Ko tsallake yin karin kumallo na da haɗari ga lafiya?

Asalin hoton, Getty Images
Dukkan mu mun taɓa jin shawarar da ake bayarwa game da yin karin kumallo mai kyau wanda zai iya tabbatar da cewa ranar za mu kasance cikin walwala. Amma ko wannan na nufin cewa cin wannan abincin zai iya ƙara mana ƙoshin lafiya, ya kuma taimaka mana rage ƙiba - ko dai wannan wani abu ne na daban?
Kamar yadda ake amfani da kalamai irin su "karas na gyara gani da daddare" da "Santa ba ya kawo wa yara marasa jin magana kayan wasa", haka iyaye da dama ke amfani da kalaman da ke nuni da cewa, karin kumallo ne abincin da ya fi kowanne muhimmanci.
Da yawa daga cikinmu mun taso da yardar cewa rashin yin karin kumallo keta dokokin cin abinci ne, amma adadin da ke cikinmu da ke ɗaukar lokaci mu ci abincin na iya bambanta.
Kusan kashi uku cikin huɗu na Amurkawa suna yin karin kumallo akai-akai, yayin da a Birtaniya, kusan kashi 94% na manya da kashi 77% na samari na yin karin kumallo akai-akai. Wani bincike da aka yi a Switzerland ya nuna kashi biyu bisa uku na manya a can suna cin abincin safe akai-akai.
A lokacin da ake fama da ƙarancin lokaci, karin kumallo na safe sau da yawa shi ne abu na farko da ake fara haƙura da shi. Sau nawa ne za ka ga muna cin abinci yayin da mu ke kan hanya, ko kuma mu ke haƙura da abincin da za mu ci da safe domin mu samu ƙarin mintuna muna barci?
Duk da haka, alamar dalilin da ta sa ya kamata karin kumallo ya zama ya na da mahimmanci a cikin sunansa a turance: Muna ci ne don mu karya azumin da muka yi a lokacin da muke barci da daddare.
Idan ba karin kumallo kaɗai ba ne ke tabbatar da rage nauyi, me ya sa ake alaƙanta ƙiba da rashin yin karin kumallo?
Ko rashin yin karin kumallo na iya haifar da ƙiba?
Akasarin binciken da ake yi kan karin kumallo (da kuma rashin yin sa) shi ne alaƙar da ke tsakaninsa da ƙiba. Masana kimiyya suna da ra'ayoyi daban-daban game da dalilin da ya sa akwai dangantaka tsakanin waɗannan abubuwan biyu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wani bincike da aka yi a Amurka wanda ya yi nazari kan bayanan lafiyar mutane 50,000 cikin shekaru bakwai, masu bincike sun gano cewa waɗanda suka yi karin kumallo mai nauyi a rana sun fi samun ƙarancin ma'aunin jiki (BMI) fiye da waɗanda suka ci abincin rana ko abincin dare mai yawa. Masu binciken sun yi iƙirarin cewa karin kumallo yana taimakawa wajen tabbatar da ƙoshi da kuma inganta yanayin abincinmu.
Amma wani bincike da aka yi kan wasu mata masu ƙiba guda 52 ya gano cewa ba karin kumallo ba ne da kansa ya sa wasu matan rage ƙiba : sauya yadda suke gudanar da al'amuransu na yau da kullum ne ya janyo hakan. Matan da suka ce kafin binciken cewa yawanci suna cin karin kumallo sun rasa kilogiram 8.9 a lokacin da suka daina yin karin kumallo, idan aka kwatanta da 6.2kg a rukunin karin kumallo. A halin yanzu, waɗanda suka saba ƙin yin karin kumallo sun rage kilogiram 7.7 lokacin da suka fara cin abincin - da 6kg lokacin da suka ci gaba da ƙin cin abincin.
Idan ba karin kumallo ne kaɗai ya tabbatar da raguwar nauyin ba, me yasa ake alaƙanta ƙiba da rashin yin karin kumallo?
Alexandra Johnstone, farfesa a fannin binciken cin abinci a Jami'ar Aberdeen, ta yi jayayya cewa yana iya kasancewa saboda masu ƙin yin karin kumallo ba su da masaniya ce game da abinci mai gina jiki da lafiya.
"Akwai nazari da yawa kan alaƙar da ke tsakanin cin karin kumallo da sakamakon lafiya, amma wannan na iya zama saboda waɗanda suke yin karin kumallo sun kasance da dabi'un inganta kiwon lafiya kamar rashin shan taba da kuma motsa jiki na yau da kullun," in ji ta.
Amfanin yin karin kumallo ga lafiya

