New Zealand ta ƙaddamar da gagarumin yaƙi kan ɓeraye

..

Asalin hoton, Getty Images

Ranar wata Lahadi da hantsi masu ƙaunar namun daji suka yi cincirindo a Miramir, waje mai kama da tsibiri.

Sun taru ne a manufarsu ta kawar da batun hallaka dabbobi.

Raba Miramir da masu cin naman dabbobi na da manufar kare tsuntsaye da suke wannan yanki na Wellington, babban birnin New Zealand, ta hanyar raba birnin da beraye – ya kasance ba ko daya da ya rage.

Bayan sun sanya rigunan kariya, an mika wa ‘yan sa-kan tunkuza - wadda za a yi amfani da ita wajen jan hankalin beraye – da kuma guba.

Kowanne aka nuna masa inda zai binciki tarko da akwatunan kama bera don kashe su. “Abokan aiki Allah Ya ba da sa’a,” in ji Dan Coup, wanda ya jagoranci mutanen.

..

Wata manhaja ta GPS ce take yi wa Coup jagora bin hanya, domin kutsawa cikin dajin. A kowanne shi yake canza masa da wani kayan aikin da kuma sabunta bayanan da suke cikin manhajar. Babu wanda ya nuna wata alama ta bera ya zo buruntu wajen.

Amma da ya ci gaba da lalube da neman dukkan wata shaida ko alama, sai ga wayarsa ta girgiza. Wani a cikinsu ya tura hoto dandalinsu na whatsapp: ga wani mataccen nera a cikin tarko.

Wannan ba labari ba ne mai dadin ji. “Dave zai ji dadi ya kama, sai dai muna bakin cikin cewa har yanzun da sauran bera, in ji Coup.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kawar da beraye da sauran dabbobi da suke kashe dabbobi suna cin namansu shi ne burin, ba a Miramar kawai ba, har ma da dukkan ilahirin New Zealand.

Gwamnati tana sa ran kammala wannan aiki nan da shekara ta 2050.

Aiki ne ja. A ce tsibiri mafi girma da ya kawar da duka beraye shi ne South Georgia/Ku]ancin Jojiya, kasa mai nisan kilomita 170 (Mil-105) da ke Kudancin Tekun Atalanta.

Masu rajin kare muhalli na New Zealand sun yi imanin nasarar da za a samu tana iya zarce girman Birtaniya.

Wasu kuma suke nuni da matsaloli na gudanarwa a aikace da kuma batu na ka’ida.

Abin da ya mamaye zuciyar wannan aiki shi ne alkinta muhalli.

New Zealand ta balle daga tsohuwar babbar nahiya tun shekaru miliyan 85 da suka gabata, da dadewa kafin karuwar dabbobi masu shayar da jariransu nono. Bacin dabbobi da suke kasa da suke kashe wasu dabbobin ba, da tsuntsaye za su iya yin sheka a kasa ko tafiyar da rayuwarsu ba tare da sai sun tashi sama ba.

..

Bugu da kari, New Zealand ce kasa mai fadi ta karshe da ‘yan Adam suka zauna a cikinta. A karni na 13 mutanen wuraren tsibirin Polynesia suka kawo kananan beraye. Bayan karni shida, Turawa suka kawo manya-manyan dabbobi da suke cinye tsuntsaye marasa karfin kare kan su. Daga zaman dan Adam za a iya cewa an gama da kusan kashi uku na nau’in tsuntsayen kasar.

Kokarin da ake ta fafutukar yi na ceto sauran ba sabon abu ba ne. A shekarun 1960, masu rajin kare muhalli sun kawar da duk wani bera da ke kananan tsibiran teku. Sai dai magance matsalar dabbobi da suke kashe wasu dabbobin ba ta zama ruwan dare game duniya ba, har sai a wajen shekara ta 2010.

“Ta yunkura, ta zama wani babban lamari na kasa.” In ji James Russell, wani masanin halittu a Jami’ar Aukland kuma wanda yake kan gaba, a burin na 2050.

..

Asalin hoton, Getty Images

Wani muhimmin abu kamar yadda Russell ya yi bayani, shi ne kirkiro da kyamarorin daukar hoto masu iya auna yanayin abu. A karni na 20 kwarin da aka fi gani, da kuma abubuwan da aka fi mayar da hankali don rage su, su ne manyan dabbobi masu cin shuke-shuke kamar su namun daji dangin su barewa da su bunsuru da akuya.

Sai dai daga shekarun 2000, masu sha’awar namun daji sun samu nasarar nuna abubuwan da kananan dabbobi ke yi da daddare.

An ta nunawa tare da tura hotunan yadda beraye ke auka wa kwayaye da kaji. “Wannan hoto tamkar wani kaimi ne,” In ji Russell. A wannan lokaci wani masani bangaren alkinta muhalli ya yi bayanin cewa New Zealand tana asarar tsuntsaye guda miliyan 26 a duk shekara sanadiyyar hallaka su da wasu dabbobin suke yi ta hanyar kashe su da cinye su. Ko cinye su da ran su.

A shekarar 2011 wani fitaccen masani a bangaren kimiyyar abubuwa na makamashi da dangoginsa, Sir Paul Callaghan, ya yada tare da daukaka burin raba kasar da dabbobin da suke cinye ‘yan uwansu dabbobi. Russell da sauran matasa ‘yan rajin kare muhalli suka ce abu ne mai yiwuwa idan aka yi wadataccen zuba jari da kuma wayar da kai da janyo jama’a.

