Me zai faru da jikinka idan ka daina shan shayi?

Asalin hoton, Getty Images
Sinadarin Kafen (Caffeine) wanda yake cikin abubuwa da dama da suka kama daga gahawa da shayi da goro da alewar cakulan hatta a wasu magungunan ma, shi ne abin kara kuzari da mutane suka fi sha a duniya, domin sinadari ne da ke cikin abubuwa da yawa da mutane suke ci ko sha a kayan abincinsu.
Idan mutum ya sha ko ya ci wani abu da yake dauke da wannan sinadari da ke cikin gahawa, nan da nan yake bin jiki ya yi tasiri cikin sa'a biyu - amma kuma zai dauki tsawon lokacin da ya kai sa'a tara kafin ya bar jikin.
Wannan sinadari yana ratsa dukkanin sassan jikin mutum.
Wannan ne ya sa masana ke shawartar mutum babba da ka da ya sha abin da ya wuce kofi hudu na gahawa a rana daya.
Idan mutum ya sha abin da ya zarta haka to zai iya gamuwa da matsalolin da suka hada da karkarwa ko ciwon kai, ko yawan bugawar zuciya, ko jin amai, har ma mutum zai iya mutuwa idan lamarin ya yi tsanani.
Hatta mutanen da ke shan gahawa ko shayi kadan a rana za su iya gamuwa da wasu matsaloli - kamar saurin fushi, da kasa bacci da damuwa.
Wannan na daga cikin dalilan da ke sa wasu mutanen su daina shan gahawa ko kuma duk wani abin ci ko sha da ke dauke da sinadarin Kafen.
Aikin Kwakwalwa
Daina shan gahawa ko kuma duk wani abu da ke da sinadarin da ke cikinta na iya haddasa wa mutum ciwon kai, ko gajiya. Wannan na kasancewa ne kuwa saboda jikin mutum ya riga ya saba da sinadarin.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shi wannan sinadari shansa yana sa jinkirta gajiya ko bacci ga jikin wanda yake sha - wannan ne ya sa idan mutum yana son ya yi wani aiki ko kuma ba ya son bacci ya kama shi sai ya ci ko ya sha wani abu da yake dauke da wannan sinadari.
Saboda haka idan mutum ya daina shan sinadarin akwai sinadarin da kwakwalwa ta riga ta saba da fitarwa sakamakon yawan shan na cikin gahawar da mutum ke yi a baya, a don haka wannan sinadari da kwakwalwa ta saba fitarwa yana nan tare da yawa sai ya sa mutum gajiya fiye da yadda yake ji a baya.
Dangane da ciwon kai kuwa ga yadda abin yake: a cikin kai da wuya, sinadarin na cikin gahawa na sa jijiyoyin jini su tsuke, wanda hakan ke rage yawan jinin da yake zuwa kwakwalwa.
Saboda haka bayan sa'a 24 da daina shan sinadarin sai jijiyoyin jininka su koma yadda suke daidai - su bude - wanda hakan sai ya kara yawan jinin da ke zuwa kwakwalwa, hakan zai kuma haddasa ciwon kai.
Galibi wannan matsala na kaiwa tsawon kwana tara kafin ta rabu da mutum.

Asalin hoton, Getty Images
Saboda jikinka ya riga ya saba da shan gahawa ko sinadarin cikinta, akwai wani sinadari da yake hana jikin mutym jin zafin ciwo ko wani abu makamancin haka saboda gahawar da ya saba sha, to idan ka daina shan gahawar shi kuma jikinka ya riga ya saba samar da wancan sinadari da yake hana ka jin ciwo, hakan zai sa jikinka a yanzu ya zama yana iya jin abu nan da nan da an taba ka.
Sinadarin gahawa yana shafar bacci ne kawai idan an sha shi da yamma ko da daddare. Yana yin hakan ne kuwa saboda yana jinkirta wa jiki sakin sinadarin da ke sa mutum ya ji gajiya har bacci ya kama shi, da minti 40.
Haka kuma sinadarin na gahawa na iya rage tsawon lokacin da mutum ke bacci. Wannan zai iya kara yawan gajiya a jikinka washegari, abin da zai sa ka ji ya kamata ka sha gahawa domin ka tashi daga baccin.
To amma kuma a dalilin hakan za ka gamu da matsala ka kasa bacci nan gaba. Idan ka daina shan gahawa baccinka zai inganta. Wasu bayanai sun nuna cewa ana ganin wannan cigaba cikin sa'a 12.

