin wasa yanke hukunci, bayan da aka yi zargi ya ci kwallo da hannu.
Daf da za a tashi wasan ne Real Madrid ta ƙara na uku ta hannun Daniel Carvajal, hakan ya sa ta haɗa maki ukun da take buƙata.
Real Madrid ta buga wasanta, daga baya kuma za a fafata tsakanijn Real Betis da Barcelona da na Girona da Sevilla.






