Aikin daidaita halittun gado da zai iya warkar da masu sikila ya fi ƙarfin masu cutar

    • Marubuci, Makuochi Okafor
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Lagos

"Matsanancin ciwo mai cin jiki," shi ne yadda Maureen Nwachi, matashiya 'yar shekara 39 daga Lagos a Najeriya, ta bayyana halin rashin lafiyarta ta sikila.

Ta kwatanta tsananin ciwon da irin “yanayin da ƙofar mota ta datse maka ɗan yatsa. Ko kuma a yi ta kwankwatsa wa mutum guduma a tsakanin gaɓoɓinsa.”

Maureen tana rayuwa ne da cutar sikila wadda larura ce ta rashin daidaitaccen jini da ta yi gado. Wannan da wata cutar jini da ita ma ake gado mai suna, beta-thalassemia, na shafar miliyoyin mutane a faɗin duniya, inda mafi yawan masu fama da cutukan ke zaune a Afirka da Indiya.

Duka cutukan na shafar wani sinadari da ke kai iska cikin tsokar jiki. Kwayoyin cutar sikila na sauya yanayin kwayoyin jan jini ya yi kauri ya kuma yi zafi. Hakan na shafar lafiya da tsayin rayuwar kwayoyin jinin ta yadda ba sa dadewa yadda ya kamata, sannan kuma suna toshe jijiyoyin da jini ke bi, wanda kuma yakan haifar da raɗaɗi da barazana ga rayuwa.

Cutar jini ta Beta-thalassemia tana hana jiki samar da wadataccen sinadarin da ke samar da iska ga jan jini. Idan kuma babu isassehn wannan sinadari (Haemoglobin) a cikin kwayoyin halitta na jan jini, iskar oxygen ba za ta iya kai wa ga kowanne sashe na jiki ba.

Sai a yanzu ne aka samu wasu magunguna biyu - sauya jinin jiki da kuma kwayoyin maganin Hydroxyurea - da su ake amfani wajen shawo kan wannan cutar.

Amma maganin da ake yi na dindindin shi ne sauya ɓargon jiki wanda ya yi kusa da na wanda zai taimaka da shi, wanda kuma ake fuskantar turjiya daga jiki sau da dama ya ƙi karba.

Na'urar 'genetic scissors'

A ƙarshen 2023, Birtaniya ta zama ƙasa ta farko a duniya da ta samu lasisin amfani da kayan aikin sauya kwayoyin halitta, wanda ake kira da Crispr domin maganin duka cutukan biyu. A watan Disambar shekarar, ita ma Amurka ta samu irin lasisin guda biyu.

Na'urar wadda aka fi sani da 'genetic scissors' tana aikin daidaita kwayoyin halittar dan'adam, wanda ake kwashe kwayoyin halittar mutum. Kuma waɗannan kwayoyi da aka kwashe su ake mayarwa sai su ci gaba da aiki a jiki a matsayin lafiyayyun kwayoyin halittar.

Har yanzu likitocin ba su san tsawon wane lokaci wannan sabuwar hanyar za ta iya ci gaba da aiki ba a jikin majinyaci, sai dai har yanzu ana tattara bayanan farko kan gwajin da ake yi.

Cikin mutanen da aka yi gwajin a kansu akwai marasa lafiya 28 cikin 29 da yanzu suka daina jin wannan raɗaɗi na tsawon shekara tun bayan yi musu magani. Yayin da 39 cikin 42 na masu fama da Beta-thalassemia na buƙatar a ci gaba da sauya musu jini na tsawon shekara bayan aikin.

Amma zuwa yanzu wannan ci gaba ya yi tsada kuma yana da wuya ga majinyata. Lasisin da aka bai wa Amurka na aikin, kowanne aiki zai iya laƙume dala miliyan biyu zuwa uku ga kowanne majinyaci. Aiki ne mai sarƙaƙiya da ke ɗaukar awanni masu yawa a asibiti irin wanda ke da kayan aikin na zamani.

Kashi 80 cikin 100 na masu sikila a Kudu da Hamadar Sahara suke

Sama da mutum miliyan biyu da ke fama da sikila na rayuwa ne a ƙasashen Kudu da Hamadar Sahara kamar yadda alƙaluman Global Burden of Disease na 2021 suka bayyana.

An yi hasashen cewa ana haifar yara 1,000 a yankin Afrika da cutar sikila a kullum, hakan ya sa cutar ta zama ruwan dare a nahiyar. Najeriya ce ƙasar da ta fi fama da masu wannan cuta a duniya sai dai yanzu haka an fi samun ƙaruwarta a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

Hakan ya sanya wuraren ibada da ake aure kamar su coci da masallatai a Najeriya neman shaidar gwajin rashin kamuwa da cutar kafin aure. Wasu ma ba sa ɗaura auren sai sun tabbatar da duka masu shirin auren sun kubuta daga hatsarin haifar mai ɗauke da cutar, wanda hakan zai kare yara daga hatsarin a haifesu dauke da sikila.

