'Za mu ɗauki matakin shari'a kan ƴan siyasa da suka tayar da tarzoma'

Asalin hoton, Comrade Aminu Abdulsalam/Facebook
Gwamnatin jihar Kano ta ce tana zargin wasu ‘yan siyasa da hannu da tarzomar da ta ɓarke yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar.
Hukumomin sun ce za su yi duk mai yiwuwa a karkashin damar da doka ta basu don tabbatar da cewa waɗanda suke da hannu wajen kunna wutar rikici a lokacin zanga-zangar sun fuskanci shari’a.
Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo shi ne mataimakin gwamnan Kano kuma ya shaida wa BBC cewa tuni suka tattara bayanai akan wadanda suke zargi kuma za su ɗauki mataki na gaba.
"Ba zargi muke ba muna da takamaiman shaida da hujja na ƴan siyasa da suka shiga suka kawo ƴan iska suka kawo ƴan ta'adda, suka biya su kuɗi suka zo suka yi wannan ta'annati, muna kuma tattara bayanai."
Gwamnatin jihar Kanon ta ce ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen ɗaukar matakin da ya dace," Za mu tabbata duk wanda ke da hannu wajen sabbabawa mutane baƙin ciki da ta'adi da aka yi a jihar Kano, babu shakka sai mun gabatar da shi gaban sharia."
Mataimakin gwamnan jihar Kanon ya ce gwamnati ta fara ɗaukar dukkan matakan da suka kamata domin ganin dukkan wanda ke da hannu cikin tayar da tarzomar bai sha ba.
Gwamnatin Kanon ta kuma ce dokar taƙaita zirga-zairga za ta ci gaba da kasancewa a jihar har sai lokacin da jami'an tsaro suka bayar da rahoton cewa gari da ƴan ta'addan sun haƙura ko kuma an kama su.
Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi kira ga iyaye da su kula da ƴaƴansu, su kuma riƙa gaya masu abin da ya kamata su sani na kishin ƙasa, "Kar kuma wani yaro ya ɗauko ko hula ce ya shigo da ita gidanka da sunan sun je an yi tarzoma sun samo wani abu, wannan yana da haɗari sosai wajen al'umma da iyaye da yaran."
Gwamnatin Kano dai ta yi zargin cewa an shiga da ƴan daba cikin garin domin tayar da tarzoma a lokacin zanga-zangar matsin rayuwa da aka fara a ranar Alhamis.











