Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda matasan Tunisiya suka sa min wuƙa a maƙogoro'
Tana tsaye a kan titi babu wajen zama tare da jaririnta dan shekara ɗaya da ta goya a bayanta, Louise Fallone, ta bayyana yadda wasu mahara rufe da fuska suka shiga gidanta tare da fito da ita waje kan titi.
Ta ce, "Da misalin ƙarfe biyu na dare ne wasu matasa suka kai hari gidanmu. Sun rinƙa jifar mu da dutse sannan suna ɗauke da wuƙa a hannunsu suka kuma sanya mini ita a maƙogorona."
"Sai na ɗauki ɗana na tsere ba tare da na ɗauki komai ba. Wata maƙociyata ce ma ta jefo mini bargo a lokacin da ta ga ina gudu. Sun ɗauke mini kuɗina da kuma kwashe duk abin da na mallaka mai muhimmanci."
Louise na zaune a birnin Sfax tsawon shekara guda bayan da ta isa birnin daga Ivory Coast. An kai mata hari a wani rikici da ake yi kan nuna kin amincewa da baki 'yan ci-rani a birnin na Tunisiya, rikicin kuma ya samo asali ne bayan da aka caka wa wani mutum mai shekara 41 wuka a yayin wata taƙaddama da aka yi da 'yan ci-rani.
Da muke shiga cikin birnin, abin da muka fara cin karo da shi shi ne daruruwan 'yan ci-rani tsaye a gefen titi mai ƙura suna riƙe da kwalaye da aka rubuta alamun neman zaman lafiya.
Yanayin zafi a birnin a lokacin da muka je ya kai digiri 40 a ma'aunin salshiyas.
Mun ga yadda mutane ke taimaka wa 'yan ci-ranin suna ba su ruwa da burodi, abin da ya nuna cewa har yanzu akwai karramawa tsakanin ƴan gari da kuma baƙi ƴan ci-rani ke nan.
Hotunan bidiyon harin ya kare da wurare. Daya daga cikin bidiyon ya nuna wani mutum rufe da fuska na ihu, yana cewa "Baƙaƙen fata ƴan Afirka na barazana gare mu da matanmu. Dole mu far musu, mu hada kai don yakarsu."
A daya bidiyon kuwa, wani mutum ne ke ihu yana cewa "Dole mu fatattaki wadannan bakaken fata. Ba ma bukatar zamansu a nan."
Domin mu fahimci abin da ya janyo tarzoma a birnin, muka yanke shawarar shafe dare guda tare da daruruwan 'yan ci-rani da suke kwanciya dandanyar kasa.
Yawancinsu sun ji raunin da za a iya gani sun kuma shaida mana yadda harin ya faro a ranar 4 ga watan Yuli.Akwai wata a gefe da ta ji raunin sosai har ma bata cikin hayyacinta.
An kwantar da mutane 25 a asibiti a daren da aka kai harin, ciki har da yara.
Wani dan ci-rani ya ce har da dan uwansa dan shekara bakwai a cikin waɗanda aka kwantar a asibiti saboda karya masa kafa da aka yi.
Hotunan da muka gani na harin ya nuna rashin kai dauki daga 'yan sanda duk da bukatar hakan da aka rinka nema a lokacin.
Washegari ne mahukunta suka mayar da martani ta hanyar cire 'yan ci-rani fiye da 100 daga birnin da karfin tsiya tare da kai su iyakar kasar da Libya.
A cewar jami'an kasar ta Tunisiya, kawo yanzu an kai 'yan ci-rani dubu guda iyakar kasar da Libya da kuma Algeria.
Hotunan bidiyon da muka gani na halin da 'yan ci-ranin da ke kan iyakar da kuma aika wa kungiyar kare hakkin dan'adam ta Human Rights Watch, sun nuna su a cikin hali marar dadi domin wasunsu sun ji rauni, har ma suna iƙirarin cewa mahukuntan Tunisiyan sun dake su.
Masu tsaron iyakar dai sun musanta zargin cewa an ci zarafin 'yan ci-ranin.
Kazalika shugaban ƙasar ta Tunisiya, Kais Saied, ma ya yi watsi da batun an wulakanta 'yan ci-ranin inda ya ce ana kulawa da su.
A yanzu an ɗan samu zaman lafiya a kan titunan birnin, to amma har yanzu ana kai hari nan da can a wuraren shan gahawa.
Wata mata mai shago kuma mai fafutuka, Miriam Bribri, ta ce ranta ya baci sosai sannan ta fusata, to amma ba ta yi mamakin rikicin da ya barke ba.
Ta ce "Akwai bidiyon wariyar launin fata da aka rinka yadawa a kafafen sada zumunta. Da nake kallon bidiyon marar dadi, sai na damu saboda na san cewa irin wannan bidiyon babu abin da yake haifarwa sai fitina."
Ta dora alhakin hakan a kan shugaban kasar. Saboda a farkon shekarar nan ya amince da irin wadannan al'amura a kasar.
Akwai wani shafi a shafin sada zumunta na facebook da ke sukar yadda ake yada rikicin Sfax, in ji Sayeb-Etrottoir.
Kwanaki kafin a fara rikicin, an wallafa wasu hotuna da bidiyon da ke nuna cewa ya kamata a ceto birnin Sfax daga 'yan ci-rani.
Mai kula da shafin Zied Mallouli, ya yi watsi da irin wadannan zarge zarge.
A cikin wata hira da ya yi da BBC, ya ce yana yada dalilin da ya sa mutane suke bin tituna cikin dare.
Su a wajensu suna kai hari ne saboda suna ganin kamar 'yan ci-rani sun kwace musu gidaje, ma'ana sun samu wurin zama.
Ya ce, " Mafita a kan wannan matsala ita ce mahukunta su tara dukkan mazauna birnin na Sfax su samar musu wajen zama a inda ya dace."
A cikin tsakiyar birnin, kusa da wani waje da ake zubar da shara, akwai 'yan ci-rani 300 da suka yi sansaninsu a wajen tun bayan da aka kore su daga gidajen da suke ciki.
Ta ce, "Na shafe kwana hudu a nan tare da iyalina saboda ba mu da wajen da za mu zauna."
Mariam, tana da yara biyu kuma ta zo ne daga Saliyo.
Ta ce ta gaji da halin da suke ciki. Ta ce tana ji kamar ta ranto kudi ta koma gida.
"Na ga wadannan mutanen suna jin yunwa da kuma kwana a budadden waje", in ji wani mutum da ke zaune a wajen.
Ya ce, " Saboda haka ne ni da abokaina muka yanke shawarar kawo musu gasasshen burodi."
Ya ce a jiya sun kai musu nono da ruwa duk kyauta, saboda Allah.
Shi kuwa wani direban tasi ya ce shi da matarsa sun fara saukar bakin hauren inda suka sauki wata mata da 'yarta bayan an kai musu hari sun gudu.
Bayan ganin irin abubuwan tashin hankalin da suka faru a makon da ya wuce, mazauna birnin Sfax na ganin cewa da wuya birnin ya dawo yadda yake a baya.
Gwamnatin Tunisiya yanzu ta yanke shawarar abin da take ganin ya dace ta yi.