Duk da cewa a Najeriya ana yin sauyin jini da kuma samun kwayoyin cutar, da yawa ba sa iya biyan kuɗin da za a yi. Wanda hakan yake sanya su ci gaba da rayuwa cikin raɗaɗi, wasu har su hakura da neman 'ya'ya.

Wannan matsalace da ta zama ruwan dare a nahiyar wadda take fama da matsaloli irinsu HIV/AIDS, gudawa, maleriya da tarin fika.

Dr Stella Rwezaula, ta sashen Haematology a Asibitin Muhimbili da ke Dar -er - Salaam a Tanzaniya, ta ce yanzu ba a samun aiki ko maganin sikila a asibitin nasu, saboda ya yi wa masu fama da rashin lafiyar tsada.

"Mun san cewa mutanenmu ba su da inshorar lafiya," in ji ta.

"Kamata ya yi gwamnatoci su sanya jari su taimaka wa mutane domin samun wannan magani."

Dr Faramola Ogunkoya wata mai bincike ce kan sikila a jihar Legas a Najeriya, ta amince da hakan ita ma. Tana fatan ganin an sanya wannan cuta cikin tsarin inshorar lafiya, a sake fadada samar da kwayoyin cutar yadda za su yi sauki a kasuwa a kuma ci gaba da bincike na cikin gida a jami'o'in Afirka da sauran cibiyoyi.

"Mafi yawan ƙasashen Kudu da Hamadar Sahara har yanzu da maganin hydroxyurea suke amfani wanda yake bai wa masu jinya sauki na wani lokaci," in ji ta tana mai cewa wasu wuraren sayar da magani kalilan ne a Najeriya suke samar da shi.

Dr Ogunkoya na son a riƙa gwada duka jariran da aka haifa ko da yaushe, "cikin watanni ukun farko na haihuwa, dan a sani a fara yi musu magani tun da wuri".

Dr Akshat Jain ya ce zai iya ɗaukar gwamman shekaru kafin a samu ci gaba na'urar da za a riƙa sauya ɓargo da ita a Afrika.

'Tamkar mafarki ne a wajen mai fama da sikila a Indiya'

Yayin da sikila ta fi yawa a Najeriya, cutar jini ta beta-thalassaemia ta fi kankama a Indiya.

Kamar a Afrika, mafi yawan mutane na fama a can wajen samun maganin. Mafi yawan mutanen India rabin kuɗin asibitinsu suke biya - musamman kan magani.

Anubha Taneja na daga cikin wata kungiya a Delhi da ke wayar da kai da kuma neman a sake taimaka wa masu fama da beta-thalassaemia.

Ta ce yayin da suka ji labarin samar da wannan na'ura cikin farin ciki, su a India maganar sauyin jini yanzu aka sa a gaba.

"Muna son gwamnati ta ƙara mayar da hankali kan yadda za a samar da fasahar da mutane za su zuba mata jari domin gudanar da aiki ga masu fama da sikila," in ji ta.

"A wajen masara lafiyar inda akan ba komai ba ne face burin da ake son ya cika a nan gaba".

Allura guda?

Ko a Amurka kasa da cibiyoyi 12 aka bai wa damar amfani da na'urar sauya ɓargo saboda sarƙaƙiyar da yake da shi, da kuma yadda ake buƙatar a sanya idanu kan marasa lafiya.

Amma Gidauniyar Bill da Melinda na cikin waɗanda ke aiki domin sauƙaƙa hakan.

Likitan Gidauniyar Dr Mike McCune ya shaida wa BBC cewa tawagarsu na neman wata hanya da za ta fi wadda ake da ita a yanzu sauki, wata hanyar magance matsalar wadda za ta fi sauki nan da shekara biyar.

"Fatanmu samar da wani ci gaba da zai mayar da wannan ko wa zai iya biya, ya samat da allura guda da za a yi a kafaɗa amma za ta magance matsakar sikila da HIV - ta kuma taimakawa kwayoyin halitta," in ji shi.

Gidauniya Gate na aiki tare da kamfanoni irinsu Novartis wanda tuni suka sa ɗanba kan maganin sikila yanzu haka suna Najeriya da fatan yadda za a sa maganin ya yi araha mutane na ƙasa su iya saya.

Ga mutane irin su Maureen Nwachi da ke Najeriya, samun taimako kan matsalar jini ba abu ba ne da za a shawo kansa a kusa.