Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Al'ummar garin Uromi na tserewa saboda fargaba'
Bayanai da BBC ta tattaro daga garin Uromi na nuna cewa mazauna garin da maƙwabta na tserewa daga garuruwan nasu saboda zaman ɗar-ɗar da fargabar hare-haren ɗaukar fansa da kuma kamun ƴansanda.
Tun dai bayan kisan wasu maharba 16 matafiya ƴan arewacin ƙasar da ƴan sintiri suka yi a Uromin da ke jihar Edo suka yi ake ta samun zazzafan martani daga shugabannin yankin da ke ta kiraye-kirayen sai an hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aika.
"Shaguna sun kasance a rufe, inda wasu bayanai ke nuna cewa wasu mazauna garin na barin wurin saboda tsoron abin da zai faru bayan kisan gillar da ta faru a ranar Alhamis." A cewar shugaban matasan arewacin Najeriya mazauna garin na Uromi , Babangida SBJ Yawuri ya ce mazauna wurin na cikin fargaba.
"Yayin da da dama daga ƴan asalain garin ke tsoron shiga kasuwar ƴan arewacin garin. Saboda ganin da suka yi an ɗauki mataki kwakkwara, In ji duk irin abin da suke yi wa Bahaushe ba a taɓa samun ɗaukar mataki kamar irin wannan ba" In ji Babangida.
Tuni dai gwamnan na jihar Edo, Monday Okpebholo ya kai ziyara jihar Kano, inda maharan suka fito, inda ya kuma ya ɗauki alkawarin biyan diyya ga maharban da aka kashe tare da tabbatar da an hukunta masu laifin.
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ba za ta bar maganar ba har sai an hukunta waɗanda ke da hannu a kisan gillar.
Bayanai sun nuna cewa an kama mutum 40 da ake zargin suna da hannu kan al'amarin.
Yadda abin ya faru
A ranar Juma'a shafukan sada zumunta musamman a arewacin Najeriya sun cika da fushi da alhini na abin da ya faru a Edo, ɗaya daga cikin jihohin kudancin ƙasar.
Hotunan da aka riƙa yadawa, waɗanda BBC ba ta tantance da kanta ba sun nuna yadda aka yi wa wasu mutane jina-jina, sannan aka riƙa jefa tayoyin mota a kansu.
Haka nan an ga yadda wasu ke dukan wani mutum da katako a cikin kwalbati, sannan a wani hoton kuma an ga wuta na ci daga nesa.
Sannan kuma an ga babbar motar kamfanin Dangote, wadda aka farfasa wa gilashi yayin da wani ɓangare nata ke ci da wuta.
Wani hoton kuma ya nuna bindigogin harba ka ruga, irin ta masu farauta ta gargajiya, da kuma adduna.
Bayanai sun nuna cewa mutanen da lamarin ya rutsa da su, wadanda suka bayyana kansu a matsayin mafarauta, ƴan sintiri ne suka tare su yayin da suke tafiya a wata babbar mota.
Binciken da ƴan sintirin suka yi ya sanya aka gano bindigogi a motar, lamarin da ya janyo mutanen gari suka far wa waɗanda ke cikin motar bisa zargin cewa masu garkuwa da mutane ne.
BBC ta tattauna da shugaban ƴan arewa mazauna Edo, Alhaji Badamasi Saleh, wanda ya ce mafarauta 27 ne a cikin motar, inda mutane ne ƴan arewacin ƙasar waɗanda suka tashi daga garin Fatakwal domin zuwa gida bukukuwan Sallah.
"Lokacin da suka zo garin sai ƴan bijilante suka tare su, sai suka ce kidinafas ne, suka kama su da duka, suka kashe su, suka ƙona wasu daga daga cikinsu."
"Mutum 11 suna nan da lafiyarsu amma mutum biyu na jinya a asibiti."
Yanzu haka dai shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike tare da hukunta waɗanda ke da hannu.