Asalin hoton, Getty Images
An gano cewa karin kumallo ba ƙiba kaɗai ya ke da alaƙa tda shi ba. Rashin yin karin kumallo yana da alaƙa da haɓakar cututtukan zuciya da kashi 27%, da haɗarin kamuuwa da ciwon sukari da kashi 21 cikin ɗari a cikin maza, da haɗarin nau'in ciwon sukari na 2 mafi girma da kashi 20% a cikin mata.
Wannan na iya zama saboda rashin yin karin kumallo yana shafar yawar sinadarin glucose, da insulin, in ji masu binciken da suka gudanar da binciken 2023 kan azumi da ciwon sukari. Sun bi diddigin abincin mutane sama da 100,000 a tsawon shekaru bakwai, kuma sun gano cewa haɗarin kamuwa da cutar ya fi yawa a tsakanin wadanda aka yi binciken a kansu da ke cin karin kumallo bayan karfe 9 na safe, idan aka kwatanta da waɗanda suka ci kafin karfe takwas na safe.

Asalin hoton, Getty Images
Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa ake ganin fa'idodin karin kumallo kan kiwon lafiya - aƙalla a yammacin duniya - na iya zama darajar sinadirai da ake samu a abinicin da ake yawan ci da safe, wani ɓangare soboda wadannan hatsin na ɗauke da sinadaran inganta lafiya da dama. A wani bincike da aka gudanar kan dabi'ar karin kumallo tsakanin sama da mutane 8,000 a Burtaniya, masu binciken sun gano cewa mutanen da suke cin karin kumallo akai-akai suna da yawan sinadarai masu gina jiki. An dai gudanar da wannan binciken ne a ƙasasehn Australia da Brazil da Kanada da Indonesia da kuma Amurka.
Har ila yau, ana alaƙanta abincin karinm da ingantaccen aikin ƙwaƙwalwa, gami da mai da hankali kan abubuwa da kuma kaifin kalamai. Binciken da aka gudanar ka wasu rahotanni 54 ya gano cewa cin karin kumallo na iya inganta yadda mutum ke tuna abubuwa, ko da yake ba a kammala tabbatar da tasirin wasu ayyukan kwakwalwar ba. Duk da haka, daya daga cikin masu binciken, Mary Beth Spitznagel, masaniyar ilimin halayyar ɗan adam a Jami'ar Jihar Kent a Ohio, ta ce akwai hujjojin da ke nuna cewa karin kumallo yana inganta kaifin tunani - amma dai ana buƙatar ƙarin bincike kan lamarin.
Bayanin ƙarshe
Duk da yake babu tabbataccen shaida kan ainihin abin da ya kamata mu ci da kuma lokacin da ya kamata mu ci abincin, yarjejeniyar da aka samu ita ce mu saurari jikunanmu kuma mu ci abincin a lokacin da muke jin yunwa.
"Karin kumallo shi ya na da matuƙar mahimmanci ga mutanen da ke jin yunwa lokacin da suka tashi bacci," in ji Johnstone.
Misali, bincike ya nuna cewa waɗanda ke fuskantar hadarin kamuwa da ciwon sukari da waɗanda suka riga suka kamu da ciwon sukarin na samu ƙarin kaifin ƙwaƙwalwa sakamakon yin karin kumallo da abinci da ke ƙara yawar sukarin da ke jini a hankali.
Kowa akwai yadda ya ke fara ranarsa - kuma waɗannan bambance-bambancen, musamman a adadin sukari ko sinadarin glucose da ke jinin mutum, suna buƙatar a zurfafa bincike a kan su, in ji Spitznagel.
A ƙarshe, maslahar na iya kasancewa kada a ba da fifiko kan kowane abinci ɗaya, a maimakon haka riƙa duba yadda muke cin abinci duk tsawon rana.
"Madaidaicin karin kumallo yana da taimako sosai, amma samun ingantaccen abinci na yau da kullun a kodayaushe a cikin yini shine mafi mahimmanci don kiyaye kamuwa da ciwon sukari, wanda ke taimakawa wajen daidata nauyin jiki da matakan yunwa," in ji Elder.
"Karin kumallo ba shi ne kaɗai abincin da ya kamata mu inganta ba."










