Har yanzu rikicin Syria zai iya ci gaba - MDD

Motar Majalisar Dinkin Duniya da yara a keke

Asalin hoton, AFP

Lokacin karatu: Minti 3

Wata babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya ta ce, har yanzu al'amura ba su daidaita ba a Syria ta yadda tarin mutanen da suka tsere wa yakin basasar kasar za su iya komawa.

Shugabar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar, Amy Pope, ta ce idan ba a samu tallafin da za a bai wa jama'a ba, sake mayar da su kasar, zai iya sake jefa ta cikin karin rikici.

Da take magana da kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, bayan ziyarar da ta kai babban birnin kasar ta Syria, Damascus, shugabar hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta Majalisr Dinkin Duniya, Amy Pope, ta ce, tuni ma har kusan 'yan gudun hijira dubu daro daya sun koma kasar – amma kuma wasu 'yan Shi'a sun bar kasar saboda fargabar da suke da ita a kan sababbin masu rike da iko a Syriar.

Tun da farko kuma wakilin musamman na Majalisar ta Dinkin Duniya a Syriar, Geir Pedersen, ya yi gargadin cewa kasar za ta iya sake fadawa cikin rikici idan ba ta samu tallafi daga kasashe da hukumomin duniya ba, cikin gaggawa.

Pedersen ya gaya wa kwamitin tsaro na Majalisar cewa yakin ba fa karewa ya yi ba, duk da tserewar da tsohon shugaban kasar Bashar al- Assad ya yi zuwa Rasha.

Wakilin na musamman ya yi nuni da fadan baya-bayan nan da aka yi tsakanin kungiyoyin da ke samun goyon bayan Turkiyya da kuma dakarun Kurdawa a yankin arewa maso gabashin kasar, inda aka tsawaita yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Amurka ta jagoranta har zuwa karshen makon nan.

Mista Pedersen ya ce taimakon da Syria ke bukata na da yawa, bayan yakin basasa na tsawon shekaru – sannan kuma akwai bukatar a cire wa kasar takunkuman da aka Sanya mata, domin a samu damar sake gina ta;

Ya ce, ''kwakkwaran hobbasa da zai kunshi kowa da kowa na mayar da kasar turbar siyasa shi ne ginshikin tabbatar da kasar ta samu tallafin tattalin arzikin da take bukata. Kamar yadda ake da Muradin ganin aniyar kasashen duniya ta shiga lamarin.''

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniyar a Syria ya kara da cewa bukatan kasar ta Syria suna da yawa, kuma za a iya magance su ne da gagarumin taimako – wanda ya hada da kawo karshen takunkumin da aka Sanya wa kasar da daukar matakan da suka dace da kuma sake gina kasar gaba daya.

A halin da ake ciki jami'an agaji na sa-kai na rundunar tsaro da kai dauki ta Syria – wato White Helmet na can na ta faman nema da kuma tantance dubban mutanen da aka yi wa kisan gilla bayan azabtar da su a lokacin mulkin hambararren Shugaba Assad, aka kuma binne gawarwakinsu a manyan kaburbura na bai daya, da aka boye.

Sama da mutum 100,000 ake ganin sun bata bat a kasar ta Syria tun 2011.

Kuma kungiyoyin kare hakkin dan'Adam sun ayyana cewa sama da mutum 80,000 daga wadanda suka bata sun mutu.

Kuma akwai wasu 60,000 da aka yi amanna an hallaka su, kamar yadda kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin dan'Adam a Syriar da ke da London, wato Syrian Observatory for Human Rights (SOHR), ta bayyana.

Kungiyar 'yan tawaye ta Hayat Tahrir al-Sham (HTS) – wadda ta kawo karshen mulkin iyalan gidan Assad na sama da shekara hamsin, ta bude gidajen yari da wuraren tsare jama'a a fadin kasar ta Syria, bayan ta hambarar da Bashar al-Assad a 'yan kwanakin da suka gabata.