Daga nan ‘yan siyasa suka bi sahu. A shekarar 2016 wata doka ta bayyana dabbobin da suka fi kashe ‘yan uwansu dabbobi suna cinye su, da za a mike tsaye domin kawar da su (Beran Pacific, da beran jirgin ruwa da beran Norway), da sauran nau’o’i na beraye da suke yi wa sauran dabbobi lahani. Aka kuma sa wa’adin tsakiyar karni.

..

Aka kafa wata kungiya ta bainar jama’a mai suna Predator Free 2050 Ltd domin tura kudaden gwamnati da na bangaren da ke zaman kansa, zuwa kananan ayyuka domin gwajin dabarun kawar da wadannan mugayen dabbobi.

Wanda ya fi fice a cikinsu shi ne Predator Free Wellington, wato raba Wellington da wadannan mugayen dabbobi. A birni mai mutum 200,000, manufarsa ita ce kashe nau’o’i daban-daban na kwari, musamman beraye da suka yi ka-ka-gida a birane

Aikin wanda yake da ayari mai karfi na mutum 36 ya mayar da kananan masu farautar bera sun zama ainihin masu hallaka beraye,

{ungiyar ta samar musu da guba wacce ta fi tarko aiki, da manhajar GPS da take adana bayanai daga kowacce na’ura a lokacin da ya kamata.

Aka girke kyamarori a muhimman wurare. “Duk beran da ya zo” in ji Daraktan Predator Free Wellington James Wilcox, “mutanena masu tsare-tsare sun san inda suke so su mayar da hankali da kayan aiki.”

Duk beran da aka samu a mace, sai a aike da shi dakin gwaje-gwaje da bincike domin fede shi don gano mene ne ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Wannan yana da muhimmanci domin irin gubar da suke amfani da ita, ita kashe bera take yi sannu a hankali ba kisa ta farat-daya ba. Beraye nau’in dabbobi ne da suke da wayon tsiya, da suke da dabarar kauce wa abubuwan da ko shakka babu suna musu lahani.

A lokacin da beran ke mutuwa a tarkon, kungiyar Predator Free Wellington tana bukatar ta duba cikin jikin beran domin tantance ingancin wannan hanya ta tarko.

“Muna fede su domin gani ko gubar ce ta kashe su,” kamar yadda Willcox ya yi bayani. “Har ila yau muna bukatar mu fahimci beran mace ce ko namiji, kuma ko ya hayayyafa a ‘yan kwanakin nan? Muna bin bera ne guda daya ko gungu na beraye?”

..

Asalin hoton, Getty Images

Miramir ta kasance ita ce kan gaba a yaki gadan-gadan da birnin yake yi da dabbobi masu kashe sauran dabbobi su lakume su. A yanzun berayen sun kaura da wuya ake ganinsu a yankin, sannan tsuntsayen na gida da dama suna ta dawowa. Tsuntsun da ake kira tui da yawansa ya ci gaba da raguwa a Wellington a 1990, sai ga shi yana ta yawaita a ko’ina.

“A lambunmu da yake baya, a yanzun muna da tui yana ta shawagi a kowanne lokaci,” in ji dadadden mazaunin Miramir Paul Hay. “Rayuwar tsuntsun ta kankama, musamman a shekaru biyar da suka gabata,”

Kokarin da aka yi a fadin birnin ya amfana ne daga kokarin da masu rajin alkinta muhalli na farko suka yi, wadanda su ne suka soma wannan yunkuri a Wellington: da ake kira da predator-proof fencing da ke nufin katange kai daga mugayen dabbobi da suke hallaka sauran dabbobi suna cinye su.

A shekarar 1999 aka bude gari na farko a duniya mil guda daga tsakiyar birnin saboda yadda tui ke ta shawagi.

A yanzun ana kiransa da Zealandia, an kare shi da wata katanga mai nisan kilomita 8. Ana bincikar jakunkunan maziyarta kuma dole su bi ta wani shinge mai kofa biyu.

..

A wannan waje da aka sa matakan tsaro masu tsauri, tsuntsayen da aka taba nema aka rasa, ba tsira kawai suka yi ba, suna ma ci gaba da yaduwa zuwa inda ake makwabtaka da su.

A yanzun akwai gomman irin wadannan wurare da aka katange a sassan New Zealand. Daya daga cikin wadanda suka fi girma shi ne wanda yake da kusan kadada 700, ya ninka na Zealandia har sau uku a girma, da ke Nelson a Sauth Island.

Shekara guda da yin wata katangar ware mugayen dabbobi a 2016, aka raba yankin da kwari.

Kalubalen da ke nan a yanzun shi ne tabbatar da babu wanda ya shiga ciki. Tsautsayi yana iya sa wani tsuntsu mai cin bera, ya jefa bera a ciki; ko bishiya tana iya faduwa kan katangar, wasu mugayen dabbobin su samu damar rarrafawa ciki.

Ana yi wa katangar barna za a ji gargadi yana tashi. “Da an ji kararrawar ankararwa da talatainin dare, wani cikinmu zai mike a can domin dubawa,” in ji Nick Robson, manajan aikace-aikace na wajen.

Kyamarori da sauran abubuwa da aka tanadar na tsaro za su ankarar da ma’aikata cewa ga fa kutse an yi. Sai dai kayayyakin gano ko an yi kutsen, kuma manyan abokan gabar mugayen dabbobin, su ne kuma manyan abokan mutum. “An horar da wasu karnuka domin gano wasu nau’in kwari, da yin watsi da wadanda ba ruwan su, da su,” in ji Robson.

“Kare zai iya gano cewa akwai fa wani bera, da na’urarmu ba ta gano shi ba.”