Yadda aka yanke wa Simon Ekpa hukuncin shekara shida a gidan yari

Asalin hoton, Simon Ekpa/X
Kotu a ƙasar Finland ta yanke wa ɗan Najeriya mai 'rajin ɓallewar ƙasar Biyafara', Simon Ekpa hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari bisa laifukan ta'addanci.
Kotun ta same shi da laifin ƙoƙarin harzuƙa jama'a da niyyar ta'addanci da kuma shiga cikin ayyukan ƙungiyar ta'addanci.
Kotun ta kuma same shi da laifukan zamba ta haraji da kuma karya doka wanda hakan ya sanya kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari.
Kotun ta bayyana cewa Ekpa ya yi ƙoƙarin ƙarfafa rajin ɓallewar yankin Biyafara a kudancin Najeriya ta haramtacciyar hanya tsakanin watan Agustan 2021 zuwa Nuwamban 2024.
Asalin tuhume-tuhumen
A watan Disambar 2024 ne dai hukumomi a Finland suka cafke Simon Ekpa bisa tuhume-tuhumen ayyukan ta'addanci.
Kotun lardin Paijat-Hame ce ta aike da Simon Ekpa zuwa gidan yari bisa tuhume-tuhumen ingiza jama'a da kuma na aikata laifuka da manufar ta'addanci.
Kotun ta kuma ce ya yi amfani da kafafen sada zumunta domin samun shigewa gaba-gaba a wannan fafutika.
Ƙungiyar ƴan-awaren ta kuma samar da wasu ƙungiyoyi masu ɗaukar makami, waɗanda kotun ta bayyana a matsayin na ta'addanci.
A cewar hukuncin, Ekpa ne ya samar wa waɗannan ƙungiyoyin makamai da abubuwa masu fashewa da harsasai ta hanyar wasu mutanensa.
Haka kuma, an same shi da laifin amfani da kafafen sada zumuntarsa wajen ingiza mabiyansa su aikata laifuka a Najeriya.
Kotun ta ce ya aikata duk wadannan laifuka ne yayin da yake zama a garin Lahti na ƙasar ta Finland, sai dai ya musanta zarge-zargen.
Hukuncin da kotun ta yanke dai ba shi ba ne na ƙarshe ba, inda ake kyautata zaton cewa zai iya ɗauka ƙara zuwa kotu ta gaba.
An dai tuhumi Simon Ekpa da aikata laifukan a ranar 23 ga watan Agustan 2021 a Lahti.
Wane ne Simon Ekpba?
Simon Ekpa ɗan Najeriya ne mazaunin Finland wanda yake fafutikar kafa ƙasar Biafra, kuma yake iƙirarin maye gurbin tsohon shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Ekpa yana zaune ne a ƙasar Finland, amma yana jagorantar harkokin kafa ƙasar ta Biafra daga can.
Simon ya yi kira da ƴan ƙabilar Igbo da ke kudu maso gabashin Najeriya da su ƙaurace wa zaɓe har sai gwamnatin Najeriya ta saki Kanu.
A shafinsa na X, Ekpa ya bayyana kansa a matsayin mai fafutikar ƙwatar ƴancin mutane, babban jami'in gudanarwa, kuma babban mai bada shawara kan harkokin shari'a na Ekpa & Co Oy.
Har wayau Ekpa ya bayyana kansa da mai bincike kan harkokin shari'a, marubuci, mai sharhi kan al'amuran yau da kullum sannan ɗan siyasar Finlanda kuma kakakin Biafra.
Ekpa ba shi da lasisin zama lauya

Asalin hoton, Screengrab from Ekpa and Co Oy website
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kotun ƙasar Finland ta samu Simon Ekpa da laifin "karya dokokin tsarin mulki na lauyanci na ƙasar', bisa zargin cewa yana shige wa ƴan cirani gaba domin samun mafaka a ƙasar.
Simon Ekpa dai ya kafa ofishin shari'a mai suna Ekpa & Co Oy a shekarar 2015 inda yake gudanar da ayyukan da suka jiɓanci iyalai da ƴancin ƙananan yara da fassara da sauran abubuwan da suka shafi kare haƙƙoƙin mutane.
To sai dai ƙasar Finland ta ce Ekpa ba shi da lasisin gudanar da irin wannan ofishi ballantana ma har ya wakilci wasu domin kare su a kotu.
An ce tsohuwar maiɗakinsa, Marianne Sakajarvi ita ce cikakkiyar lauya kuma ita ce take gudanar da mafi yawancin ayyukan da ke zuwa ofishin nasa, kamar yadda bincike ya nuna.
To sai dai kuma Ekpa ya shaida wa ƴanjarida cewa yana da digiri na biyu a fannin shari'a domin kare haƙƙoƙin bil'adama daga jami'ar Aberystwyth University ta hanyar karatu daga gida. Kuma ya amince cewa digitin nasa bai wadatar ba wajen tsayawa wasu a kotu a matsayin lauyansu.
Me gwamnatin Najeriya ta ce?
Gwamnatin Najeriya ta yaba da hukuncin da kotun lardin Päijät-Häme da ke ƙasar Finland ta yanke a ranar Litinin, inda ta yanke wa mai fafutikar kafa ƙasar Biyafara Simon Ekpa hukuncin zaman gidan kaso na shekara shida bisa samunsa da laifin ta'addanci.
A wata sanarwa da ministan watsa labarai Mohammed Idris ya fitar, ya ce suna maraba da hukuncin, kuma suna jinjina wa ƙasar ta Finland.
"Hukuncin ya zo a daidai, domin zai zama adalci ga ɗimbin ƴan Najeriya da suka rasa rayukansu da waɗanda suka shiga tashin hankalin a sanaiyar bala'in da su Ekpa suka jefa su," kamar yadda sanarwar ta bayyana, inda ministan ya ƙara da cewa wannan hukuncin zai ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin Najeriya da Finland.
Sanarwar ta ce Ekpa ya yi shekaru yana tunzura jama'a suna aikata laifuka, wanda ke "ruguza rayuwar iyalai da karya kasuwancin su da mayar da yara marayu da jefa garuruwa da dama cikin fargaba, da ma zama silar mutuwar ɗaruruwan mutane da sunan fafutikar da ke barazana ga haɗin kan Najeriya da ƴancinta."
Ya ƙara da cewa a shirye gwamnatin Tinubu take ta tsayawa da ƙarfinta wajen kare ƴancin ƙasar da mutuncin ƴan ƙasar baki ɗaya ta hanyar "amfani da diflomasiyyar ƙasa da ƙasa da jami'an tsaro da ɓangaren shari'a domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin ƙasar."
Simon Ekpa dai na ɗaya daga cikin mutane da ƙungiyoyi 17 da gwamnatin Najeriya ta ayyana a matsayin waɗanda ta ƙaƙaba wa takunkumin tare da kulle asusun bankinsu saboda harkokinsu da ake zargi na tallafa wa ayyukan ta'addanci.
An ɗauki matakin ne bisa dogaro da sashe na 54 na dokar hana yaɗuwar ta'addanci ta 2022.
A watan Maris na 2024 ne rundunar sojin Najeriya ta ayyana Ekpa da wasu mutane guda 96 a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin su da ta'addanci da ingiza yunƙurin ɓallewa daga ƙasar da tayar da zaune tsaye.