Asalin hoton, Getty Images
Haka kuma ana danganta shan gahawa da matsalar karuwar fargaba da tsoro - ba kawai ga mutanen da ke da larurar kwakwalwa ba.
Saboda haka rage yawan sha ko ma daina shan gahawa na iya inganta yanayin mutum.
Wannan ka iya kasancewa saboda samun bacci mai kyau, domin hana kai bacci na kara wa mutum larurar fargaba da sauran matsaloli.
Lafiyar Zuciya
Rage yawa ko ma daina shan gahawa na iya magance matsalar zafin kirji (zuciya) da ciwon ciki na sanadiyyar rashin narkewar abinci.
Wannan na kasancewa ne saboda sinadarin cikin gahawa na sa jikin mutum ya zuba wani sinadari a cikin mutum, wanda ke raunana aikin kofar makogaro da duk abincin da mutum ya ci ke bi ta wurin zuwa ciki wanda a sanadiyyar hakan abincin da mutum ya ci ba ya narkewa yadda ya kamata. A don haka sai mutum ya gamu da matsalar ciwo ko rikicewar ciki.

Asalin hoton, Getty Images
Fararen hakora
Daina ko rage shan gahawa na iya sa hasken hakoranka ya karu - ba wai kawai saboda sinadarin kafen da ke cikin gahawa ko shayi ko goron ba, a'a, wannan na kasancewa ne saboda shayi ko gahawar na dauke da wasu sinadarai da suke sa hakori baki.
Sukarin da ke cikin irin lemon nan mai kara kuzari ma na iya lalata hakori. Bincike ya nuna cewa irin wadannan lemukan kamfani da ke dauke da sinadarin cikin gahawa - kafen - na iya rage yawan yawun bakin mutum - wanda kuma shi yawu yana kare hakori daga lalacewa.
Haka kuma za ka ji cewa bayan da ka daina shan gahawa, ka fi jin zakin abubuwan da kake ci ko sha masu zaki, saboda sinadarin na gahawa na shafar yadda kake jin zakin abubuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Yawan zuwa bandaki
Sanadarin gahawa na tasiri a kan jijiyoyin hanji musamman babban hanji, inda yake sa hanjin ya matse hakan kuma na sa mutum ya yi saurin jin bahaya.
Haka kuma wannan sinadari na iya shafar yadda kake zuwa bandaki - musamman idan kana shansa da yawa.
Sannan wannan sinadari yana sa jiki saurin samar da fitsari - saboda tasirinsa yana sa jiki ya rage tsawon lokacin da yake iya rike ruwa.
Akwai kuma sheda da ke nuna cewa sinadarin cikin gahawa na tunzura jakar fitsari wanda hakan zai iya sa mutum yawan zuwa fitsari.
Saboda haka daina shan gahawa ka iya rage yawan zuwa bandaki da mutum ke yi.
Sha madaidaici

Asalin hoton, Getty Images
Kamar dai komai, shan gahawa ma abu ne da ya kamata mutum ya rika yi daidai-wa-daida, wato kar a tsananta.
Idan har da gaske kake kana son ka daina shan gahawa ko abubuwan da ke kunshe da sinadarin da ke cikinta wato Kafen, hanyar da ta fi dacewa ita ce, ka janye sannu a hankali - ba kwatsam lokaci daya ba.
Dakatar da shan gahawa lokaci daya na iya janyo ma wasu matsaloli da suka hada da ciwon kai da gajiya - da za su iya kaiwa tsawon mako biyu zuwa uku.
Tsanani da kuma tsawon lokacin da wadannan matsaloli za su dame ka ya danganta ne da yawan gahawar da kake sha kullum da kuma tsawon lokaci ko shekarun da ka yi kana sha.











